Ticker

6/recent/ticker-posts

Macukule

8.7 Macukule

Wannan wasan tashe ne na maza manya. Adadin masu gudanar da shi na iya kaiwa biyar ko sama da haka. Sannan akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi. Domin kuwa akan samu ɗaya daga cikin masu wasa ya yi shigar Gwari. Sannan ya shafe fuskarsa da farar ƙasa ko wani abu mai kama da wannan. Zai kuma riƙe ƙwarangwal na kan wata dabba, kamar akuya ko tinkiya da makamantansu. Kamar dai sauran wasannin tashe, an fi guduanar da shi da dare, bayan an sha ruwa.

8.7.1 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin masu wasa zai yi shigar Gwari, kamar dai yadda aka bayyana a sama ƙarƙashin 6.7. Sai kuma su ɗunguma wurin tashe. Da yake manya ne kuma maza, sukan bi dandali ne wurin sana’o’i da kuma wuraren da mutane ke zama. Yayin da suka zo wurin da za su yi tashe, wanda ya yi shigar gwari zai juya murya, ya riƙa magana irin ta gwarawa. Zai riƙa ba da waƙa sauran kuwa na amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Salamu’alaikum, ga baƙonku Nagwari,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Shekara ta dawo,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Ni ma na dawo.

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Allah Ya kawo,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Zan muku tashen Gwari,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Yaro ba zai iya ba,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Ni ma da ƙyar na koya,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: A can ƙasarmu Gwari,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Kan kare da daɗi,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Romon kan jaki daɗi,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Tun ba wurin idon ba,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Tsutsa shinkafa ce,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Tana ko taliya ce,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Kan ƙuda kuɓewa,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Majina kitse ce,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Tumbuɗi da daɗi,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Alhaji namu yana nan,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Ba Alhajin tsiya ba,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Ya sha ruwa lafiya lau,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Wani Alhaji na nan,

Amshi: Macukule.

 

Bayarwa: Bai sha da lafiya ba,

Amshi: Macukule.

8.7.2 Tsokaci

Haƙiƙa wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Idan mutum ya dubi yadda mai waƙar ya taƙarƙare yana maganar Gwari, dole abin ya ba shi sha’awa da dariya. Sannan wasan na nuna cewa, al’adun al’ummu sun bambanta da juna. Haka abin yake duk da ma an gina waƙar wasan ne kan raha da kuma ban dariya. Kuma fa da ganin kan jaki, romonsa zai yi daɗi.

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


WASANNI A ƘASAR HAUSA

Post a Comment

0 Comments