Ticker

6/recent/ticker-posts

3.1.1 Almajirai

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.1.1 Almajirai

Almajirai jam’in kalmar almajiri ce wadda ke nufin ƙananan yara da ke tsakanin shekaru shida zuwa sha biyar, waɗanda iyayensu ke ɗaukar su su kai wajen wani malami da ke zaune wani gari da ba garinsu ba domin su yi karatun allo su sami ilimin addinin Musulunci.

Ƙamusun Hausa wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, na Jami’ar Bayero, Kano ya bayyana ma’anar almajiri da cewakamar haka:

1.                  “ Mai neman sani ko ɗalibi” 2. “Mai bara”

Wannan ita ce ma’anar kalmar almajirai da ta dace ƙwarai da manufar wannan aikin, saboda ma’anar ta haɗa neman ilmi da bara. Masu neman ilmin addini Musulunci ko da sun girma cikin abin sukan kira kansu da suna almajirai domin waiwaye ga matsayin da aka fito lokacin da ake ƙanana ana neman ilmin saboda ƙaƙan-da-kai[1]. Wato ke nan mai yin bara domin neman ilmi shi ne Almajiri mai jam’i almajirai.

Khalid kuwa cewa ya yi

“Almajiri kalmar Hausa ce da ke nufin ɗalibi ko ɗan makaranta. An samo kalmar ne daga harshen Larabci ‘al-muhajir’ mai nufin wanda ya yi ƙaura. A tarihance kalmar asalinta daga waɗanda suka yi hijira daga Makka zuwa Madina tare da Manzon Allah (SAW) waɗanda aka sani da Muhajirun (ɗaya muhajir) Khalid, (2006:3).

Wannan malamin ma ya nuna ma’anar kalmar almajiri da ɗan makaranta wanda ke iya zama ɗan makarantar boko ko ta allo, sannan ya kawo tushen da aka samo kalmar. A dalilin tasowar yara daga garuruwansu zuwa wasu domin neman ilmi sai aka kira su da sunan, da yake addinance duk wanda ya bar garinsa zuwa wani saboda wani abu da ya danganci addini mai hijira ne.

Wannan nau’i na mabarata suna aiwatar da bara ne wani ɗan lokaci, wato iya lokacin da yaro yake ƙarami (tsakanin shekaru 6-15) yana karatun allo. Da zaran sun girma ko da sun ci gaba da karatun za su daina bara, su nemi wata sana’a su riƙa yi domin samun abinci. Wasu idan sana’ar da suke yi ta ɗauke su sai su yi zamansu wannan gari har iya rai. Wannan kaso na mabarata yana da yawa ainun a cikin yankin ƙasar Hausa, akwai su lugu-lugu, saƙo-saƙo na ƙasar.



[1]  Wahala

Post a Comment

0 Comments