Ticker

6/recent/ticker-posts

3.2.2 Attajirai

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.2.2 Attajirai

Attajirai su ne mutane masu hali waɗanda tushen samun wadatarsu ya fi ta’allaƙa da kasuwanci da fatauci da noma. Ita kanta kalmar attajiri ararra ce daga Larabci mai nuna ma’anar ɗan kasuwa[1]. Kodayake an fi nuna cewa masu wadata daga cikinsu a matsayin attajirai a wannan ƙasa ta Hausa. Kafin shigowar mulkin Turawa da sauye-sauyen da hakan ya haifar ga ƙasar Hausa, sarakuna da attajirai su ne kawai mawadata da ma wasu malamai a cikin al’umma. Canjin da aka samu na gudanar da mulki a ƙasar Hausa shi ya kawo a ƙidaya ma’aikata da ‘yan siyasa a cikin mawadata, domin ma’aikata da ‘yan siyasa sun koma su ne masu mulki.

Abin nufi a nan shi ne wannan kaso na masu arziki ne ko kuma a ce mawadata waɗanda suka mallaki abubuwan biyan buƙatunsu da na iyalinsu da ma na taimaka wa wasu idan suna so. Su ma irin wannan rukunin jama’a mabarata na yi masu bara a kowane lokaci, kuma kowane waje. Ana isko su a shagunansu ko gidajensu ko a kowane waje na gudanar da sana’o’insu a yi masu bara. Sau da yawa ana dacewa su taimaka ko da da abu kaɗan ne.



[1]  Wannan na nuna cewa mutumin da ke lamarin saye da sayarwa shi ake kira attajiri.


Post a Comment

0 Comments