Ticker

6/recent/ticker-posts

4.5.1 Waƙoƙin Almajirai

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.5.1 Waƙoƙin Almajirai

Waƙoƙin Almajirai su ne waƙoƙin da yara ƙanana ‘yan misalin shekaru biyar zuwa goma sha shida masu karatun allo suke amfani da su a lokacin da suke yin bara domin neman abin da za su ci. Irin waɗannan waƙoƙin duk na baka ne ba tare da sanin takamaimai wanda ya tsara su ba, kuma an ɗauki lokaci mai tsawo ana amfani da su wajen yin bara. Waƙoƙin mafi yawa gajeru ne kasancewar yara ne ke ta’ammuli da su, kasancewar gajarci wata siga ce ta waƙoƙin yara[1]. Irin waɗannan waƙoƙin sukan ƙumshi jigogi kamar fatar alheri da addu’a da ƙasƙan da kai da ban tausayi da darajar almajiri da begen[2] Annabi da sauransu. Waɗansu daga cikin ana yi masu amshi, wasu kuma almajiri ɗaya ne kawai yake rera abinsa. Misali:[1]  Duba a Dunfawa 2002.

[2]  Yabon Annabin rahma, Annabi Muhammadu (S.A.W).


Post a Comment

0 Comments