Ticker

6/recent/ticker-posts

Fasihahhiya: Gudummuwar Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy a Fagen Kimiyyar Harshe

 Citation: Sani, A-U. (2021). Fasihahhiya: Gudummuwar Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy a Fagen Kimiyyar Harshe. In Yakasai. S.A. et al (eds), A Great Scholar And Linguists: A Festchrift in Honour of Professor Ibrahim Ahmad Mukoshy, Pp, 537-543. Kaduna: Amal. ISBN 978-978-59094-3-2.

Fasihahhiya: Gudummuwar Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy a Fagen Kimiyyar Harshe

Na

Abu-Ubaida Sani

Department of Educational Foundations
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Phone No: 08133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com 

J - Jalla maƙagin kowa,

Allahu mai rayawa,

Gare ka nai roƙowa,

Na ilmi har ma baiwa,

 Kullum ba ka gajiyawa.

 

I - Ilahu yau ma ga ni,

Sai dai a yau ta sauya zani,

Domin kusan karambani-

Na ne kawai ya saka ni,

 Wannan aiki nai farawa.

 

N - Na soma aiki mai tsauri,

Batu a kan mashahuri,

Da ke buƙatar tsari,

Da zurfafawar nazari,

 Ƙimarsa na ruɗarwa.

 

J - Jalla ba za ni iya ba,

Tab! Ba na ma fara ba,

Da son ka Sarki Rabba,

Zan yi shi ba tababa,

 Abin yana rikitarwa.

 

I - Idan rana ta fitowa,

Tafi fa bai karewa,

Muruci in ya fitowa,

Ga dutsi yai shiryawa,

 Ka fi su sai hangowa.

 

N - Na so a ce ku biyo ni,

Mu taka dukkan tsani,

Tare da ku kuma ga ni,

Domin ku fahimci bayani,

 Kansa gwani ɗan baiwa.

 

 

 

 

 

A - A farko dai sunansa,

Ibrahim Ahmad sunansa,

Mukoshy inkiya nasa,

Maiwurno ne tushensa,

 Sakkwato can gun baiwa.

 

G - Gimshi wajen ilimi ne,

Idan batun haifa ne,

Ɗai ga wata na ɗaya ne,

Na shekarar nayintin ne,

 Sai foti wan ɗorawa.

 

A - Akwai ɗiya shida gunsa,

Jamilu babban ɗansa,

Ahmad Rufa’i ka bin sa,

Sai Faɗima ban Musa,

 Mamman da Maimuna nawa.

 

F - Firɗi! Batun karatunsa,

Maiwurno yai farkonsa,

Da ke Sudan can nesa,

Nayintin foti sabin sa,

 Sai fifti wan ƙarewa.

 

A - Al’mahad Al-ilmin nan,

Da ke a Omdurman ɗin nan,

Intermediate School  ɗin nan,

Nayintin fifti tu ɗin nan,

 Fifti sabin ya yi kammalawa.

 

R - Rankayawa yai sakandari,

A Khartoum can yai nazari,

Captic College wurin nazari,

Nayintin fifti ed fari,

 A sisti ed yai ƙarewa.

 

 

 

 

 

F - Farko nayintin sisti tiri,

Ibadan ya fara yin digiri,

Yunibasiti nan yai nazari,

A sisti fo cikon ƙuduri,

 Ashekar yai ƙarewa.

 

E - Elum boko bai  masa ba,

Domin bai tsaya haka ba,

Sai da ya ƙara ciwo gaba,

Karatu tuni ya zam babba,

 Tabbas ko ya yi ƙwarewa.

 

S - School of Oriental ya je,

London can ƙasar waje,

Jami’ar Wisconsin ya je,

Da ke a USA ta waje,

 Duk ilm yai ƙarowa.

 

A - Akwai yunibasitin nan,

Sudan a Khartoum ɗin nan,

Tuni ya je har wannan,

Domin biɗar ilmin nan,

 Babba abin gaisarwa.

 

I - Idan ko kwalifikeshin ne,

Tuli garai kowanne,

Abin a-zo-a-yaba ne,

Arabik wannan Ibadan ne,

 Yunibasiti yai amsowa.

 

B - B.A. a harshe da al’ada,

Wisconsin can ya ida,

M.A. a Linguistics wanda-

Wisconsin shi ma ya ida,

 Abin gwanin ban sha’awa.

 

 

 

 

 

R - Rawar ganin da ya taka,

Yunibasiti da ya sauƙa,

Can Khartoum ba shakka,

Hakan a Linguistics ya saka,

 Ph. D. yai samowa.

 

A - In batun harshe kuwa,

Yana fahimtar da yawa,

Sa Larabci farawa,

Da Ingilishi daɗawa,

 Fillanci ya yi ƙwarewa.

 

H - Har French yai ganewa,

Hausa ko sai ƙyalewa,

Domin ko ya yi ƙwarewa,

Ya yi fice da zarcewa,

 Fitilarsa na haskawa.

 

I - Idan batun littafai ne,

Ya yi tuli kowanne,

Abin a-zo-a-gani ne,

Suna ilmantarwa ne,

 ‘Fulɓe’ kui dubawa.

 

M - Mutuncin Shehu ya duba,

Ya zayyano ba wai ba,

Siffofin Shehu je duba,

Transciency Nomadism duba,

 Mobile Education Kammalawa.

 

A - A Fulfulde-English Dictionary,

Wannan an masa tsari,

Tindinore Demuwa ya yi ƙari,

Kaɗan ke nan cikin tari,

 Yawansu ya fi ƙirgawa.

 

 

 

 

 

H - Haka yai littafai da yawa,

Sun fi gaban ƙirgawa,

Sannan editan masu yawa,

Gime Fulfulde farawa,

 Sannan da wasu da yawa.

 

M - Matsayi ya fa rirriƙe,

Mai ji zai yo kasaƙe,

Nauyin kansa ya sauƙe,

Cikin adalci ya riƙe,

 Kowa yana ta yabawa.

 

A - A ɓangaren koyarwa,

Ya je makaranti da yawa,

Kamar a Sokoto farawa,

Nizamiyya yai koyarwa,

 Kowa yana ta yabawa.

 

D - Daɗi an ji a Ibadan,

Aikin da yai gadan-gadan,

Sun so riƙe shi har abadan,

A yunibasiti na Ibadan,

 Kowa yana ta yabawa.

 

M - Mukoshy har a London ma,

Ya nuna ɗabi’un girma,

A jami’ar S.O. gama,

Ya yo aiki babu zama,

 Sabo da zimmar koyarwa.

 

U - UDUS garai ai gida ne,

ABU sananne ne,

BUK ma sananne ne,

Unimaid ba baya ba ne,

 Har Khartoum ya yi koyarwa.

 

 

 

 

 

K - Kowa yana son barka,

Da fatar ƙara ɗaukaka,

Al’umma duk na son ka,

Saboda kyawun halinka,

 Da ƙoƙarin ilmantarwa.

 

O - Organized mai recognition,

Ga Allah shi yai submission,

Gaskiya yai adhesion,

Outstanding in nation,

 Farfesa ka sam dacewa.

 

S - Sannan yana da karamci,

Ga shi da kirki da mutunci,

Faɗin gaskiya duk ɗaci,

Amana ba ha’inci,

 Rayuwar abin burgewa.

 

H - Har kullum kai dace,

Wannan gare ka du’a’i ce,

Aljanna ga kai ta kasance,

 Makoma wurin hutawa.

 

Y - Yawan baitukan talatin ne,

Sai shida ‘yan ƙari ne,

Na ƙanƙanin ɗalibi ne,

Abu-Ubaida sunan ne,

 Hamdan nai ƙarewa.

Post a Comment

0 Comments