Ticker

6/recent/ticker-posts

3.2.3 Talakawa

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.2.3 Talakawa

Matalauci a nan na nufin mutum wanda ba ya da wadata, wato wanda abin da yake samu bai wuce bukatarsa ta yau da kullum ba ko da shi basarake ne ko malami ko ma’aikacin gwamnati ko ɗan siyasa. Wato dai mutane waɗanda ba masu hannu da shuni ba waɗanda ba su iya biyan bukatun kansu cikin yalwa saboda rashin abin hannunsu. Da yawa daga cikin waɗannan jama’a sun dogara ga ‘yan aikace-aikacen hannu domi neman abin biyan buƙatu, kamar abin ci da na sha da sutura da sauran ‘yan ƙananan bukatocisu. Talaka mutum ne mai wani matsayi a tsarin zamantakewar Bahaushe wanda kankasance cikin yunƙurin zama mawadaci a kowane lokaci. Ƙarancin abin hannun wasu daga cikinsu yakan tsananta su kasance cikin halin ƙaƙa-ni- ka-yi har marasa ƙarfin zuciya daga cikinsu su rikiɗa su koma mabarata. To duk da ƙaramcin abin da ke hannunsu bai hana mabarata su yi masu bara ba. Su kuma sukan ɗiba cikin kaɗan ɗin nan da suke da shi su ba mabarata sadaka. 

Post a Comment

0 Comments