Ticker

6/recent/ticker-posts

Shehu jagoran Jahas Sakkwato, Bajini na Sarkin Kudu...

 Shehu jagoran Jahas Sakkwato, Bajini na Sarkin Kudu...
"Da za ka je Kano Alhaji Sir Abubakar hwaw wata addu'a yay yi ma,
Taron nan da za ka na,
Allah kaika lahiya,
Allah sa a watce taron nan lahiya
Ka dawo muna lahiya
Shehu jagoran Jahas Sakkwato,
Bajini na Sarkin Kudu..."

Inji Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo Yauri a cikin waƙarsa mai amshi "Gwamnan Jahar Sakkwato, Shehu Kangiwa mai niyyar riƙon gaskiya, bajini na Sarkin Kudu". Marigayi mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III a gefen hagu tare da marigayi mai girma tsohon Gwamnan Jihar Tsohuwar Jihar Sakkwato, Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa (Turakin Argungu /Turakin Kabi). Allah ya jiƙan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815

Post a Comment

0 Comments