Ticker

6/recent/ticker-posts

3.3 Naɗewa - Daga littafin “Bara Da Wasu Waƙoƙin Bara A Ƙasar Hausa”

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.3 Naɗewa

A bayanan da suka gabata cikin wannan babi an yi ƙoƙarin fito da ma’anar bara da tarihin samuwarsa da yaɗuwarsa a duniya, da kuma yadda ya samu a ƙasar Hausa. Haka ma a cikin babin an yi bayani a kan irin mutane biyu da ke bara a yankin na ƙasar Hausa, wato almajirai da sauran masu wata naƙasa da kuma waɗanda ake yi wa baran, wato mawadata da ma wasu talakawa. Waɗannan mabarata da aka yi bayaninsu cikin wannan babi su ne za a dubi dabarun da suke ammfani da su wajen yin bara ga waɗanda suke yi wa baran. Babi na gaba zai nazarci waƙoƙin ya fito da ƙunshiyarsu.


Post a Comment

0 Comments