Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
3.1.3 Naƙasassu
Naƙasassu su ne wani jinsin mutane da Allah Ya nufa da samun wata tawaya[1] ga halittarsu. Tawayar na iya kasancewa ga hannu ko ƙafa ko wani sashe na jiki ko hankali. Ita kalmar daga Larabci Bahaushe ya aro ta ya yi amfani da ita da ma’anar da take a cikin Larabci, wato kasawa.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayar
da ma’anar naƙasa kamar haka:
A disability is may be generally defined as a condition which my restrict a person mental, sensory, or mobility functions to undertake or perform a task in the same way as a person who does not have a disability. (WHO 2012)
Fassara:
“Ana iya bayyana ma’anar Naƙasa da cewa wata tawaya a cikin ayyukan jiki ko kuma wahalhalun da ake samu wajen wani sanannen aikin da mutum kan samu wajen gudanar da hidima ko aiki kamar yadda wani wanda bai da wata tawaye ke yi’.
Wannan ma’anar ta nuna duk wata
tawaya da aka samu a wata gaɓa ta
jikin mutm ana kiranta naƙasa, wannan
kuwa har da taɓin
hankali. Irin waɗannan
mabarata akwai manya akwai yara, kuma suna bara ne saboda halin naƙasar da suke da ita. Mabarata da ke cikin wannan kaso sun
haɗa da kutare da
makafi da guragu da masu mutuwar zuci[2].Wasu daga cikin yaran da
ke da naƙasa manya ne lafiyayyu ke bara da su. Waɗannan mabarata ba kamar almajirai
suke ba, ba su da wani lokaci na daina bara, suna yi ne har iyakar rai, ba wani
lokaci da za su daina yin baran.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.