Ticker

6/recent/ticker-posts

2.2.2 A Fiffigi Zogale - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 73)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.2.2 A Fiffigi Zogale 

Wannan ma wasan dandali ne wanda ke da zubi da tsari irin na kwalba-kwalba dire. Mutane biyar ne ko sama da haka suke gudanar da shi.

2.2.2.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Wasan na gaɗa ne da aka fi gudanarwa da dare, musamman lokacin hasken farin wata.

2.2.2.2 Yadda Ake Wasa

Zubi da tsarin wannan wasa daidai yake da na kwalba-kwalba dire da kuma ruwan ƙauye. Saboda haka za a yi amfani da sunan masu gudanarwa irin na ruwan ƙauye domin tantance matsayin kowa a cikin waƙa. Ga waƙar wannan wasa kamar haka:

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

 Yarinya a fiffigi ɗorawa,

 Idan mamanki ta zo,

Yarinya yaya kike mata?

Mai Direwa: Hakannan nake mata,

 Har ma in juyo ina haka.

Mai direwa za ta tsuguna ta nuna alamar ladabi na gaisuwa ga iyaye.

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

 Yarinya a fiffigi ɗorawa,

 Idan babanki ya zo,

Yarinya yaya kike masa?

Mai Direwa: Hakannan nake masa,

 Har ma in juyo ina haka.

Ladabin da mai direwa ke yi da salon da take yi daidai yake da na mahaifiya. Daga nan masu cafewa za su ci gaba da waƙa:

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

 Yarinya a fiffigi ɗorawa,

 Idan uwar mijinki ta zo,

 Yarinya yaya kike mata?

Mai Direwa: Hakannan nake mata,

 Har ma in juyo ina haka.

A nan mai direwa ba za ta tsuguna ƙasa ba. Sannan za ta riƙa gaisuwar tana gatsine da alamar reni.

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

 Yarinya a fiffigi ɗorawa,

 Idan mijinki ya zo,

 Yarinya yaya kike masa?

Mai Direwa: Hakannan nake masa,

 Har ma in juyo ina haka.

A nan ma za ta duƙa cikin girmamawa da nuna alamun yin maraba.

Masu Cafewa: A fiffigi zogale,

 Yarinya a fiffigi ɗorawa,

 Idan kishiyarki ta zo,

 Yarinya yaya kike mata?

Mai Direwa: Hakannan nake mata,

 Har ma in juyo ina haka.

A nan kuma, mai direwa za ta riƙa gatsine da kallon hadirin kaji tamkar dai wadda take da kishiyar gaske a gabanta. Da zarar an zo wannan gaɓar to mai direwa ta kammala yinta. Daga nan za ta koma cikin layi, wata kuma ta fito.

2.2.2.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi da annashuwa ga masu yi da kuma masu kallo. Sannan hoto ne ko madubi da ke hasko wasu halayyar mata a gidan aure. Musamman da ɓangaren yanayin hulɗarsu da wasu mutane na musamman da suka haɗa da iyaye da miji da kuma kishiya da makamantansu.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments