"Jama'a ku duba tun dag Jega niyyi burki Ƙaura,
Bakin gidan Alu Haidara kun ji masu kuɗɗi Ƙaura"
Inji Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan Anace Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato a cikin Bakandamiyarsa, watau Waƙar Ɗan Dambe Alhaji Abubakar Yarkofoji da aka fi sani da suna 'Shago' /Shagon Bakura, Shagon Mafara. Wannan shi ne marigayi Alhaji Aliyu Haidara Ƙaura Namoda da aka fi sani da suna Alhaji Alu Haidara. Malamin addini kuma shahararren Ɗan Kasuwa, Attajiri mai aikin tawali'u. Allah ya jiƙan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.
Daga Taskar
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
1 Comments
Masha Allah.
ReplyDeleteYau na ga Alu Haidara.
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.