Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta'aziyyar Ɗanborno

1. Na saka Rabbi Gwani Sarkina,

 Wanda ya ƙage uwa da ubana,

 Yau ta'azziya zan yi wa kowa.

2. Rabbi ka ninka salatai sosai,

 Gun mai gatan sama da ƙassai,

 Alu, Sahabu da masu biyowa.

 

3. Mun yi rashi ba ɗan karami ba,

 Wanda ba zai iya mantawa ba,

 Auwalu Garba gwani son kowa.

 

4. Mai kirki ne ga shi da zafi,

 Gun nazari duk yai mana zurfi,

 Alƙawari baya saɓawa.

 

5. Mai haƙuri ne ba shi da ɗaci,

 Ga barkwanci har da kawaici,

 Ya yi zumunci Ɗanbarnawa.

 

6. Shi marubuci ne tacecce,

 Mai hikima da azancin gaske,

 Bai son raini bai rainawa.

 

7. Baya tsoron haushin kowa,

 Ko suka, zagi da ɗagawa,

 Ya riƙe Allah bai da zaƙewa.

 

8. Gun addini an masa shaida,

 In ya yi sanyi sai ya yafi randa,

 Har da amana bai cinyewa.

 

9. Gun sulhu shi limami ne,

 Kwatar haƙƙi kai shaida ne,

 Don Ɗansanda ne son kowa.

 

10. Auwalu ya tafi ba dawo wa,

 Kai! Mutuwa tayo gaggawa,

 Da ta raba mu da mai koyarwa.

 

11. Yau Kati ba mai lale shi,

 Gun sharhi ba wanda ya kai shi,

 Nasan duk kun yo shaidawa.

 

12. Ya Allah ka ji Ɗanbarno,

 Allah dubi gidan Ɗanbarno,

 Raya don kai ke rayawa.

 

13. Allah haskaka inda ya kwanta,

 Rabbi haɗa shi da Baban Binta,

 Amin, don za kai amsawa.

 

14. Dangin juna ga ta'azziya,

 Gun marubuta nai marsiyya,

 Har Ahali nasa ban mantawa.

 

15. Mamman ne daga birni Borno,

 Mai ƙaunar Auwal Ɗanbarno,

 Ke ta'azziya kan ya isowa.

Daga

Mohammed Bala Garba
9 Dul Hajji, 1444 AH
27 Yuli, 2023 M
10:57am

Post a Comment

0 Comments