Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zama Da Mijin Da Ba Ya Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam tanbayana shi ne ina da miji yanzu a haka 'ya'yanmu 3 amma baya sallah. Ba yadda ban yi ba idan ya fara sai ya bari amma sallar juma'a baya wuce shi yanzu a haka mahaifina yace zai yi kararsa ya sake ni tunda baya Sallah to malam in kashe auren ne ko yaya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Tabbas idan har anyi masa nasiha amma bai ji ba, to bai halatta ki cigaba da zama amatsayin matarsa ba. Domin kuwa akwai sashen Malaman Musulunci dake ganin cewa ko da sallah guda ce mutum ya barta da gangan to ya kafirta, balle kuma shi Mijin naki wanda ba ya yin dukkan sallolin ma in banda Juma'a.

Abin lura anan shi ne tun ranar da aka daura aurenku aka damƙa masa amanar ciyar dake da tufatar dake, da kuma koyar dake addini. To Mutumin da shi kansa ba ya yin sallah, ta yaya zai koyar dake addini?. Ta yaya zai koya ma 'ya'yanku kulawa da muhimmancin sallah? Cigaba da zama dashi awannan halin zai iya kaiwa zuwa ga lalacewar taki tarbiyyar ma. Kuma zai wahala bai lalata tarbiyyar yaran naku ba.

Manzon Allah ﷺ Ya ce: "SALLAH ITA CE GINSHIKIN ADDINI. WANDA YA TSAYAR DA ITA, TO HAKIKA YA TSAYAR DA ADDINI. WANDA KUMA YA RUSHETA TO HAKIKA YA RUSA ADDINI". Kuma ya faɗa a cikin wani hadisin wanda Muslim ya ruwaito : "TSAKANIN MUTUM DA TSAKANIN SHIRKA DA KAFIRCI SHI NE BARIN YIN SALLAH".

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅��𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments