Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Maƙaryaciya

Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

Maƙaryaciya kira ta,

Zuciyar da ta saba ƙarya.


Zuciyarmu takan yi ƙarya,

Ta sa mu tsanar waninmu,


Hakan nan ba dalili,

Sai ta saka tsanar maƙoci.


Zuciyarmu takan haɗa mu,

Husuma har da gaba.


Takan ce dubi wane,

Ɗan uwana bai da kirki.


Ba ya so na da khairan,

Ba ya son ci gaba na.


Ko takan ce dubu wance,

Ba ta ƙaunar ta ganni.


Duk da dangi ce wajena,

Tana da halin kunama.


Zuciyarmu takan hana mu,

Uzuri mui wa waninmu.


Ido duka sai mu runtse,

Ga alherin waninmu.


Takan yi raɗa gare mu,

A kunne ta ce ga wane.


Ƙoƙari a aji a da can,

Nai mas nisa haƙiƙa.


Wai shi ne yau da mota,

Da gidaje fal a birni.


Tun muna yara ƙanana,

Shegen rowa gare shi.


Ba ya kyauta gare ni,

Akan me zana so shi.


Ba ya fara da amsar,

Gaisuwa ko nai gare shi.


Saƙe-saƙen zuciyarka,

Maƙushi ne na tsumma.


Sharri ne fal cikinsa,

Ka tsaya kai tsai ka gane.


Zuciyarka idan ta ce ma,

Ko kai uzuri ga wane.


Bai kulawa kul ka ji ta,

Don Allah tambaye ta.


Me yasa shi ɗin ya sauya,

Ko dai kai ne ka canza?


Mai biye wa zuciyarsa,

Ke sa shi faɗa da dangi.


Wanda ke bin zuciyarsa,

Kan raba ka masu sonka.


Mujiya wataran takan sa,

Ka zama a cikin abokai. 


Zuciya kan yauda reka,

Mutuƙar ta auri Shaidan.


Takan sa ɗa ƙiyayya,

Da mahaifi kan dalili.


Ɗan ƙalilan yai ta ruri,

Ya bi ƙaryar zuciyarsa.


Gu ji ruɗanin tunani,

Gobara ne bai da kirki.


Zuciya mutuƙar ta harbu,

Da ruɗani da ƙarya.


Sai mai ita yai da gaske,

Zai tsira da sharrukanta.


Rabbana Sarkin sarakai,

Zuciyata Kar Ka bar ta.


Sui abota sui aminci,

Da Shaiɗan ko na minti.


Zuciya ya Jalla ba ni,

Lafiyayya don Muhammad.


Kakan su Hassan Husaini,

Musɗafa angon Khadija.


Khalid Imam Kano ce,

Mahaifar haihuwata.


Yakasai unguwarmu,

A nan na tsaya da baiti.

Malam Khalid Imam
08027796140

khalidimam2002@gmail.com

18/6/2023.

Post a Comment

0 Comments