Citation: Nazir Ibrahim Abbas (2023). Waiwaye A Kan Rabe-Raben Kare-Karen Harshen Hausa Na Yamma. Sch Int J Linguist Lit, 6(7): 287-295.
Nazir Ibrahim
Abbas, Ph.D.
Department
of Nigerian Languages,
Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto
email: ibrahimabbasnazir@gmail.com
Gsm: +234
8060431934
Abstract
Scholars have divergent views on the classifications of
Hausa dialects. Their classifications were based on the Hausa dialects'
linguistic features and the geographical locations of the dialects in the Hausa
land. Bargery (1934) was the first scholar who classifies the Hausa dialects
into two broad divisions of Eastern and Western Hausa dialects in the
introduction of his famous dictionary. He made the classification based on
their common linguistic features and their regional or geographical locations.
Most of the subsequent research of scholars conducted after Bargery’s 1934
dictionary followed the same footsteps of the Eastern and Western dialects
classifications, though some scholars had different views on the individual
dialects constituting the earlier two broad divisions. Some of the works of
these scholars include; Jaggar (1945), Muhammad (1978), Abubakar (1982), Amfani
(1993), Bello (1992), Musa (1995), Fagge (2002), Sani (2003), Yakasai (2006),
Muhammad (2010), Bello (2015), Musa (2015) and Bello (2016). However, the
research works of Ahmed and Daura (1970), Malka (1978), Wurma (2005), and
Zulyadaini (2005) on the other hand classified Hausa dialects on the basis of
major and minor dialects. They argued that the dialects are supposed to be
classified and studied based on popularity and populations of speakers. In
essence, the population of speakers of a dialect determines its status of being
either a major or a minor Hausa dialect. This paper attempts to make a critical
review of the scholars' classifications of Hausa regional dialects of Eastern
and Western Hausa dialect divisions with a view to highlighting some of the
neglected Western Hausa dialects found in Nigeria today that were not earlier
considered in the scholars' two broad divisions. The data of this research was
sourced mostly from the Hausa dialect works conducted by scholars and
researchers. The research discovered that the earlier classification of
individual Western Hausa dialects made by scholars was too narrow, which
resulted in merging a number of independent Hausa Western dialects into one,
instead of classifying the dialects and studying each dialect independently and
broadly.
Keywords: Hausa Dialects, Linguistic Features, Geographical
Locations, Classification of Dialects
1.0 Gabatarwa
Nazarin karin harshen Hausa wani fage ne wanda ya samu gatar kulawar masu
nazarin harshen Hausa tun lokaci mai tsawo. Ɓangaren nazarin karin harshe kuwa
yana ƙoƙarin fito da irin kamanci da kuma bambance-bambancen da ake samu
tsakanin kare-karen harshe a cikin harshe ɗaya, waɗanda ba su isa su haifar da
rashin fahimta gaba ɗaya tsakanin masu magana da harshen ba. Irin waɗannan
bambance-bambance suna fitowa a dukkan siffofin harshe na nahawu da suka
danganci furuci da ƙirar kalma da ginin jumla da kuma ma’ana, wani lokacin,
nazarin yana keɓanta ne kawai ga kalmomi da sashen jumloli da kuma jumlolin,
musamman waɗanda suka shafi wasu ayyuka na musamman, keɓantattu da ke da kalmomin
fannu.[1]
Malamai masu nazarin harshe sun bayyana cewa akwai nau’o’i biyu na karin
harshe; waɗannan nau’o’in kuwa su ne; karin harshen yanki, (wanda ake samu dalilin
yanki ko muhallin da al’umma suke zaune) da kuma karin harshe na rukuni, (wanda
ya ta’allaƙa ga shekaru ko matsayi ko jinsi ko addini ko muƙami ko sana’a ko
ilimi ko wani aiki da ya haɗa wasu gungun al’umma wuri ɗaya). Wannan bincike ya
ta’allaƙa ne ga karin harshen Hausa na yanki, wanda yake nazarin nau’in magana
da ake samu a wani yanki ko muhallin da al’umma suke zaune.
A matakin farko, malamai sun fara gudanar da irin wannan bincike na karin
harshe ne ta fuskar nazarin siffofin kare-karen harshe a ɗaiɗaikunsu (traditional dialectology) maimakon kallon karin harshe a matsayin wani al’amari ɗaya na harshe wanda ke tattare
da tsare-tsare daban-daban a cikinsa. Daga baya sai wasu malaman zamani suka faɗaɗa
fagen nazarin karin harshe da ra’in nazarin samar da jumla (Generative grammar) wanda a cikinsa ne suka samar da ra’in nazarin
karin harshe (Generative dialectology).[2]
Wannan ra’in kuwa yana taimakawa ta amfani da tsare-tsarensa na musamman waɗanda
suka shafi furuci wajen nazarin kare-karen harshe daban-daban da kwatanta su tare
da amfani da wasu dokoki na harshe.[3]
Malamai masu nazarin Hausa sun
rarraba kare-karen harshen Hausa a yankuna daban-daban, ra’ayi mafi karɓuwa
tsakanin malaman shi ne raba kare-karen harshen a ɓangaren kare-karen harshen
gabas da kare-karen harshen yamma ta la’akari da kamannin siffofin kare-karen
harshen da kuma muhalli da suke da tarihin al’ummominsu. Kare-karen harshen gabas a kason da malaman
suka yi su ne: Kananci da Bausanci da Zazzaganci da Haɗejanci da Guddiranci da
Dauranci. Kare-karen harshen yamma kuwa su ne; Sakkwatanci da Katsinanci da Arewanci
da Gobiranci. Waɗannan rabe-raben duk suna
da alaƙa da tarihin daulolin ƙasar Hausa da jinsunan Hausawan da ke cikin waɗannan
daulolin.
La’akari da tsawon lokacin da aka yi
wannan rabon da wasu dalilai na tarihi da harshe da ci gaban zamani da aka samu
a yau, wanɗanda duk suna tattare da tarihin asalin jinsunan al’ummar Hausawan da ke cikin waɗannan daulolin. Wannan maƙala ta yi
waiwaye a kan kare-karen harshen da ke cikin waɗannan rabe-rabe na karin
harshen Hausa da aka yi na gabas da yamma, musamman a yankin yamma.
Maƙalar ta ƙalailaice yawan kare-karen harshen yamma da
tabbatar da dangantaka tsakaninsu, sa’annan ta fito da wasu daga cikin siffofin
da suka haɗa su (waɗanda su ne, suka sa aka kira su kare-karen harshen yamma).
2.0 Ma’anar Karin Harshe
Malamai da yawa sun bayar da ma’anoni daban-daban na karin harshen. Wasu ma’anonin
da suka fi dacewa da tunanin wannan nazarin sun haɗa da;
Crystal (2008:142)
Dialect is a regionally or
socially distinctive VARIETY of language, identified by a
particular set of
WORDS and GRAMMATICAL STRUCTURES. Spoken dialects are usually also associated
with a distinctive pronunciation or ACCENT.
Fassara:
Karin harshe wani nau’in magana
ne da ake iya ganewa ta yanki ko rukuni a cikin harshe wanda ke da kalmominsa
da tsarin harshe da nahawu. Kare-karen harshe mafi yawa suna da tsarin
furucinsu na daban.
Finegan (2012: 371)
Dialect refers to a language variety
in its totality – including vocabulary, grammar, pronunciation, pragmatics, and
any other aspect of the linguistic system.
Fassara:
Karin harshe yana nufin nau’in
magana a cikin harshen gaba ɗayansa – wanda ya haɗa da kalmomi da nahawu da
furuci da dangantakar ma’ana da al’adar harshe da duk wani ɓangare na tsarin
harshe.
La’akari da waɗannan ma’anoni mun
lura cewa karin harshe nau’in magana
ne a
cikin harshe ɗaya wanda ake samu a wani yanki, wanda ke da bambanci da wani
nau’i na
harshen ta fuskar furuci da tsarin sauti da ƙirar kalma da ginin jumla da kuma
ma’ana waɗanda duk masu magana da wannan harshen suna fahimtarsu. Samuwar
nau’in karin harshe na yanki koyaushe ba ya rasa nasaba da tarihin muhalli ko
wurin zaman da al’umma suka samu kansu da yanayin ƙasarsu da kuma al’ummomin da
suke maƙwabtaka ko cuɗanya da su.
3.0 Ra’ayoyin Wasu Masana Kan Rabe-Raben Kare-Karen Harshen Hausa
Malamai sun rarraba kare-karen harshen Hausa ta fuskoki da
yankuna daban-daban wasu daga cikin rabe-raben da malaman suka yi sun danganci
girman kare-karen harshen ko yankunan da suka fito ko kuma kamannin da ke gare su a furuci da kuma nahawu. Girman karin harshe da ƙaranci a wannan kason malaman ba yana nufin na fifiko ba, sai
dai na yawan al’ummar da ke magana da karin harshe a wuri ɗaya. Wani karin harshen za a tarar ya fi wani yawan ƙasa da al’umma, irin wannan yanayi ne ya sa wasu malamai suka rarraba kare-karen harshen a ajin manya da ƙananan kare-karen harshe. Ta fuskar daɗewa da tsarin nahawu kuwa duk kare-karen
harshen matsayinsu ɗaya. A rabo na yanki, malaman sun kula da muhallin kare-karen
harshen Hausa suke da kuma kusancinsu da juna, wanda shi ya haifar da
tarayyarsu a mafi yawan siffofin harshe. Duk waɗannan rabe-raben tun asali suna da alaƙa ta tarihin ƙasar Hausa da kuma
daulolin ƙasar Hausa kafin haɗuwar
Hausawa da wasu al’umma. Ga yadda ra’ayoyan malaman suke a kan rabe-raben karin
harshen Hausa.
3.1 Ra’ayoyin Malamai a kan Raba
Karin Harshen Hausa a Rukunin Manya da Ƙananan Kare-karen Harshe
Ahmed da Daura
(1970) sun kawo rukunin da suka kira manyan kare-karen harshen Hausa guda bakwai
da suka haɗa da Kananci da Katsinanci da Sakkwatanci da
Dauranci da Zazzaganci da Bausanci da kuma Haɗejanci.[4]
Malka (1978) a nasa
ra’ayin ya bayyana cewa akwai manyan kare-karen harshen Hausa (14). Bakwai a
Nijeriya da kuma bakwai a Jamhuriyar Nijar. A Nijeriya akwai; Kananci ko Hausar
Kano da Katsinanci ko Hausar Katsina da Dauranci ko Hausar Daura da Zazzaganci
ko Hausar Zazzau (Zariya) da Sakkwatanci ko Hausar Sakkwato da Bausanci ko
Hausar Bauchi da Zamfaranci ko Hausar Zamfara. A Jamhuriyar Nijar kuwa malamin
ya kawo Damagaranci ko Hausar Damagaran (Zinder) da Gobiranci ko Hausar Gobir
(Tsibiri) da Adaranci ko Hausar Adar (Tahoua/Tawa) da Arewanci ko Hausar Arewa
(Dogon-Dutsi) da Kurfayanci ko Hausar Kurfai (Filinge) da Canganci ko Hausar
Cangawa (Gaya) da Agadasanci ko Hausar Hausawan Agadas.[5]
Wurma
(2005) ya kawo rabe-raben kare-karen haeshen Hausa da ake samu a Nijeriya da
kuma jamhuriyar Nijar kamar yadda Malka (1978) ya kawo. Malamin ya ce
kare-karen harshen Hausa da ake samu a Nijeriya su ne Kananci – Hausar Kano da
Katsinanci - Hausar Katsina da Dauranci - Hausar Daura da Zazzaganci - Hausar
Zazzau (Zariya) da Sakkwatanci – Hausar Sakkwato da Bausanci – Hausar Bauci da
Zamfarci – Zamfara. A Jamhuriyar Nijar kuwa
akwai Damagaranci – Hausar Damagaram (Zinder) da Gobiranci – Hausar Gobir
(Tsibiri) da Adaranci – Hausar Adar (Tahoa/Tawa) da Arewanci – Hausar Arewa (Dogon-Dutsi)
da Kurfayanci – Hausar Kurfai (Filinge) da Canganci – Hausar Cangawa (Gaya) da
Agadasanci – Hausar Hausawan Agadas.
Wurma (2005) bugu da ƙari ya bayyana cewa ba waɗannan kawai ne kare-karen harshen Hausa ba domin a Nijeriya
akwai wasu kare-karen harshen Hausa da suka haɗa da; Haɗejanci – Hausar Haɗeja da Gumalanci – Hausar Gumel da Kabanci – Hausar
Kabi/Kebbi da kuma Guddiranci – Hausar Azare/Katagum.[6]
Zulyadaini (2005) ya
bayyana cewa harshen Hausa yana da kare-karen a cikinsa da suka haɗa da Katsinanci (karin harshen Katsina) wanda ake magana da
shi a Katsina da kewayenta da Sakkwatanci (karin harshen Sokoto) wanda ake
magana da shi a Sokoto da kewayenta da Kananci (karin harshen Kano) wanda ake
magana da shi a Kano da kewayenta da Dauranci (karin harshen Daura) wanda ake
magana da shi a Daura da kewayenta da Zazzaganci (karin harshen Zaria) wanda
ake magana da shi a cikin Zaria da kewayenta da Bausanci (karin harshen Bauci)
wanda ake magana da shi a Bauci da kewayenta da Guddiranci (karin harshen
Guddiri) wanda ake magana da shi a Katagum da kewayenta.
3. 2 Ra’ayoyin Malamai a Kan Raba
Karin Harshen Hausa a Yankin Gabas da Yamma
Bargery (1934) shi
ne malami na farko wanda ya fara rarraba kare-karen harshen Hausa a cikin
manyan rukunan gabas da yamma. Malamin ya bayyana cewa karin harshen yamma ya ƙunshi
karin harshen Katsina da Zaria da Gobir wadanda sun fi kama da karin harshen
Sokoto yayin da kare-karen harshen gabas suka haɗa da; karin harshen Kano da Haɗejia
da Katagum.[7]
Malamin ya yi rabon ne ta la’akari da kamannin siffofin kare-karen harshen na furuci da nahawu.
Jaggar (1945) ya
bayyana cewa akwai nau’o’in kare-karen harshe biyu na gabas da yamma, waɗanda
ake iya bambancewa tsakaninsu. Kare-karen harshen gabas su ne karin harshen
Kano da Zaria da Bauchi da kuma Daura yayin da kare-karen harshen yamma kuwa su
ne karin harshen Sokoto da Gobir da
Arewacin Nijar.
Haka ma a tsakiyarsu akwai karin harshen Katsina da Maraɗi.
Muhammad (1978) ya
kawo kare-karen harshen Hausa shida da suka haɗa da; kare-karen harshen Daura
da Kano da Katsina da Sokoto da Zaria da Bauchi. Kare-karen harshen yamma a
ra’ayin malamin su ne karin harshen Katsina da Sokoto (har da Gobir da Zamfara
da Kebbi dake cikin yankin karin harshen Sokoto).[8]
Kare-karen harshen Gabas kuwa su ne; karin harshen Kano da Daura da Damagaran
da (Zinder a Jamhuriyar Nijar) da Zaria da Bauchi. Waɗannan rabe-raben
kare-karen harshen na gabas da yamma, malamin ya bayyana cewa akwai siffofin da
suke bambanta su.[9]
Abubakar (1982) a
kawo kare-karen harshen Gabas da Yamma kamar yadda ake samunsu a yankin ƙasar
Hausa da ke Nijeriya. A yankin Yamma ya kawo kare-karen harshen Sakkwato da
Katsina, yayin da a yankin Gabas ya kawo kare-karen harshen Daura da Kano da
Zariya da kuma Bauchi.
A ra’ayin Amfani
(1993) kare-karen harshen Gabas su
ne karin harshen Bausanci
da Dauranci da Kananci da kuma Zazzaganci. A rabon kare-karen harshen Yamma kuwa ya kawo Katsinanci da Sakkwatanci da Zamfarci. Malamin ya ƙara da
cewa akwai siffofin da suka bambamta waɗannan rabe-raben kare-karen harshen Gabas da Yamma.
Musa (1995) ya kawo rabe-raben karin harshen Hausa kamar
yadda Bargery (1934) ya kawo, ya fara rarraba kare-karen harshen Hausa a
yankunan Yamma da Gabas. Malamin ya ce kare-karen harshen Gabas sun haɗa da;
Bausanci da Dauranci da Guddiranci da Kananci da kuma Zazzaganci su kuma
kare-karen harshen Yamma su ne Sakkwatanci da Katsinanci da sauransu.[10]
Fagge (2002) ya raba karin harshen Hausa na nahiya[11]
(yanki) zuwa gida biyu dangane da muhimmanci da irin bambance-bambancen da ake
samu tsakaninsu. Rabe-raben a ra’ayainsa su ne na; Hausar Gabas wadda ta ha]a
da Kananci da Bausanci da Zazzaganci da Gudduranci da Haɗejanci. Kare-karen
harshen yamma kuwa sun ƙunshi Sakkwatanci da Kabanci da Gobiranci da
Zamfaranci, sai na Arewa da suka haɗa da; Dauranci da Gumalanci da Katsinanci
da Damagaranci.
Sani (2003) ya kawo
rukunoni biyu na karin harshen Hausa da suka haɗa da karin harshen Gabas da
Yamma. A rukunin gabas ya kawo karin harshen; Kananci da Bausanci da Dauranci
da Guddiranci da Zazzaganci. A rukunin yamma kuwa malamin ya kawo karin harshen
Arewanci (Dogon Doutchi) da Katsinanci da Sakkwatanci da kuma Kurhwayanci
(Filinge ta Jamhuriyar Nijar).
Mohammed (2010) ya kawo ra’ayin Bargery (1934) wanda ya ce ya
kasa kare-karen harshe gida biyu: (a) karin harshen Sokoto da (b) karin harshen
Kano. Ya ƙara bayyana cewa Katsina da Zaria da Gobir suna kason karin harshen
yamma ne na karin harshen Sokoto yayin da karin harshen Haɗeja da Katsina suna
cikin kason gabas na karin harshen Kano.[12]
Malamin ya ci gaba da bayanin cewa Kananci karin
harshe ne na jihar Kano yayin da ake amfani da Katsinanci a jihar Katsina. Ana
magana da Sakkwatanci a jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi duk da yake
akwai sassan karin harshen Sakkwatanci wa]anda suka samar da Zamfaranci a jihar
Zamfara da Kabanci a jihar Kebbi.[13]
Ana magana da Bausanci a Bauchi da kuma Haɗejanci a jihar Jigawa.
Bello (2015) ya fito da abun ya kira manyan kare-karen
harshen Hausa na Gabas da Yamma. Kare-karen harshen gabas da ya kawo sun haɗa
da; Kananci da Bausanci da Dauranci da Guddiranci da kuma Zazzaganci.
Kare-karen harshen yamma kuwa su ne: Katsinanci da Sakkwatanci da Kurhwayanci
da Arewanci waɗanda ake magana da su a Katsina da Sokoto da Kurfey da Dogan Doutchi
da kuma karin harshen Maraɗi.
Waɗannan rukunin ra’ayoyin malamai biyu na rararraba kare-karen harshen Hausa a rukunin manya da ƙanana da
kuma shiyyar gabas da yamma su ne fittatun hanyoyin da malamai manazarta karin
harshen Hausa suka yi amfani da su wajen rarraba kare-karen harshen Hausa.
Wannan bincike ya ta’allaƙa ne ga rabon da aka yi na shiyyar gabas da yamma. Binciken
ya mayar da hankali a kan kare-karen harshen yamma, amma wannan ba zai hana ya
kalli kare-karen harshen da yake nazari a kansu a matsayin rukunin manya da ƙanana ba ko a cikin
kare-karen harshen na yamma, domin su ma a cikinsu akwai waɗanda
suka fi wasu girma.
Kare-karen harshen
Zamfarci da Kabanci na wannan bincike a yau sun fi girma da yawan al’umma a
kan kare-karen harshen Gobiranci da Adaranci da kuma Arauci. Girman a nan yana
nufin na yawan al’ummar da ke magana da kare-karen harshen, ba wai wani fifiko na
tsari ko daɗewar karin harshe ba, domin duk kare-karen harshen daɗewarsu
ɗaya kuma za a tarar kowane yana da cikakke da ingantaccen tsarinsa na sadarwa.
4.0 Kare-Karen Harshen Hausa na Yamma
Bisa
ga rabe-raben kare-karen harshen Hausa da malamai suka yi wanda wannan maƙala ta kawo a sashe na 3.1 da kuma 3.2 mafi yawansu sun bi
tsarin da Bargery (1934) ya kawo na rarraba kare-karen harshen Hausa a rukunin
gabas da yamma ta lura da kamanni da bambancin siffofin kare-karen harshen a
nahawu da kuma yanki ko muhallin da suka fito tare da la’akari da tarihin al’ummomin.
Rukunin malaman da ayyukansu ke da ra’ayin raba kare-karen harshen Hausa a
cikin manyan kare-karen harshen Hausa sun haɗa da; Ahmad da Daura (1970) da Malka (1978) da Wurma (2005)
da Zulyadaini (2005). Waɗannan malaman sun yi
la’akari da tarihin yankunan ƙasar Hausa ne wajen
fito da waɗannan kare-karen harshen.
Malaman da suka haɗa da Bargery (1934) da Jaggar (1945) da Muhammad (1978) da
Abubakar (1982) da Amfani (1993) da Musa (1995) da Fagge (2002) da Sani (2003)
da Muhammad (2010) da Bello (2015) duk suna da ra’ayi iri ɗaya na kallon kare-karen harshen Hausa a babban rukunin gabas
da yamma wanda yake ƙunshe da ɗaiɗaikun kare-karen harshe
masu kama da juna ta siffofi da kuma kusanci na muhalli. Duk da yake akwai
ra’ayoyi mabambanta tsakanin malamai na ɗaiɗaikun kare-karen harshen da ke cikin kowane yanki na karin
harshen gabas da yamma ɗin. Dukkan rukunnan
ra’ayoyin malaman biyu na rarraba kare-karen harshen Hausa (ko dai a ɗaiɗaikunsu ko a babbar kafa
ta gabas da yamma) suna da alaƙar da ke tattare da
tarihin al’ummomin da ke yankunan da ake samun kare-karen harshen na asali.
Wasu daga cikin
kare-karen harshen yamma da malaman suka kawo, wa]anda ake samu a yammacin
}asar Hausa sun ha]a da; Sakkwatanci da Gobiranci da Arewanci (a Dogon-Dutsi da
ke Nijar) da Katsinanci da Zamfarci da Kurhwayanci (Filinge) da Kabanci. Wannan
ma}alar na da ra’ayin cewa akwai bu}atar yin bita da waiwayen wannan rabo na
kare-karen harshen Hausa na yamma kamar yadda suke a yau a yankin }asar Hausa
da ke Nijeriya ta hanyar sake dubin tarihin jinsun manyan al’ummomin Hausawa da
ke yankin da kuma wasu al’amurra da suka shafi siffofin Hausar da suka
dangancin harshe (nahawu).
Wani abin lura a nan
shi ne ba kowane daga cikin waɗannan kare-karen
harshen na yamma ya samu gata aka yi nazari a kansa ba sa’annan ko a rabe-raben karin harshen ma, ba dukkan
malaman suka ambaci kare-karen harshen da ake samu ba. Bargery (1934) da Jaggar
(1945) da Fagge (2002) kawai ne suka kawo karin harshen Gobiranci a cikin
kare-karen harshen yamma. Haka ma Fagge (2002) da Muhammad (2010) kawai ne suka
ambaci Kabanci a cikin rabe-rabensu. Bugu da ƙari daga cikin malaman Amfani (1993) da Fagge (2002) ne kawai
suka kawo karin harshen Zamfarci a cikin kason karin harshen Hausa na yamma.
5.0 Rabe-Raben Kare-Karen Harshen Hausa na Yamma a Yau
Idan aka yi la’akari
da waɗannan rabe-raben kare-karen harshe na Hausa da ci gaba da faɗaɗa su da malamai suka yi a
lokuta daban-daban duk suna da alaƙa sosai da wasu bayanan
tarihin asalin daulolin ƙasar Hausa na
Bayajida, waɗanda su ne suka samar da
masarautun da ake kira ƙasar Hausa a tarihi. A
tarihin Bayajida, akwai dauloli bakwai da ake kira na Hausa bakwai da kuma dauloli
bakwai na banza bakwai waɗanda suka kafu, suka
kuma shahara tsakanin ƙarni 12 zuwa ƙarni na 16 a wasu bayanan tarihi.[14]
Daulolin Hausa bakwai
waɗanda suka samar da asalin ƙasar Hausa su ne; Daura da Kano da Zaria da Gobir da Katsina
da Biram da kuma Rano. Yayin da daulolin banza bakwai su ne; Zamfara da Kebbi
da Nupe da Gwari da Yauri da Kwararrafa da
Ilorin. Duk da yake wannan ruwaya ta Bayajida tana da rauni a ra’ayoyin wasu
malaman tarihi, akwai wasu bayanan tarihi da ke nuna cewa a ƙarshen ƙarni na 18 wasu daga
cikin waɗannan daulolin ƙasar Hausa sun samu ƙarfin da kowaccensu ta zama jiha mai cin gashin kanta da
iyokoki da kuma al’ummominta. Al’ummomin Kano da Katsina da Zazzau da Zamfara
da Kabi, suna rarrabe kansu a matsayin Kanawa da Katsinawa da Zazzagawa da
Zamfarawa da kuma Kabawa.[15]
La’akari da tarihin waɗannan daulolin da bambancin wasu siffofi na harshe da ke
tsakaninsu ne Bargery (1934) ya fara raba kare-karen harshen Hausa a yankunan
gabas da yamma. Sai dai malamin bai fito da dukkan yankunan masarautun ba domin
a kasonsa na yamma ya kawo; Katsina da Zaria da Gobir, a gabas kuwa ya kawo
Kano da Haɗejia da Katagum. Waɗannan
yankunan gaba ɗaya suna cikin masarautun ƙasar Hausa da aka kawo a tarihin na Bayajida, in ban da Haɗejia da Katagum amma
kuma ba iyakarsu ke nan ba.
Ahmed da Daura (1970)
a bisa wannan tsari na tarihin daulolin ƙasar
Hausa ne suka kawo rukunin da suka kira manyan kare-karen harshen Hausa guda bakwai
na; Kanonci da Sakkwatanci da Dauranci da Zazzaganci da Bausanci
da Haɗejanci. Sakkwato da Bauci da Haɗejia ne kawai ba su cikin rukunin manyan masarautun ƙasar Hausa na Hausa Bakwai kamar yadda ya zo a tarihin
Bayajida.
Muhammad (1978) a nasa
kason wanda ɗori ne a kan wannan ra’ayin na Bargery (1934) sai da ya kawo
tarihin masarautun yankunan ƙasar Hausa waɗanda a ƙarni na 16 sun shahara
sosai a matsayin jihohin ƙasar Hausa masu ikon
cin gashin kansu da sarakunansu da suka haɗa da; Daura da Kano da Katsina da Zaria da kuma Kebbi. Huɗu daga cikinsu; ya ce suna daga cikin manyan masarautu nan na
"HAUSA BAKWAI" wato Daura da Kano da Katsina da Gobir da Zaria da
Biram, wasu bayanai sun maye gurbin Biram da Zamfara.
Dalilin wannan tarihi
ne, Muhammad (1978) ya fito da kare-karen harshen yankunan yamma da suka haɗa da; Katsina da Sokoto (wanda ya haɗa da Gobir da Zamfara da Kebbi, yankin da ke ƙarƙashin mulkin Sokoto na
Turawa, Sokoto Province) da Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijar. Manyan kare-karen harshen gabas
kuwa su ne; Kano da Daura da Damagaran (Zinder, a Jamhuriyar Nijar) da Zaria da
Bauchi. A nan ma idan muka lura, za mu ga cewa yankunan da ya kawo na Katsina
da Gobir da Zamfara da Kebbi da Kano da Daura da Zaria duk suna daga cikin
manyan daulolin ƙasar Hausa a tarihi. Matsalar kawai ita ce malamin bai
rarrabe kare-karen harshen Gobir da Zamfara da Kebbi (kamar yadda daulolin suke
a tarihi) a matsayin kare-karen harshen Hausa masu cin gashin kansu ba,
maimakon haka ya gwama su cikin karin harshen Sakkwatanci.
Ko a ƙarni na 18 lokacin da Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo da
mutanensa suka shigo ƙasar Hausa bayanan tarihin
sun nuna cewa sun isko ƙasar tana da manyan
dauloli masu cin gashin kansu a Zaria da Kano da Katsina. Haka ma akwai daular
Gobir da Zamfara da kuma Kebbi waɗanda su ne manyan
daulolin yammacin ƙasar Hausa. Bugu da ƙari waɗannan yankuna ne da
ke magana da harshe ɗaya, suna kuma da al’adu
iri ɗaya, amma kowace daula daga cikinsu tana da nata tsarin
tattalin arziki da iyakokin mulki da yanayin magana na harshe da ya bambanta ta
da wata
daular, ƙoƙarin faɗaɗa waɗannan iyakokinsu ya sha haifar da yaƙe-yaƙe tsakaninsu.[16]
Bayan jihadin Shehu Usmanu ma, daular Usumaniyya ta riƙe tsari da yankuna waɗannan
masarautu da ma sunayen sarautun kamar yadda yake har yau a wasu yankunan da ke
cikin ƙasar Hausa.
Wani al’amari da zai ƙara tabbatar muna da bambancin waɗannan jinsunan Hausawa shi ne irin tsagar gado da kowannensu
ke da. Kowane rukuni daga cikin mayan jinsunan al’ummar Hausawan na Gobirawa da
Zamfarawa da Kabawa da Arawa yana da irin ta sa tsagar gado da ke bambanta
asalinsa da wani rukunin. Wannan ma wata hujja ce da ke nuna muna cewa jinsunan
Hausawan suna da wani bambanci da suke ji tsakaninsu wanda ya ke alaƙa sosai da asalinsu da kuma harshe.
Gobirawa suna da tsaga
mai gado ɗaya, wadda ake yi shida a
gefen dama da bakwai a gefen hagu na fuskarsu ko kuma shida da biyar a kowane
gefe na fuskarsu tare da bille, yayin da wasu kuma ke da bille ko shatane kawai
a kowane gefe na fuskarsu. Zamfarawa kuwa suna yin tsaga mai gado biyu, tara a
kowane gefe na fuskarsu. Yayin da Arawa suke da tsage biyu-biyu da ake yi tun
daga baki har zuwa cikin kai. Kabawa kuwa suna tsaga mai gado uku-uku, tara a
gefen dama na fuskarsu da kuma sha ɗaya a gefen hagu na
fuskar.
Duk da yake ko
tsakanin jinsuna ɗaya ana iya samun ‘yan bambance-bambancen tsagen da ba a rasa
ba.[17]
Augie (1983: 38) ya bayyana cewa tsagar Gobarci tana bambanta Gobirawa da
sauran maƙwabtansu na Zamfarawa da Kabawa. Gobirawa na nufin al’ummar
masarautar Gobir, Kabawa kuwa al’ummar masarautar Kabi (Kebbi), su kuwa
Zamfarawa suna nufin al’ummar ƙasar Zamfara. Bugu
da ƙari ya ce, tsagen yana nuna
bambancin ko dai na wurin zama ko harshe ko al’adu ko kuma sana’o’i. Arawa suna
da yanki a cikin daular Kabi kuma suna da nasu al’adu yayin da Adarawa kuma
suna da yanki a cikin yankin Sakkwato ta yau da Adar ta Jamhuriyar Nijar, kuma
su kaɗai ne jinsin al’ummar Hausawan da ba su da tsagen da ya
bambanta su a cikin jinsunan da wannan nazari yake bincike a kansu.
Tabbatar da samuwar waɗannan manyan dauloli da yankuna na Gobir da Zamfara da Kebbi
da kuma yankunan mazaunin Arawa da Adarawa da kuma wasu muhimman al’amurra da
suka bambanta su, sun isa su zama hujjar da ake iya tabbatar da cewa
dukkansu al’ummomi ne na jinsunan Hausawa masu bambance-bambance tsakaninsu.
Bambance-bambancen kuwa na iya haifar da kare-karen harshen Gobiranci da
Zamfarci da Kabanci da Arauci da kuma Adaranci tsakaninsu waɗanda kuma ake iya nazari a kansu.
Lokacin da Turawa
mukin mallaka suka shigo ƙasar Hausa suka kuma
kafa tsarin mulkinsu, sun bi wannan tarihi na dauloli da masarautun ƙasar Hausa wajen kafa yankunansu na mulki. Duk da yake
Turawan mulkin mallakan ba su kafa hukumomi a dukkan daulolin ƙasar Hausa na asali ba, amma
tarihin daulolin ya taimaka wajen kafa yankunan mulkin Turawa (Provinces) na
wancan lokacin a arewacin Nijeriya. Yankunan mulkin Turawa na Arewa a lokacin
su ne; Sokoto da Kano da Borno da Bauchi da Zaria da Nupe da Kontagora da
Illorin. Haka ma akwai yankin Kabba da Bassa da Nassarawa da Muri da Yola.[18]
A nan ma idan muka
lura ko da yake ba dukkan yankunan masarautun aka ɗauka ba, za mu ga cewa Turawan mulkin mallaka sun kula da
yankunan masarautun Zaria da Kano waɗanda suna cikin
rabe-raben kare-karen harshen Hausa na gabas da malamai suka kawo. Kafa hukumomin
a waɗannan yankuna yana da alaƙa da tarihi da asalin masarautun. Haka ma yankin Sokoto ya
samu kulawa, kasancewar shi ne ya
tattara waɗannan muhimman dauloli na Gobir da Kebbi da Zamfara da kuma
yankin al’ummomin Arawa da Adarawa waɗanda
wannan nazarin yake ƙoƙarin fito da kare-karen harshensu a cikin Hausar yamma.
A shekara ta 1991 da
kuma shekara ta 1996 an kafa jihohi a yankunan Kebbi da kuma Zamfara, babu shakka wannan yana da alaƙa da tarihin asalin al’ummomin waɗannan yankuna da kuma yankunan nasu. A cikin jihar Kebbi, akwai
ƙaramar hukumar mulkin Arewa wadda mafi yawan al’ummar da ke
cikinta Arawa ne. A jihar Sokoto akwai ƙaramar
hukumar mulkin Sabon Birni da Isa waɗanda mafi yawan
al’ummarsu Gobirawa ne, ba ya ga wasu yankuna daban-daban da ake samun
Gobirawan da yawa a cikinsu. Akwai Gobirawa a cikin wasu yankuna jihar Sokoto da kuma
yankin Tsibiri (Tcibiri) da ke Jamhuriyar Nijar. Adarawa kuwa Hausawa ne da ake
samu, musamman a yankuna Ɗunɗaye da Binji da Gwadabawa da yankin Tawa da ke Jamhuriyar
Nijar. Duk waɗannan al’ummomi ne masu tarihi da yankuna daban-daban a cikin
ƙasar Hausa.
Idan aka kalli waɗannan hujjoji na asalin masarautun ƙasar Hausa da tarihinsu da rabe-rabensu da al’ummomisu tun
kafin zuwan masu jihadi da bayan kafa daular Usumaniyya da kuma bayan zuwan
Turawan mulkin mallaka har zuwa sauye-sauyen da aka samu na zamani da suka shafi
mulki da iyakoki a yau, waɗanda duk suna tattare
da tarihin al’ummomin za a ga cewa tabbas akwai buƙatar yin waiwaye a kan rabe-raben kare-karen harshen Hausa da
Bargery (1934) ya yi na kare-karen harshen Hausa na gabas da yamma. Bisa la’akari da tarihin al’ummomin, wasu kare-karen harshe
musamman waɗanda ake ƙoƙarin nazari a wannan bincike ba su samu kulawar da ta kamace
su ba a cikin kare-karen harshen Hausa na yamma. Karin harshen Gobir kawai
malamin ya kawo a cikin karin harshen yamma. Bincikensa bai kawo karin harshen Zamfarci da Kabanci da Arauci da kuma Adaranci ba.
Kare-karen harshen
Hausa na yamma kamar yadda ake samunsu a Nijeriya ta yau su ne; Sakkwatanci da
Zamfarci da Kabanci da Gobiranci da Arauci/Arewanci da kuma Adaranci. Ana iya
kallon Sakkwatanci da Zamfarci da Kabanci a matsayin manya kare-karen harshe ta
fuskar girma da yawan masu magana da su da kuma kasancewar yankunansu jihohi a
yau. Yayin da ake iya kallon Gobiranci da Arauci/Arewanci da Adaranci a
matsayin ƙananan kare-karen harshe ta la’akari da cewa yankunansu ba su
da girma sosai kuma ba su da yawan jama’a (mutane) da ke tattare wuri ɗaya (masu magana da karin harshen) kamar sauran kare-karen
harshen na farko. Asali ma yanzu, a tsari na zamani
yankunan ƙananan hukumomi kawai ke gare su a cikin jihohin Sakkwato da Kebbi
da ke cikin yankin Arewacin Nijeriya ta yau. Duk da yake wannan ba zai hana a
fito da siffofi da iyakokin waɗannan kare-karen
harshen da bambancin da ke tsakanin al’ummominsu da
sauran jinsunan Hausawa ba waɗanda su kansu, koyaushe
suke sane da su.
6.0 Wasu Siffofin Kare-Karen Harshen
Hausa na Yamma
Kare-karen
harshen Hausa na yamma waɗanda wannan nazari
ya ƙara fitowa da
su a fili a taswirar kare-karen harshen Hausa na Yamma na; Zamfarci da Kabanci da Gobiranci da Arauci da kuma
Adaranci duk suna da wasu siffofin harshe masu kama da juna waɗanda su ne suka tattara su a matsayin kare-karen harshe na
yanki guda (na yamma) baya ga wasu dalilai na tarihi da kusancin muhallin da kare-karen
harshen suke da. Waɗannan siffofin harshe
kuwa a bayyane suke, kamar yadda ake iya bambanta siffofin sauran kare-karen
harshen Hausa na gabas tun daga matakin furuci/tsarin sauti da ƙirar kalma da ginin jumla da ma’ana, suma ana iya ganin irin
nasu siffofin. A nan za a kawo misalan wasu siffofinsu da suka danganci furuci
da tsarin sauti da kuma ƙirar kalma.
A
matakin furuci/tsarin sauti ana samun wasu al’amurra masu kama da juna a
kare-karen harshen yamma a ɓangaren
sauyawa/canjin sauti alal misali sautin /Φ/ yana komawa /h/ idan wasullan a, i ko e suka biyo shi
baya a cikin wasu kalmomi kamar; hwata, hwanka, hwara, hira, hita, hita, here, heɗe, hesa. Haka ma a sautin /ts/, ana samun irin wannan sauyawar sautin zuwa /tc/
idan wasullan a, i ko e suka biyo bayansu a cikin wasu kalmomi; misalan sauyin a cikin wasu kalmomi su ne; tcada, tcaga, tsanya, tciya, tcintciya,
tcintuwa, tcegumi, tcehe, tsere. Ana samun sauyawar sautin /r/ gare zuwa sautin /l/ da /t/ da
kuma /s/ a cikin wasu kalmomin Hausar yamma misalai; galma, halshe, marka, rigat, ƙwayat,
biɗat, bugas, shigas, mayas.
A tsarin sautuka da ke zuwa a cikin kalma kuwa kare-karen harshen Hausa na yamma
suna da siga iri ɗaya a wajen naso da shafewa da kuma musayar gurbi. Misalan
naso a cikin wasu kalmomin su ne gwamna>gwanna,
ɓarna>ɓanna, zauna>zanna. Shafewa kuma ta danganci shafe wani sashe na kalma, musamman
a ƙarshen kalmar, misali a cikin kalmomin sunaye da aikatau da
kuma wakilin suna. Abubakar (2013: 707) ya bayyana cewa shafewa na nufin cire
wani sashe na na ƙarshen kalma[19].
Ana samun shafewa a karin harshen yamma cikin wasu kalmomi, misali; baya>bai, kayi>kai, ɗauka>ɗau, gawayi>gawai, sani>san, ɓarayi>ɓaray. Ana iya ganin misalan musayar gurbi a cikin kalmomin; takalmi>talkami, bagaruwa>gabaruwa,
hawainiya>wahainiya, ɗauraya>ɗarwaya, ɗingisa>ginɗisa,
gawraya>garwaya.
A ƙirar kalma kare-karen harshen yamma suna amfani da ɗafe-ɗafe masu kama da juna
wajen gina kalmomin jinsi da kuma jami’i. Haka ma kare-karen harshen suna
tarayya wajen shaddantawa/maimaita baƙi a
cikin wasu kalmomi. Daga cikin misalan kalmomin da za su tabbatar ana samun haka akwai; makaranta/makarantu/,makarantunne/makarantinne,
ma’aikata/ma’aikatu/ma’aikatinne/ma’aikatunne, kwarkawaɗa/kawarkwaɗu/kwarkawaɗinne, ƙato/ƙatuwa/ƙatanya, sakarai/sakarya/sakaranya,
kaasuwa/kassuwa, jaaki/jakki, muuciya/mucciya.
7.0 Kammalawa
Wannan maƙala ta kawo ra’ayoyin malamai a kan
ma’anar karin harshe tare da kawo ma’anar karin harshen da ta fi dacewa da wannan nazari.
Haka ma maƙalar ta tattauna rabe-raben karin harshen
Hausa a ra’ayoyin malamai da dalilan da suka haddasa yin waɗannan rabe-raben
a ɓangaren gabas da yamma da kuma rukunin manya da ƙananan
kare-karen harshen Hausa. Bugu da ƙari maƙalar ta yi waiwaiye a kan rabe-raben
kare-karen harshen Hausa na yamma da malaman suka yi bisa wasu dalilai
tare da fito da kare-karen harshen Hausa na yamma a yau
kamar yadda ake samunsu a yankin ƙasar Hausa da ke Nijeriya a
kan hujjojin tarihi da harshe da
kuma ci gaban zamani da aka samu. Daga ƙarshe
maƙalar ta tabbatar da wajabcin sake fasalin raba kare-karen harshen Hausa na
yamma ta hanyar faɗaɗa tsohon rabon da aka yi a can farko.
Manazarta
Abubakar, A. 1982. "Generative Phonology and Dialect Variation."
Thesis Submitted for the Degree of
Doctor of Philosophy & Linguistics of the University of London.
Abubakar, S. 1999. "Northern Provinces Under Colonila Rule". Groundwork of Nigerian History. Pp.
447-481. Ikemi, O. (Ed.). Ibadan: Heinemann Educational Books Nigeria, Plc.
Ahmed, U & Bello, D. 1970. An
Introduction to Classical Hausa and Major Dialects. Zaria: NNPC.
Amfani A. H. 1993. "Aspects of Hausa Dialectology." Research in African Languages and Linguistics.
Vol. 3. Pp.1-12. Kaduna: Sunnals Press.
Augi, A. R. 1983. "The Nature and Significance of Facial Marks Among
the People of Sokoto State." Zaruma
A Cultural Magazine of Sokoto State. 5th Edition. Pp. 35-40. Council
of Arts and Culture. Sokoto: Sidi Umaru Press.
Bello, A. 1992. The Dialects of
Hausa. Enugu: Fourth Dimension Publishing Co. Ltd.
Bello, A. 2015. The Hausa Dialects.
Revised Edition. Zaria, Kaduna State, Nigeria: Ahmadu Bello University Press.
Bello, A. 2016. Hausa Dialects and
Distinctive Feature Analysis Phonology, Morphology, Syntax and Lexicon.
Zaria, Kaduna State, Nigeria: Ahmadu Bello University Press.
Bergery, G.P. 1934. A Hausa-English
Dictionary & English Hausa Vocabulary. London: Oxford University Press.
Chambers, J.K. & Peter, T. 2004. Dialectology.
Second Edition. Cambridge. University Press.
Colonial Reports – Annual No. 594. Northern Nigeria Report for 1907-8 (For
Report for 1906-7, see No. 551) Presented to both honers of Parliament by
Command of his Majesty, Feb, 1909. London: Printed for His Majesty’s Stationary
Office by Darling & Son Ltd. 84-40, Bacon Street, E.
Crystal, D. (2008). A Dictionary of
Linguistics and Phonetics. Sixth Edition. UK: Blackwell Publishing.
Dogo, A. M. 1982. "The Administration of Zamfara Kingdom". Zaruma A Cultural Magazine of Sokoto State.
Pp. 20-25. Council of Arts and Culture. Sokoto: Sidi Umaru Press.
Falola, T. et. al 1989. History of
Nigeria 1 Nigeria before 1800 AD. Ikeja: Longman Nigeria Ltd.
Finegan, E. 2012. Language Its
Structure and Use. USA: Wadsworth.
Fromkin, V. Robert, R. & Nina H. 2009. An Introduction to Language. Ninth Edition. USA: Wadsworth.
Harris, P. G. 1932. Sokoto Provincial Gezetter.
Jaggar, P. J. 1945. Hausa. Amsterdam/Philadelphia:
John Benjamins Publishing Company.
Malka, J. 1978. "Nazarin Bambance-Bambance da ke Tsakanin
Daidaitacciyar Hausa (Nijeriya) da Hausar Filinge (Jamhuriyar Nijar) ta Fuskar
Tsarin Fannin Furuci". Harshe Journal
of the Department of Nigerian Languages Ahmadu Bello University Zaria, Nigeria.
Mohammed, U. A. 2010. "Analysis of Degrees of Similarities among Hausa
Dialects". Harshe 4, Journal of
African Languages. Department of Nigerian & African Languages, Ahmadu
Bello University, Zaria. Gusau, S. A. et al (Eds). Zaria: Ahmadu Bello
University Press.
Muhammad, L. 1978. Hausa Dialects. Zaria:
Institute of Education, Ahamadu Bello University, Zaria.
Muhammad, M. 1978. Hausa Dialects.
Zaria Institute of Education: University Press.
Musa, A. 2015. "Hausa Dialectal Lexical Synonyms: A Cognitive Synonymy
Approach". Bayero Journal of
Linguistics. Pp. 251-258. Yusuf. M. A. (Ed.) Kano: Bayero University Press.
Musa, A. 1995. "Issues in Hausa Dialect Boundaries". Hausa Language, Literature and Culture. The
5th International Conference. Centre for the Study of Nigerian Languages,
BUK. Bichi, A. Y. et al (Eds.).
Musa, A. 1997. "Kananci and Other Hausa Dialects: Some Observations on
Linguistic Variations." Harsunan
Nijeriya Vol. XVIII. Dedicated to the Memory of Ibrahim Yaro Yahaya
1944-1995. CSNL, BUK.
Musa, A. 2015. "Hausa Dialectal Lexical Synonyms: A Cognitive Synonymy
Approach". Bayero Journal of Linguistics.
Pp. 251-258. Yusuf. M. A. (Ed.). Kano: BUK Press.
Nahuche, I. M. 1994. "Kananci Karin Harshe ko Daidaitacciyar
Hausa."
Takardar da aka gabatar a bukin makon Hausa, Jami’ar
Usmanu Danfodio Sakkwato.
Notes on the Tribes, Provinces, Emirates and States of Northern Provinces
of Nig. Compiled from official Reports by O. Temple. Edited by C. L. Temple
(Second Ed.) 1965. Frank Cass & Ltd.
Obara, I. (Ed.) 1980. Groundwork of
Nigerian History. Ibadan: Oluseyi Press Limited.
Sa’id, B. 1972. "Hausar Sakkwato." Harsunan Nijeriya II. Centre for the Study of Nigerian Languages,
Ahmadu Bello University, Abdullahi Bayero College, Kano. Nigeria. Newman, P.
(Ed.).
Sani, M.A.Z. 2003. Alfiyyar Mu’azu
Sani 3 Karorin Harshen Hausa A Wa}e. Kano: Benchmark Publishers.
Sani, M.A.Z. 2009. Siffofin
Daidaitacciyar Hausa. Kano: Benchmark Publishers.
Shagari, A. S. & Jean, B. 1978. Uthman Danfodio: The Theory and Practice of His Leadership.
Lagos: Islamic Publications Bureau.
Shuji, M. 1993. Bargery Toolbox 1
Based on Rev. G. P. Bargery’s A Hausa-English Dictionary. Hausa Dialect
Vocabulary 1. Tokyo University of Foreign Studies: Institute for the study
of Languages and Cultures of Asia and Africa (ILCAA).
Southworth, F.C & Chander J. D. 1974. Foundation of Linguistics. London: The Free Press.
The Abdullahi Smith Centre for Historical Research, Zaria, Nigeria, 1987. A Little New Light. Selected Historical
Writings of Professor Abdullahi Smith Volume 1. Zaria: Abdullahi Smith
Centre for Historical Research. "Some considerations Relating the Formation
of States in Hausaland". Pp. 59-127.
The Abdullahi Smith Centre for Historical Research, Zaria, Nigeria, 1987. A Little New Light. Selected Historical
Writings of Professor Abdullahi Smith Volume 1. Zaria: Abdullahi Smith
Centre for Historical Research. "Some considerations Relating the Formation
of States in Hausaland". Pp. 59-127. "The Early States of the Central
Sudan". Pp. 80-111.
Wurma, A. G. 2005. Daidaitacciyar
Hausa Da {a’idojin Rubutu. Kaduna: Alatunde Rasheed Publishing Works.
Yakasai, S. A. 1995. "Sociolinguistic Factors in the Nigeria – Niger
Border: Some Phonological Differences and Adaptations." Hausa Language, Literature & Culture. The
5th International Conference. Centre for the Study of Nigerian
Languages, BUK. Bichi, A. Y. et al (Eds.).
[1] Kalmomin fannu a
cikin karin harshe sun danganci karin harshe na rukuni.
[2] Dubi Chomsky and
Halle (1968). The Sound Pattern of
English Langauge.
[3]Traditional dialectology tend to treat linguistic forms in isolation rather than as
parts of systems or structures. Generative dialectology involves application of
concepts and findings from generative grammar, especially generative phonology,
to the description and comparison of
different dialects. Chambers & Trudgill (1998:38-45).
[4] Dubi An Introduction
to CLASSICAL HAUSA and the Major Dialects, shafi na 71-127.
[5] Domin }arin bayani dubi “Nazarin Bambance-Bambancen da ke
Tsakanin Daidaitacciyar Hausa (Nijeriya) da
Hausar Filinge
(Jamhuriyar Nijar) ta Fuskar Tsarin Fannin Furuci”. Shafi na 19- 20. A cikin Harshe
ta I.
[6] Malamin ya bayyana cewa duk wa]annan kare-karen harshen
sun sha bamban da daidaitacciyar Hausa. Ana
amfani da
daidaitacciyar Hausa a makarantu da kafafen watsa labarai da wajen rubuta
littafai da kuma wajen
koyarwa a makarantu.
[7] Dubi Some Notes on Various Dialects of Hausa in A Hausa – English Dictionary and English –
Hausa
Vacabulary.
[8] A wancan lokacin Zamfara da Kebbi duk yankuna ne a cikin
Sokoto kafin daga baya su zama jihohi
[9] Domin }arin bayani dubi Muhammad (1978). Hausa Dialects. Shafi na 2-3.
[10] Ga alama a nan ba a baiwa kare-karen harshen Yamma kulawa ba
domin biyu kawai aka ambata daga cikinsu kuma a ra’ayin mafi yawan malamai
Katsinanci yana cikin kare-karen harshen Hausa na Gabas ne, wannan bincike ma
yana da irin wannan ra’ayi domin siffofin karin harshen sun fi kama da kare-karen
harshen Gabas.
[11] A wannan aikin ba a yi amfani da kalmar karin harshen nahiya
ba, a nan karin harshen nahiya yana matsayin karin harshen yanki ne.
[12] Sic. Bargery ya kawo Katsinanci cikin kason karin harshen Hausa na
Yamma ba Gabas ba kamar yadda ya fito a nan domin }arin bayani dubi, a nan kuma
akwai alamun kuskure maimaita Katsinanci a cikin duk yankunan biyu. Some notes on the various dialect of Hausa Pp.
xxiv. Bargery G. P. (1934) A HAUSA – ENGLISH DICTIONARY AND ENGLISH – HAUSA
VOCABULARY. Katsinanci da Zazzaganci kuwa a fasalin rabe-raben da malamai suka
yi bayan wannan sun koma yankin gabas, wannan bincike ma yana da irin wannan
ra’ayin.
[13] Babu wasu ayyukan
bincike sanannu masu zurfi da aka gudanar a kan karin harshen Zamfaranci da Kabanci, wannan bincike na
da manufar fitowa da su sosai a bisa faifan nazarin karin harshen Hausa.
[14] Dubi History of Nigeria 1, Nigeria before 1800 AD, pp.
51.
[15] Domin }arin bayani dubi, Hausa states Pp. 51-54 in History of Nigeria 1.
[16] Dubi Uthman Dan
Fodio The Theory and Practice of His Leadership by Shagari, A. S and Jean
B. Pp. 1- 4.
[17] Gobirawawan da ke
tsage shida da bakwai mafi yawa ‘ya’yan sarauta ne masu biyar da shida kuwa
talakawa ne. Akwai Zamfarawan da ake kira masu wutar buta da ake samu da tsage
biyu-biyu a kowane sashe na bakinsu. A cikin Arawa kuwa akwai Gubawa wa]anda
tsagensu iri ]aya ne da sauran Arawan biyu-biyu a kowane gefen fuska, sai dai
bai kai cikin kai ba gajere ne (ana cewa su ‘ya’yan mata ne a tarihi).
[18] Domin }arin bayani dubi Colonial Reports – Annula No 594,
Nothern Nigeria Report for 10907-8.
[19] Domin }arin bayani akan shafewa a Hausa dubi, Abubakar, A. 2013.
"Deletion in Hausa". In Festschrift for Abubakar Rasheed. Series No.
10. Pp. 706-735).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.