Ticker

6/recent/ticker-posts

4.5.1.1 Waƙoƙin Almajirai masu amshi

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.5.1.1 Waƙoƙin Almajirai masu amshi

Waɗannan waƙoƙin a cikin taro almajirai ke rera su, wato daga mutum biyu zuwa sama. Wani na bayarwa saura suna amsawa. Almajirai sun fi rera irin waɗannan waƙoƙin a gidajen da suke zuwa bara, sai wasu lokutan suke rera su a waje inda jama’a ke taruwa[1] musamman idan ana cin abinci a wurin. Sauran mabarata waɗanda ba Almajirai ba ba sa amfani da irin waɗɗannan waƙoƙi wajen bara. Ga misalin wasu daga cikin irin waɗannan waƙoƙin.



[1]  Kamar tashoshin mota ko kasuwanni da sauran wuraren da ake taruwa.


Post a Comment

0 Comments