Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.5 Nau’o’in Waƙoƙin Bara
Yadda mabarata suke dabam-daban haka ma waƙoƙinsu suke. Ana iya cewa waƙoƙin da mabarata ke bara da su a yankin ƙasar Hausa a wannan ƙarni sun kasu zuwa manyan kasusuwa biyu; wato waƙoƙin Almajirai[1] da waƙoƙin sauran mabarata[2]. Shi ma kashin na biyu ya sake kasuwa zuwa na baka da rubutattu. Ana iya zana bishiyar yadda waƙoƙin suka rarrabu kamar haka:
Waƙoƙin Bara
Almajirai Sauran Mabarata
Masu Amshi Maras Amshi Na Baka Rubutattu
[1] Ƙananan yara masu karatun
allo.
[2] Waɗanda ba masu karatun allo ba (kamar gardawa da naƙasassu)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.