Tuwon Kasa

    7.3 Tuwon Ƙasa

    Wannan wasa ne na yara masu ƙarancin shekaru sosai. Yawancin masu gudanar da wannan wasa sukan kasance ‘yan shekara shida zuwa ƙasa. Saboda haka, a mafi yawan lokuta yaran sukan kasance maza da mata. Wannan ne ma dalilin da ya sa bai kasance ƙarƙashin rukunin wasannin yara mata zalla ba, duk da cewa yara matan ne suka fi dacewa da shi. Wasan yana kama da wasan ‘yar tsana.

    7.3.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Ana gudanar da wannan wasa ne a gida. Akan nemi gindin bishiya ko inuwar kago domin gudanar da wannan wasa.

    ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma.

    7.3.2 KayanAiki

    i. Ruwa

    ii. Ƙasa

    iii. Ganyaye

    iv. Gwangwanaye da marafen murfan mayi ko marafan ƙananan robobi ko gora

    v. Ƙananan duwatsu

    vi. Tsinkaye

    vii. Tukunyar taɓo ƙarama ta wasa

    7.3.3 Yadda Ake Wasa

    Masu wasa za su samo duwatsu ƙanana guda su haɗa murahu da shi. Sai kuma su sanya tsinkaye a mazaunin itatuwa. Sannan za su aza tukunyar taɓo ta wasa ko kuma gwangwanaye a matsayin tukwane. Daga an yi haka, to sai a hau girki. Za a nemi ruwa, sannan a sanya ƙasa a matsayin gari. Yara na yin duk yadda ake dafa tuwo. Wato tun daga kan ruɗe har dai a je ga sauƙewa.

    A ɗaya ɓangaren kuma, za a samu ganyaye a yayyanka domin haɗa miya. Yayin da aka sanya a tukunya, za a sa ruwa mai ɗan dama a yi ta gaurayawa. Wani lokaci akan samu ƙananan tsakuwowi ko wani abu mai kama da wannan a matsayin naman da za a sanya cikin miyar.

    Bayan komai ya kammala, za a zuzzuba abinci. Kowane mai wasa zai samu nasa. Daga nan kuma za a fara ci. Yayin da aka ɗeɓo abincin, akan dangwala shi ne a ƙasa da baki, wato gemu. Daga nan sai kuma a watsar da baya, wanda ke daidai da an cinye. Wani lokaci mai wasa na iya cinye abincinsa har da neman daɗi. Ko ɗan wasa ya hau santi yayin cin wannan abinci.

    7.3.4 Tsokaci

    Wannan wasa kwaikwayo ne ga yadda ake dafa abinci na haƙiƙa. Yana koyar da yara, musamman mata yadda ake gudanar da girke-girke da kuma rabon abinci bayan an kammala. Yawanci yara na ɗaukar salon dafa abinci da kuma rabiyarsa da ma cin abincin, kamar yadda suke gani a gidajensu.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.