Ticker

6/recent/ticker-posts

Gabatarwa - Babi Na Biyu

2.0 Gabatarwa

A wannan babi, za a yi magana game da waƙoƙin gargajiya da suka shafi wasanni. Akwai abubuwa daban-daban da za a iya la’akari da su wurin samar da rabe-raben wasannin gargajiya na Hausa. Sai dai a nan, za a dubi ire-iren wasannin gargajiya ne na yara ta fuskar jinsi da kuma yanayin gudanarwa. Wannan ne ya kai ga samar da rukunonin wasannin yaran zuwa gida biyu kamar haka:

i. Wasannin yara maza da wasannin yara mata.

ii. Wasannin tashe da wasannin dandali.

Lura da wannan, za a kawo misalan waƙoƙin da ake gabatarwa cikin wasu wasannin yara maza da na yara mata, da kuma waɗanda ake samu cikin wasannin tashe na yara maza da mata. Tun da buƙatar wannan littafi shi ne samar wa ɗalibai bayanai game da waƙoƙin gargajiya na Hausawa, ya dace a je kai-tsaye zuwa ga waƙoƙin da ke cikin wasannin, wato ba tare da bayanin wasannin kansu ba. Sai dai kuma wani abu shi ne, samar da bayanin wasannin zai taimaka wa ɗalibai wurin samun hoton zuci na yadda tsarin falfasar waƙoƙin suke, musamman yayin da suka danganta su da salon gudanar da wasannin. Saboda haka, misalan waɗannan waƙoƙi za su taho tare da bayanin wasannin da a cikinsu ne ake samun waƙoƙin.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA
Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Post a Comment

0 Comments