Ticker

6/recent/ticker-posts

2.5.3 Tutu Kuletu - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 93)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.5.3 Tutu Kuletu

Tutu-tutu,

Tutu kuletu.

 

Ina uwar ɗan nan ne?

Ta tafi rafi.

 

Kira ta ta dawo,

Ta ba shi mama.

 

Ya sha ya ƙoshi,

Ya ba ni nawa.

 

Ya ba ni nawa,

Don ladan raino.

 

Takuletu,

Takuletu,

Takuletu!

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments