Ticker

6/recent/ticker-posts

3.1.2 Gardawa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.1.2 Gardawa

Gardawa ma jam’in kalmar Gardi ce wadda ke nufin ɗalibin Ƙur’ani da ya kai wani mataki ga karanta Ƙur’ani. Khalid ya bayyana ma’anar kalmar Gardi kamar haka:

Ɗalibin da ya karanci alƙur’ani kuma ya kai matsayin rubuta wasu ayoyinsa a kan allo tare da jagorancin malam ko wani ɗalibi na gaba da shi a makarantar, ya cigaba da karatun hadda[1] har zuwa aya ta ƙarshe a lokacin ya zama gardi” (Khalid 1998: 45).

Wannan ya nuna Gardawa almajirai ne amma waɗanda suka girma har suka fara wuce yawon bara a cikin gidaje kamar yadda almajirai ƙolaye[2] suke yi, amma sun ci gaba da karatun suna ƙara samun ilimi. Baran Gardawa ba kullum ba ne, sai mafi yawa ranakun Jum’a ko cikin azumi ko wata rana ta bukin addini kamar daren salla ƙarama ko babba. Mafi yawa sun fi dogara ga abinda almajirai suka samo suka kawo masu ko ɗan abinda suka samu ga ‘yan sana’o’in da suke yi bayan lokacin amkaranta. Gardawa sukan taimaka wa malamai wajen karantar da sauran almajirai ƙanana, kuma su sukan yi wasu ayyuka na musamman irin na almajirci waɗanda malamai ke yi kamar addu’o’i da rubutun sha tare da dukan ayyukan tsibbu da sauransu.



[1]  Iya yin karatu a ka ba tare da an duba ba.

[2]  Masu karatun allo amma ba su sauke Ƙur’ani ba


Post a Comment

0 Comments