Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara

Cite this article as: Sani, A-U., Maikwari, H.U., & Bazango, B. (2022). Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara. In Bakura, A.R. et al (eds). Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, Vol. 1, Issue 1, p. 95-107.

Abu-Ubaida Sani

Haruna Umar Maikwari

Babangida Bazango 

Tsakure

A yau, kafafen sada zumunta sun kasance wani ɓangare na rayuwar al’umma, musamman matasa. Suna da tasiri (mai kyau ko marar kyau ko duka biyu) a ɓangarorin rayuwa daban-daban da suka haɗa da zamantakewa da kasuwanci da ilmi da sana’o’i da mulki da shugabanci da makamantansu. La’akari da haka ne ya sa wannan bincike ya yi ƙoƙarin haska fitilarsa domin ƙyallaro ko kafafen na da tasiri a kan tashe-tashen hankulan jahar Zamfara? Idan suna da , yaya nauin tasirin yake? Binciken na da manufar (i) bitar yanayin tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da (ii) nazartar tasirin kafafen sada zumunta kan waɗannan tashe-tashen hankula. Kasancewar Zamfara ɗaya daga cikin manyan daulolin ƙasar Hausa masu tsohon tarihi. Binciken ya yi amfani da Bahaushen rai domin jan akalarsa. An ɗora aikin a kan tunanin Bahaushe mai cewa: “kowane allazi da nasa amanu.” An bi manyan hanyoyi guda biyu domin tattara bayanai. Na farko shi ne hira da aka yi domin samun bayanan nau’ukan tashe-tashen hankulan daga tushe (ganau ko jiyau daga ganau). Na biyu kuwa, an bibiyi kafafen sada zumunta da sauran kafafen sadarwa na yanar gizo (intanet) domin ganin wainar da ake toyawa dangane da batun da ake magana kansa, tare da tattarowa da nazartar bidiyoyi da hotuna da rubuce-rubuce da suka shafi manufar binciken. Binciken ya gano cewa, duk da ɗimbin amfanin kafafen sada zumunta, suna taka rawa kai tsaye ko a kaikaice wajen ruruta wutar tashe-tashen hankular jahar Zamfara. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga hukomomi da su fara tunanin yin wata huɓɓasa na bibiya da jagorancin al’amuran kafafen sada zumunta.

Fitilun Kalmomi: Zamfara, Kafafen Sada Zumunta, Tashe-Tashen Hankula

1.0 Gabatarwa

Duk da kiran da Abubakar Ladan Zariya ya yi cewa: “Fitina Bacci take ba ta fita," da kuma tofin Allah wadai da ya yi wa masu tado da ita,[1] wasu kam ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa. A ‘yan shekarun baya-bayan nan, musamman daga wajajen 2013 abin da ya yi sama, an ci gaba da samun tashe-tashen hankula nau’uka daban-daban. Tashe-tashen hankulan sun haɗa da garkuwa da mutane da kai farmaki kan al’umma musamman mazauna karkara da sace-sace.

Zamfara ƙasar Hausawa ce,[2] wadda kuma tana daga cikin (ƙannai bakwai) banza bakwai. A hirar da aka yi da Bunza, (2019) a gidan rediyon Pride FM na Gusau, ya bayyana ra’ayin cewa: “A yi ƙoƙarin binciko tushen Hausa daga Zamfara.” A bisa wannan dalili, akwai buƙatar gudanar da Bahaushen nazari dangane da yanayin da ƙasar ta tsinci kanta. Kamar yadda Bahaushe ya faɗa: “Ruwa ba ya tsami banza.” Dole ne a gano yadda ƙasar al’umma da ke da tarihi na tarbiyya da zamantakewa mai nagarta (halaye da ɗabi’un Hausawa na ƙwarai) ta wayi gari cikin halin tashin hankali . Bincike-binciken da za a gabatar na iya shafar ɓangarori da dama, sannan na iya kasancewa ta fuskoki da dama, duk dai domin a gano:

i.                    Mafari ko tushen inda matsalar take domin a yi wa tufkar hanci daga tushe,

ii.                   Gano tasirin nau’ukan kayayyakin amfanin yau da kullum wurin ruruta lamarin,[3]

iii.               Ƙoƙarin gano waɗanda ke da hannu cikin tashe-tashen hankulan kai tsaye ko a kaikaice domin shawo kan matsalar.

iv.               Nazartar fasali da siga na tashe-tashen hankulan domin ba da hasken kan yadda za a tunkari matsalar.

Wannan bincike ya ta’allaƙa kan mas’ala ta biyu (ii) da aka zayyana a sama. Binciken ya mayar da hankali wajen nazartar tasirin kafafen sada zumunta a tashe-tashen hankulan na jahar Zamfara. Farfajiyar binciken ba ta wuce jahar ta Zamafara ba. Saboda haka, ko da akwai yanayi makamancin wanda ake magana a kai, ba za a waiwaice shi ba idan dai ya fita daga bagiren binciken.

1.1 Manufar Bincike

Babban manufar wannan bincike ita ce nazartar yanayi da matsayin kafafen sada zumunta a tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. Kai tsaye aikin zai mayar da hankali kan:

i.                    Bitar yanayi da sigar tashe-tashen hankulan jahar zamfara, da

ii.                  Nazartar rawar da kafafen sada zumunta ke takawa a tashe-tashen hankulan.

1.2 Ra’in Bincike

Ƙasar Zamfara na ɗaya daga cikin ƙasashen Hausa masu tsohon tarihi. Wasu daga cikin masana na ganin cewa: “Idan za a lalubo asalin Bahaushe da tushen Hausa, to a neme shi a Zamfara.”[4] A bisa wannan dalili, aikin ba zai je wani wuri daban domin kalen ra’in da zai masa jagora ba. An ɗora aikin kan ragamar tunanin Bahaushe da ke cewa: “Kowane allazi da nasa amanu.” A bisa wannan tunani, kafafen sada zumunta sun kasance hanjin jimina, wato akwai na ci akwai na zubarwa. Ma’ana ke nan, suna taka rawa iri biyu dangane da tashe-tashen hankulan Zamfara. Suna taimakawa a ɓangare guda, a ɓangare ɗaya kuwa suna ƙara iza wutar matsalar. Idan haka ne kuwa, ya rage ga wannan bincike ya bi dabaru da hanyoyi mafiya dacewa domin tabbatar da wannan ikirari ko ƙaryata shi.

1.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike

An bi manyan hanyoyi uku wajen gudanar da wannan bincike. Ta farko ita ce bitar ayyuka daban-daban da aka gudanar dangane da tashe-tashen hankula musamman waɗanda suka shafi jahar Zamfara. Wannan ya ba da haske game da yanayin tashe-tashen hankulan.

Bayan wannan, wata hanya da aka yi amfani da ita wajen tattara bayanai ita ce bibiyar kafafen sada zumuta domin zaƙulo hotuna da bidiyoyi da rubuce-rubuce dangane da batun. An yi ƙoƙarin sakaye sunayen waɗanda suka ɗora ire-iren bayanan a kafafen na sada zumunta saboda dalilai na tsaro.

Daga ƙarshe kuwa, an yi hirarraki da mutane daban-daban sannan a matakai mabambanta. Yayin waɗannan hirarraki, an yi la’akari da wurin zama da shekaru da ilmin duniya da kuma cuɗanya da kafafen sada zumunta daga ɓangaren waɗanda aka yi hirar da su. Manyan ɓangarorin da hirarrakin suka taɓo su ne:

i.                    Tantance ingancin duk wasu bayanai da aka samu daga kafafen sada zumunta, da

ii.                  Samun bayanai game da yanayin tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da

iii.               Samun bayanai dangane da tasirin kafafen sada zumunta kan tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da kuma

iv.               Tantance bayanai da aka samu daga hirarrakin.[5]

1.4 Bitar Matsayin Kafafen Sada Zumunta a Zamantakewa

A duniyar yau, kafafen sada zumunta sun zama wani ɓangare na rayuwar al’umma. Kusan za a iya cewa, duniyar mutane ba za ta iya rayuwa ba sai da su. Dalili kuwa shi ne, rayuwar mutane da dama ta dogara kacokan kan ire-iren waɗannan kafafe. Nan ne cinsu, nan ne shansu![6] A rahoton da Clement, (2019: 2) ya fitar, masu amfani da kafar Whatsapp a wata kaɗan sun kai kimanin biliyan guda da miliyan ɗari biyar (1,005,000,000). Binciken da Jayasekara, (2015) ya gudanar ya nuna cewa, ana samun ƙaruwar masu amfani da kafafen sada zumunta matuƙa.

Masana da manazarta da dama sun yi bincike da rubuce-rubuce game da tasirin kafafen sadarwa a zamantakewa.[7] Siddiqui & Singh sun bayyana cewa:

Now a day’s social media has been the important part of one’s life from shopping to electronic mails, education and business tool. Social media plays a vital role in transforming people’s life style. Siddiqui & Singh, (2016: 71)

Fassara

A yau, kafafen sada zumunta sun zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan’adam tun daga kan sayayya da tura saƙonni da ilimi har zuwa kasuwanci. Kafafen sada zumunta suna taka muhimmiyar rawa dangane da salon rayuwar mutane.

Lallai wannan batu haka yake, domin kuwa ko a ƙasar Hausa akwai mutane da dama da suka rajaa matuƙa kan kafafen na sada zumunta. Akwai muhimman ɓangarorin rayuwa da waɗannan kafafe suka fi shafa. Sun haɗa da:

i.                    Sada zumunta

ii.                  Tattaunawa a matakin ɗaiɗaiku ko ƙungiyoyi

iii.               Kasuwanci da cinikayya

iv.               Ilimi da karantarwa

1.      Tun farko dai waɗannan kafafe an samar da su ne domin sada zumunta. Misali, Facebook da aka samar a wajajen 2004, ya kasance huɓɓasa ne na ɗalibin Jami’ar Harvard mai suna Mark Zuckerberg. Ya ƙirƙire shi ne a matsayin kafar sada zumunta tsakanin ɗaliban makaranta. Sannu a hankali ɗaliban wasu makarantu na daban suka fara amfana da shi.[8] A shekarar 2006 ne kuma aka fitar da shi a matsayin kafar sada zumunta da duniya gaba ɗaya za ta iya amfani da shi (Baruah, 2012: 4; Clement, 2019: 2). A zuwa yau, Facebook ke kan gaba duk cikin kafafen sada zumunta. Wasu daga cikin fitattun kafafen sada zumunta bayan shi sun haɗa da:

a.      Instagram

b.      Twitter

c.       Whatsapp

2.      A ɓangare guda kuwa, ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da kuma maaikatu na amfani da waɗannan kafafe wajen tattaunawa. A tattaunawar da aka yi da Babban Mai Kula da Ayyuka (Senior Vendor Manager) na kamfanin Amsoshi Digital Services[9], ya bayyana cewa:

Ta hanyar kafafen sada zumunta ne kamfani ke samun damar tattaunawa alhali kowa yana gidansa... Matsalar da aka fi fuskanta ita ce, har yau an bar Hausawa a baya a wannan fanni. Ko da tattaunawa za a yi, sun fi ganewa da Whatsapp kawai da Facebook, watakila saboda sun fi sauƙin shaani. (Arabi, 2019)

Ko ba komai, kafafen na tallafa wa kamfanoni wajen sauwaƙa kuɗaɗen zirga-zirga (don zuwa tarurruka). A maimakon tafiye-tafiye domin ganawa, akan tattauna ne kawai ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.

3.      Ana amfani da kafafen sada zumunta wajen kasuwanci. A wannan ɓangare matan Hausawa ma ba a bar su a baya ba wajen morar wannan dama. Kafafen sun taimaka wajen ba wa mata damar gudanar da kasuwanci a natse, ba tare da dole sai sun fita waje domin kasa haja ba. A maimakon hakan, suna kasa hajar ne bisa iska a kafafen sada zumunta. Waɗanda suka yaba, za su tuntuɓa ta waɗannan kafafen. A hirar da aka yi da Malama Sa’adatu Umar Ɗandare, ta bayyana raayinta game da matsayin kafafen sada zumunta kamar haka:

A nawa kasuwanci, kafafen sada zumunta su ne jigon kasuwa saboda kayan da duk zan saya ta intanet zan gan su, kuma ta nan zan sayar da su. (Ɗandare, 2019)

 

Shi kuwa Malam Muhammad Zulyadain[10] yana ganin ai rayuwa ma kacokan ba ta yiwuwa a yau sai da kafafen sada zumunta.[11] A ɓangaren kasuwancinsa, ya ce:

Yanzu kusan kasuwanci ya koma yanar gizo kama daga manya har ƙananan kasuwanci... Kaso mafi yawa (ɓ75%) na abokan huldar kasuwancina muna haɗuwa ne a kafafen sadarwa. (Zulyadain, 2019)

 

4.      Tuni kafafen sada zumunta suka zama wani fili na koyo da koyarwa. Ko bayan rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyi da odiyo-odiyo na ilmi da ake yaɗawa ta kafafen, akwai shafuka da zauruka da ake buɗewa na musamman domin karantarwa. Karatun kuwa yakan shafi ɓangarorin rayuwa daban-daban. Sun haɗa da addini da kimiyya da kiyon lafiya da ilmin intanet da ilmin kwamfuta da ilmin zamantakewa da ilmin kasuwanci. Wasu daga cikin fitattun makarantun da ake da su kan kafafen sada zumunta sun haɗa da:

a.      Hausa Musical Institute

b.      Makarantar Malam Bambadiya

c.       Zauren Markazus Sunnah

2.0 Tashe-Tashen Hankula a Zamfara

A shekarun baya, tun kafin shekarar 2007, Zamfara ta kasance cikin ruwan sanyi.[12] A wancan lokaci, akan samu ƙananan laifuka ne kawai irin su sace-sace ko rashin jituwa tsakanin al’umma da kan kai ga faɗa da dai makamantansu.[13] Aminu, (2020)[14] ya bayyana cewa: “A wancan lokaci, babban aikin taaddanci da ke wakana shi ne faɗa tsakanin matasan shiyar gabas da na yamma.” Faɗan na yin tsananin da har yakan kai ga samun munanan raunuka ko ma rasa rayuka. Wani nau’in aikin ta’addanci da ake samu wanda kan kai ga munanan raunuka ko rasa rai shi ne bangar siyasa.

Daga wajajen 2008 ne kuma aka samu ɓullowar tashe-tashen hankula cikin nau’uka daban-daban da suka haɗa da:

i.                    Fashi da makami

ii.                  Satar shanu

iii.               Garkuwa da mutane

iv.               Hare-hare (Almustapha, 2020; Aminu, 2020; Ibrahim, 2020)[15]

Tsakanin 2008 zuwa 2019 an samu rashe-rashen rayuwa da salwantar dukiyoyi sakamakon waɗannan tashe-tashen hankula. Duka waɗannan ayyuka akan danganta su ne da Fulani. Binciken ya ci karo da bayanan da ke tabbatar da cewa, tushen tashe-tashen hankulan ya samu tsira ne a sakamakon fansa da Fulanin suka ƙuduri ɗauka game da rashin adalci da suke ganin an yi masu. Wannan ya kasance ta fuskoki biyu:

i.                    Bayan an fara samun yawaitar fashi da makami, wasu daga cikin jami’ai ‘yan sa kai sun danganta abin da ayyukan Fulani. Daga nan ne suka ɗauki mataki kan Fulanin da suke zargin na da hannu cikin fashi da makamin. A hirar da aka yi da Almustapha, (2020) da Ibrahim, (2020) sun tabbatar da cewa, ɗaya daga cikin shuwagabannin Fulanin ya taɓa bayyanawa ƙarara cewar sun kai wasu hare-haren ne a matsayin ɗaukar fansa. Daga cikin garuruwan da aka kai wa waɗannan hare-hare na ɗaukar fansa akwai Kizara da ke ƙaramar hukumar Gusau da Yargaladima da ke ƙaramar hukumar Maru da kuma wasu ƙauyukan yankin Ɗansadau.

ii.                  Aminu, (2020) ya bayyana a hirar da aka yi da shi cewa, wasu daga cikin masu hannu cikin tashe-tashen hankulan sun yi iƙirarin bin hanyar sakamakon karya masu alƙawari da aka yi. Sun bayyana cewa, yan siyasa sun masu alƙawura goshin zaɓen 2007 (yayin da ‘yan siyasar suka ɗauke su a matsayin ‘yan bangar siyasa). Bayan zaɓe kuwa, sai aka yi abin da Bahaushe ce ke cewa: “An ci moriyar gangan, an ya da goronta!” Ko ma dai yaya abin yake, to “da walakin goro a miya,” domin kuwa “ruwa ba ya tsami banza.”

iii.               Wasu daga cikin masu riƙe da makaman na ikirarin cewa, an ƙwace gonakan da suke noma an mallaka wa ‘yan siyasa. Hakan ya samar masu da takunkumin tattalin arziki da dole sai sun nemi mafita. Idan laila ta ƙiya sai a koma basha.

iv.               Wasu kuwa na kukan cewa, burtalan[16] da suke bi aka mayar gonaki. Shiga gonakan kuwa ya kasance laifi da ke janyo hukunci ga duk wanda ya aikata. Wannan ya sa makiyayan suka kasance cikin wahala. Da tura ta kai bango, sannan tafiya ta yi tafiya, sai hannun agogo ya juya.

v.                  Akwai kuma masu ikirarin cewa, an fara samun yawaitar tashe-tashen hankulan ne tun lokacin da aka fara sace wa Fulanin yankin dabbobinsu. A wannan lokaci, ɓarayin shanun ɗauke da makamai na far ma ƙauye tare da kwashe shanu masu adadi da yawa. Dabbobin kuwa na daga cikin kaso mai tsoka daga ɓangaren tattalin arziki wanda makiyayan suka dogara a kai domin rayuwa.[17]

A ɓangare guda kuwa, akwai masu yi wa tashe-tashen hankulan kallo na daban. Dangane da musabbabinsu, tashe-tashen hankulan, binciken ya ci karo da ra’ayoyi da suka haɗa da:

i.                    Akwai waɗanda ke da fahimtar cewa, ummulhaba’isin waɗannan fitintinu shi ne albarkatun ƙasa (musamman zinare)[18] da Allah ya azurta ƙasar Zamfara da shi. Hakan ne ta sa ake ta ƙirƙirar tashe-tashen hankula domin kore mazauna ƙauyuka daga muhallansu. Hakan zai ba da damar haƙar zinaren hankali kwance.

ii.                  Wasu kuwa, musamman malaman addinin Musulunci, na da fahimtar cewa tashe-tashen hankulan jarabawa ce daga Ubangiji. Suna faruwa ne sakamakon gurɓacewar halayyar mutane. Kai tsaye sukan danganta shi da ayyukan tsafe-tsafe da ake gudanarwa, musamman waɗanda suka shafi wasa da Alƙur’ani mai tsarki.[19]

Lokacin da tashe-tashen hankulan suka yi tsamari musamman daga wajajen 2016, mazauna wasu ƙauyuka sun yi gudun hijira zuwa garuruwan da ke kusa da su. Daga nan ne kuma labaran tashe-tashen hankulan suka mamaye duniyar intanet. Hotuna da bidiyoyi da rubutattun labarai game da su, duk suka mamaye kafafen sada zumunta. Ibrahim, (2019) a hirar da aka yi da shi ya tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka yi gudun hijira na da yawa sosai. Ya ce:

Wasu daga cikinsu sun samu taimako daga mutanen gari. Wasu sun ɗauki haya. Wasu kuwa sun zauna a cikin makarantu. Wasu kuma an ba su wurare aro sun zauna. (Ibrahim, 2019)

Hukumomi sun yi ta bin hanyoyi daban-daban domin shawo kan lamarin. Daga cikin har da ƙoƙarin neman sulhu da ƙusoshin tashe-tashen hankulan. A wajajen ƙarshen 2019 zuwa farkon 2020 ne aka samu sulhun da ya kai ga raguwar tashe-tashen hankulan. Sulhun ya kasance wani yunƙurin samar da zaman lafiya na gwamnatin da aka zaɓa a shekarar 2019.

3.0 Gurbin Kafafen Sada Zumunta a Tashe-Tashen Hankulan Zamfara

Kafafen sada zumunta suna taka rawa iri biyu dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. A ɓangare guda suna taimakawa ta wasu fuskoki da suka shafi faɗakar da jama’a dangane da abubuwan da ke faruwa tare da miƙa ƙoƙon bara na neman addu’o’i daga al’ummu na kusa da na nesa, da makamantansu. A ɗaya ɓangaren kuma, kafafen sada zumuntar suna ƙara wa wuta karmami. Sukan yi hakan ta fuskar ruruta zance da yaɗa jita-jitan ƙarya da cusa tsoro a zukatan mutane.

A gaskiya tasirin kafafen sada zumunta game da tashe-tashen hankulan zamfara nau’i biyu ne. Suna amfanarwa a gefe guda. A gefe guda kuwa cutarwa suke yi...[20] (Maikwari, 2019)

A taƙaice dai, kafafen na sada zumunta sun zama hanjin jimana, wato akwai na ci akwai na zubarwa. An raba rawar da kafafen sada zumuntar ke takawa dangane da tashe-tashen hankula a Zamfara zuwa manyan rukune biyar kamar haka:

Jad. 1: Manyan Nau’ukan Tasirin Kafafen Sada Zumunta a Kan Tashe-Tashen Hankula a Zamfara

 

Masu Kyau

Marasa Kyau

1.       

Faɗakarwa

Ta da Hankali

2.       

Ƙoƙon Bara

Yaɗa Ayyukan Ta’addanci

3.       

Bunƙasa Adabi

 

3.1 Faɗakarwa

Faɗakarwa kalma ce mai kinin ma’ana da nusarwa ko nusatanwa ko tunatarwa. Bunza, (2013: 2) ya ba da ma’anar wannan kalma da cewa: “Faɗakarwa hanya ce ta ilmantar da mutane ko yi musu nasiha da tunatar da su don jan hankalinsu kan wani abu muhimmi na rayuwarsu.”[21] Kafafen sada zumunta na faɗakar da al’ummomi na kusa da na nesa dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara ta fuskoki kamar haka:

i.                    Bayanai dangane da abubuwan da ke faruwa a daidai wata rana sannan daidai wani lokaci na saurin watsuwa ta kafafen sada zumunta. Wannan na taimaka wa al’umma wajen guje wa faɗawa yankunan da abin ya shafa.[22]

ii.                  Ana tura nau’ukan faɗakarwa daban-daban na yadda mutane za su guje wa faɗawa cikin tarkon waɗannan masu ta da hankula. Wannan ya shafi labarai na yadda wasu suka faɗa tarkon masu ta da hankulan, wanda hakan na matsayin hannunka mai sanda da darasi ga mai karanta labarin. Ko da ma dai an ce, “Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.” Wasu lokuta kuma kai tsaye ake kawo bayanai kan abubuwa da ya kamata mutane su kiyaye.

iii.               Akwai faɗakarwa da ta shafi jan hankali al’umma musamman matasa daga nisanta kansu daga ire-iren waɗannan tashe-tashen hankula. Wannan na iya kasancewa ta fuskar wa’azantarwa da nuna illolin shiga cikin ire-iren ayyukan.

3.2 Ƙoƙon Bara

Ƙoƙon bara salon magana ne da ke ɗaukar ma’anar miƙa koke domin neman wani biyan buƙata.[23] Masana da marubuta daban-daban sun yi rubuce-rubuce kan bara musamman a ƙasar Hausa. Wasu daga cikinsu sun haɗa da Karofi, (1980) da Bashir, (1991) da Sarkin Gulbi, (2007).[24] Ƙoƙon bara a wannan bincike na nufin kai koke da zimmar neman agaji.

Rubuce-rubuce da ake ɗorawa dangane da halin da al’umma kan shiga a lokacin tashe-tashen hankulan na zaman ƙoƙon bara. Mutanen da ke cin kare da rubuce-rubucen (da ma maganganu da ake turawa ta odiyo), a ƙalla sukan taimaka da addu’a. A wasu lokutan kuwa, ire-iren rubucen na jefa ɗimbin tausayi a zukatan al’umma. Wannan ya sa masu gudun hijira daga cikin waɗanda abin ya shafa sukan samu tallafi a garuruwa da ƙauyukan da suka yi hijirar zuwa gare su. Nau’ukan tallafin da suke samu sun haɗa da:

i.                    Matsuguni

ii.                  Abinci

iii.               Tufafi

iv.               Kuɗi

v.                  Abubuwan buƙatun yau da kullum kamar sabulu da omo da makamantansu.

Hoto 1: Rubutaccen Labarin Tashe-Tashen Hankulan Jihar Zamfara da kan Waz’af

Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara

Madogara: An ɗauko wannan hoto daga Whatsapp ranar 29 ga watan Disemba, shekarar 2019.

A wajajen watan Disemba na shekarar 2018, na kasance ganau ba jiyau ba dangane da wannan lamari. A unguwar Sabon Gari da ke Damɓa a Gusau ta Jahar Zamfara, akwai mutane kimanin 18 da suka taso daga ƙauye bayan zaman can ya masu tsauri. Mafi yawansu mata ne da ƙananan yara. Ɗaya daga cikinsu ta san wani dattijo a nan Damɓa. A bisa haka, sai suka tare gidansa. Dattijon mai ƙaramin ƙarfi ne matuƙa. Bisa wannan dalili, sai ya garzaya masallacin da ke kusa da su ya kai kukansa. Al’ummar wannan masallacin ne ta ɗauki nauyin ci da shansu har ranar da suka bar Damɓa. A kullum liman na neman taimakon kuɗin abincinsu na wannan rana. Mu kuma mamu mu bayar.[25]

A hirar da aka yi da Ibrahim, (2019) da Maikwari, (2019) an samu bayanai dangane da wuraren da ‘yan gudun hijira suka zauna. A yayin zaman nasu, sun samu tallafi da kulawar jama’a. Wasu daga cikin wuraren su ne:

i.                    Makarantun gwamnati musaman firamare da sakandare na je-ka-ka-dawo[26]

ii.                  Sakateriyoyin wasu ƙananan hukumomi[27]

iii.               Shaguna da rumfuna a kasuwanni

iv.               Tashoshi

v.                  Gidajen jama’a

vi.               Masallatai

3.3 Bunƙasa Adabi

Wani abin jan hankali dangane da adabi shi ne, ba sai yanayin lumana ko yadda zuciya ke so ke samar masa abinci ba. A maimakon haka, sau da dama mummunan yanayi ko ƙunci ko tashin hankali ko dai wasu abubuwa na ƙi na samar da tubalan ginin sabbin falsafofi a duniyar adabi. Tashe-tashen hankulan Jahar Zamfara sun taka rawar gani wajen samar da ƙirƙire-ƙirƙiren adabi da suka haɗa da waƙoƙi da karuruwan magana musamman na zamani.[28]

Jad. 2: Waƙoƙi da Aka Samu a Sakamakon Tashe-Tashen Hankulan Jahar Zamfara

Sunan Waƙa

Mawaƙi

Nau’in Waƙa

Bazamfariya

Dr. Aliyu U. Tilde

Rubutacciya

Waƙar Kidnafas[29]

Abdulhamid M. Sani

Rubutacciya

Yau ga Allah Muka Koma

 

Waƙar Zamani[30]

Zamfara Babu Lafiya

Sagir Yusuf

Rubutacciya

Haƙiƙa waɗannan waƙoƙi sun kasance ci gaba ga adabin Hausa musamman ɓangaren waƙa. Ko baya ga haka, sun taimaka wajen jawo hankalin al’umma musamman domin dogewa bisa addu’o’i da gyara halaye da zamantakewa, duk dai domin samun sauƙin lamarin.

Jad. 3: Sabbin Karuruwan Magana da Aka Samu a Sakamakon Tashe-Tashen Hankulan Jahar Zamfara

Sabuwar Karin Magana

Tsohuwar Karin Magana

Ba da ni ba, neman aure a Ɗansadau

Ba da ni ba gaɗa a maƙabarta/hurumi

Ba kanta, an sace mai garin Ɗansadau

 

Ana Maiduguri sai ga Zamfara

Ana kukan targaɗe sai ga karaya

Ana Boko Haram sai ga kidnafas

Ana kukan targaɗe sai ga karaya

Ritaya sa! An tura ɗansanda dejin Ɗansadau

 

Duk kun raba mini hankali, an ce da ɗansanda ya baro Borno ka koma Ɗansadau

Duk kun raba mini hankali, an ce da rago sha hura ka tafi gona

Ta nan muka fara, ɗan Borno ya ga Bazamfare

Ta nan muka fara, kuturu ya ga mai ƙyasfi

Madogara: Hirarraki[31]

A jadawali na uku da ke sama, an ga jerin misalan karuruwan magana da suka samu sakamakon tashe-tashen hankulan a jahar Zamfara. Wasu daga cikin an yi amfani da tsoffin karuruwan magana ne wajen samar da su. Wato an kwaikwayi falsafar da ke cikin tsoffin karin maganar ne domin ƙirƙira su.

3.4 Ta da Hankali

A cikin wannan bincike, ta da hankali na nufin jefa tsoro ko firgici ga zukatan al’umma. Binciken ya gano cewa, ɗaya daga cikin illolin kafafen sada zumunta dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara shi ne jefa tsoro da zaman ɗar-ɗar a zukatan al’umma na kusa da na nesa. Abin lura a an shi ne, kafafen watsa labarai sukan tace sahihancin labari kafin fitar da shi. Ko bayan nan ma, sukan ba da labarai ta salo da sigar da ba za su kasance masu ta da hankalin al’umma ba.

A bangare guda kuwa, labaran da ake yawo da su ta kafafen sada zumunta ba tatattu ba ne. Wasu ma na ƙarya ne. Wasu lokutan jita-jita ce ma tsura ake rurutawa. Saboda haka, labaran da ke fita daga kafafen sada zumunta sun fi muni da ta da hankali.[32] Wannan rashin kwanciyar hankali ga masu karanta labaran na faruwa ta fuskoki da dama. A ƙasa an kawo misalan wasu daga cikin hotuna da aka ci karo da su waɗanda za su iya ta da hankulan masu gani.

Hoto 2: Hoto Mai ta da Hankali da aka Ɗola a Fesbuk

Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara

Madogara: An ɗauko wannan hoto daga Fesbuk.[33]

A hirar da aka yi da malaman makarantar da ake ikirarin wannan abu ya faru, sun bayyana cewa labarin ba haka yake ba. Abu makamancin haka ya faru, amma ba yadda aka kawo labarin ba. An kawo wannan labari a Fesbuk cikin sigar da zai iya janyo ƙiyayya da rikici irin na addini. Ko bayan haka, hoton kansa ya kasance mai ta da hankali

Hoto 3: Gawarwarki da yawa da aka jejjera su cikin rami gudaZamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara

Hoto 4: Hotunan gawarwaki a kwakkwance

Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar ZamfaraA hirar da aka yi da Maikwari, (2019) ya bayyana cewa:

A yanzu haka akwai guruf-guruf da aka buɗe a kafafen sada zumunta musamman Whatsapp waɗanda suke yaɗa farfagandar ƙarya sakamakon ƙin jinin gwamnati mai ci da suke yi. Kullum sukan ƙago labaran da ke nuna ana samun daɗuwar tashe-tashen hankula. Yayin da aka bincika, wani lokaci sai a tarar sunayen ƙauyukan da suka zayyana babu su kwata-kwata ma a jahar Zamfara. (Maikwari, 2019)

Idan kuwa haka ne, lallai matsalar ta kai inda ta kai. Dole ne kuma gwamnati da sauran hukumomi waɗanda abin ya shafa su tashi tsaye domin daidaita sahun amfani da kafafen sada zumunta.

3.5 Yaɗa Ayyukan Ta’addanci

A duk lokacin da mutane (musamman yara) ke kallon ayyukan ta’addanci, zuciyarsu tana ƙara bushewa ne da ƙeƙashewa. Sannu a hankali tausayin da suke ji zai riƙa raguwa. Za a kai gacin da kwata-kwata nau’ukan ta’addancin ba sa wani tasiri irin na sanya tausayi ko jin ƙai a zukatansu.

A ɓangare guda kuwa, yana koya wa yara hanyoyin aikata rashin gaskiya daban-daban. Daga cikin nau’ukan abubuwan da ke ƙunshe a kafafen sada zumunta waɗanda kuma ke da alaƙa da ta’addanci akwai:

i.                    Hotuna da bidiyoyi da labarai a kan makamai da yadda ake sarrafa su.

ii.                  Hotuna da bidiyoyi na makamai da yadda ake safarar su.

iii.               Hotuna da bidiyoyi da labaran kashe-kashe.

iv.               Hotuna da bidiyoyi da labarai game da ayyukan ta’addanci da aka aikata irin su fashi da makami da sata da garkuwa da mutane da makamantansu.

A ƙasa an kawo ‘yan misalai waɗanda aka tattaro daga kafafen sada zumunta.

Hoto 5: Bindigogi da Alburusai a Fesbuk

Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara

Madogara: An ɗauko wannan hoto ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.

A hoto na 5 da ke sama, za a ga hoton bindigogi da kuma alburusai. A ƙasar Hausa an saba ganin yadda yara ke kwaikwayon wasa da bindigogi waɗanda suke haɗawa da kara ko ‘yan itatuwa. Masu wayo daga cikinsu suna amfani da fayif da ƙaramin katako ko falanki da ashana domin yin bindigar wasa wadda take ƙara. Duka waɗanan na faruwa ne sakamakon kallace-kallacen hotuna da bidiyoyin nau’ukan bindigogin da kuma yadda ake sarrafa su. A bisa wannan dalilai, kai tsaye ire-iren hotunan nan na da tasiri a kan tarbiyya da falsafar yara masu tasowa.

Hoto 6: ‘Yan Bindiga na Shirin Kai Hari

Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashintashinar Zamfara

Madogara: An ɗauko wannan bidiyo ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.

An sanya wannan bidiyo ne da sunan ‘yan bindigar Jahar Zamfara ne ke shirin kai hari. Sai dai bincike ya nuna cewa, labarin ba gaskiya ba ne. Hasali ma, ba a Nijeriya aka ɗauki wannan bidiyo ba.

4.0 Sakamakon Bincike da Shawarwari

Tun wajajen shekarar 2008 aka fara samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a Jahar Zamfara. A lokacin bai yi ƙamari ba, domin bai wuce faɗa tsakanin zauna-gari-banza na unguwanni da kuma sace-sace ba. Ƙaruwar fashi da makami da satar shanu ya buɗe wani sabon babin tashe-tashen hankulan. A wajajen shekarar 2012 zuwa 2013 ne lamarin ya yi ƙamari sosai musamman bayan ƙaruwar garkuwa da mutane da kuma hare-hare da ‘yan bindiga ke kai wa ƙauyuka.

A ɓangare guda kuwa, wannan bincike ya gano cewa, kafafen sada zumunta sun kasance ruwa biyu dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. Kai tsaye alfanunsu sun haɗa da:

i.                    Faɗakar da al’umma domin su farga tare da guje wa faɗawa cikin tashe-tashen hankulan ta kowace fuska. Wannan ya haɗa da ɗaukar makami, ko kuma garaje da rayuwa wajen faɗawa cikin haɗarin tashe-tashen hankulan.

ii.                  Taimakawa wajen neman tallafin addu’o’in samun zaman lafiya da ma samun tallafi nau’uka daban-daban kamar yadda aka lissafa a ƙarƙashin 3.2 da ke sama.

iii.               Suna kuma taimakawa wajen bunƙasa adabin Hausawa musamman abin da ya shafi waƙoƙi da karuruwan magangannu.

A ɓangare guda kuwa, kafafen na sada zumunta suna da illolin da suka haɗa da:

i.                    Ta hanyarsu ne ake yaɗa jita-jita da labaran ƙarya marasa tushe. Wasu labaran na ƙara ruruta lamari tare da jefa ƙiyayya da gaba da rikicin addini da ƙabilanci a zukatan al’umma.

ii.                  Labarai da bidiyoyi da hotuna da ake sanyawa na sukan kasance masu ta da hankalin al’umma. Wannan na faruwa musamman da yake ba tacewa ake yi ba ballantana a yi tunanin waɗanda suka dace a sanya da waɗanda ba su dace ba.

 

Dangane da waɗannan, binciken an ba da shawarar cewa:

a.      Gwamnati ta tashi tsaye tare da fitar da wasu tsare-tsare da dokoki na musamman da za su lura da yadda ake tafiyar da al’amuran kafafen sada zumunta a Nijeriya. Wannan na iya kasancewa ta sigar samar da yarjejeniya ta musamman da kamfanonin da hukumomin da ke lura da kafafen sada zumuntar. Za a iya bin matakan rufe asusu da ma bin wasu hanyoyin hukunci na daban ga masu yaɗa labaran ƙarya, musamman waɗanda ke ta da hankula.

b.      Malaman addini da na makarantun boko su rinƙa faɗakarwa game da illolin yaɗa labaran ƙarya da ta da hankula da kuma jefa ƙiyayya tsakanin ‘yan ƙasa.

c.       A samu tarurrukan ƙara wa juna sani a matakai daban-daban da za a tattauna tare da samun gudummuwar malaman ilmi da manazarta game da hanyoyi da matakan da za a tunkari matsalar. Gwamnati a matakai daban-daban tare da haɗin guiwar makarantu (musamman jami’o’i) su jagoranci tafiyar.

5.0 Kammalawa

Tunanin Bahaushe na “kowane allazi da nasa amanu” na ƙunshe da ƙamshin gaskiya. Binciken nan ya ci karo da hakan yayin da ya ci karo da amfani da kuma illolin kafafen sada zumunta yayin da yake nazartar tasirin kafafen ga tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. Matsayin kafafen sada zumuntan sun kasance hanjin jimana, wato “akwai na ci, akwai na zubarwa.” Ya rage ga mahukunta da gwamnatoci da sauran waɗanda abin ya shafa, da su yi wata huɓɓasa domin amfanuwa da kyawawan manufofin kafafen, tare da samar da matakai da hanyoyin da za a zage tsirin illolinsu.

Manazarta

Baruah, T. D. (2012). Effectiveness of Social Media as a tool of communication and its potential for technology enabled connections: A micro-level study. In International Journal of Scientific and Research Publications. Volume 2, Issue 5, Pp. 1-10, ISSN 2250-3153.

Bashir, L. (1991). “Bara a Ƙasar Hausa.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Clement, J. (2019). Daily active users of WhatsApp Status 2019. Retrieved on 3rd January, 2020 from: https://www.statista.com/statistics/730306/whatsapp-status-dau/.

Jayasekara, A. H. D. (2015). Facebook users and undergraduates (Specially reference to Selected Universities in Sri Lanka ). In the International Journal of Scientific Research and Innovative Technology, Vol. 2, No. 5 , Pp. 78-85. ISSN: 2313-3759.

Karofi, D. S. (1980). “Mabarata: Tasirinsu da Gudummawarsu a Kan Adabin Hausa.” Kundin digiri na (nawa?) wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

Korkmaz, M., Celebi, N. & Yucel, A. S. (2014). Practical review of the place of social networks in our daily life and their effect on today’s youth. International Journal of Academic Research Part B; 6(1), Pp. 250-261. DOI: 10.7813/2075-4124.2014/6-1/B.35.

Owusu-Acheaw, M. & Larson, A. G. (2015). Use of Social Media and its Impact on Academic Performance of Tertiary Institution Students: A Study of Students of Koforidua Polytechnic, Ghana. In Journal of Education and Practice. Vol. 6, No. 6, 2015 ISSN 2222-1735 (Paper), ISSN 2222-288X (Online), Pp. 94-101.

Sarkin Gulbi, A. (2007). “Nazari Kan Al’adar Bara a Ƙasar Sakwkato. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jamiar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Siddiqui, S. & Singh, T. (2016).Social Media its Impact with Positive and Negative Aspects. In International Journal of Computer Applications Technology and Research. Vol. 5, Issue 2, Pp. 71 - 75, ISSN:- 2319–8656.

Umar, A. B. (2013). Waiwaye Adon Tafiya: Faɗakarwa a Cikin Ƙagaggun Labaran Hausa. An cirato ranar 28 ga watan Disamba, 2019 daga: https://www.amsoshi.com/ 2018/03/waiwaye-adon-tafiya-fadakarwa-cikin.html.                                                  

 

 

 

Kafafen Intanet da Aka Ziyarta

https://www.statista.com/statistics/273563/number-of-facebook-employees/

https://www.amsoshi.com/

 

Waɗanda Aka Yi Hira da Su

Suna

Wurin Zama

Sana’a

Ƙiyasin Shekaru

Almustapha, Aliyu

Gusau

Aikin Gwamnati

50 - 60

Aminu, Ibrahim

Gusau

 Aikin Kamfani

40 - 50

Ɗandare, Sa’adatu Umar

Kebbi

Sayar da atamfofi (Kasuwanci)

20 - 30

Gobir, Yakubu Aliyu (Ph. D)

Sakkwato

Koyarwa a jami’a

50 - 60

Hassan, Nasiru

Gusau

Koyarwa a sakandare

40 – 50

Ibrahim, Aliyu

Gusau

Aikin Gwamnati

50 - 60

Ibrahim, Faruk

Gusau

Kasuwancin man fetur da gas (Manajan gidan man fetur na Zayaz Resource)

30 - 40

Maikwari, Haruna Umar

Gusau

Koyarwa a kwaleji

30 - 40

Zulyadain, Muhammad

Kano

Kasuwancin tufafi da kayan kwalliya

20 - 30

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 


Rataye

Bazamfariya ta Dr. Aliyu U. Tilde

 


Ta’ala mun kira ka,

Gida Naija da Makka,

Na bene har na bukka,

Yakini babu shakka,

         Ga komi kai iyawa.

 

Ka shaida mun bara'a,

Ga duk wani mun yi a'a,

A saɓo ba mu ɗa'a,

Muna roƙonka sa'a,

         Gabanin mui cikawa.

 

Tsaro yau yai gazawa,

A Hausa da tausayawa,

A kullum ba lafawa,

Da yaɗon ɗan kabewa,

         Da sauri ba tsayawa.

 

A Zamfara anka fara,

Abin sanda da gora,

Ya ƙarfafa babu lura,

Da iska har da ƙura,

         Ya kai kan Sakkwatawa.

 

Ƙasar Gandi da Isa,

Da ke da natso da hirsa,

A yau an tashi rusa,

Ginin Usumanu ƙusa,

         Da Gwamna Bafarawa.

 

Suna nan yammacinmu,

A Birnin Gwari namu,

Zubairu yana kiranmu,

Mu kai ɗauki dukkanmu,

         Da sauri ba tsayawa.

 

Kasar Dikko ya jawo,

Ta'adda na ta yawo,

A ɗauke mutum a kawo,

Kuɗaɗe kan ya dawo,

         Ga dangi ba ragawa.

 

A Daura sunka sabka,

Magaji yana a garka,

Da ƙarfi sunka ɗauka,

Ya sa Sarki ya koka,

         A tashi a zam kulawa.

 

Bare hanyar Abuja,

Farin kaya da soja,

Da manya masu maja,

A tsorace babu ko ja,

         A jirgi za su zowa.

 

Muhammadu sai ka miƙe,

Ka ɗau ɗamara ka tamke,

Da R.P.G. da sulke,

Ta'adda duk ka banke,

         Ka himmata ba gazawa.

 

Nasiha ce na ba shi,

Da A'i uwargidan shi,

Su ɗau kibiya da mashi,

A kullum babu fashi,

         Ka dage gun matsawa.

 

Burutai kar ka zauna,

Ka ɗauki igwa ka auna,

Ga tungar masu ɓarna,

Ka watse duk ka ƙona,

         Su tuba su bar mayawa.

 

Sa'an nan ga Sadiƙu,

Yana ta jiran kiranku,

Ya ɗau jirgi ya bi ku,

Ya ba ku tsaro samanku,

         Da bom ba dakatawa.

 

Na bi ku ina kirari,

Ina baiti da sauri,

Kumama babu ƙwari,

Da daji ya yi ƙauri,

         Na kwanta ban ɗagawa.

 

Da malammai a baya,

Tsayayyu masu raya,

Dare duka ba ritaya,

Da farko har nihaya,

         Ijaba sui biɗowa.

 

Arewa ina kiranmu,

Mu taru a dunƙulenmu,

Mu nemi tsaron ƙasarmu,

Amana har da ilmu,

         Sana'a sai yabawa.

 

Talauci bai yi kyau ba,

Yana kawo musiba,

Da kunci ga anoba,

Da jari babu riba,

Kasa duk tai macewa.

 

Talauci in ya zauna,

Da kafirci da ɓarna,

Suna biye ba lumana,

Ɗabi’u duk su ƙona,

         Mutunci yai ficewa.

 

Ƙalau muke ko husuma,

A jaki ko a Homa,

Idan an ce mu koma,

Ka sa mu tuna da Kalma,

         Mu yi ta wajen cikawa.

 

Salamatun da tsira,

Ga Annabi sa ka ƙara,

Iyaye duk ka tara,

A haula har mu dara,

         Dawaman ba gushewa.

 

Da tammat zan tiƙe ta,

Bazamfariya kiran ta,

Watan azumi na yi ta,

Da fuska biyu gare ta,

         Wajen mai bincikawa.

 

Dr. Aliyu U. Tilde

19 May 2019

 

 

 

 

 

WAƘAR KIDNAFAS

 

Abddulhamid M. Sani

(Malumman Matazu)

 

Allah da sunanka nake farawa,

Kai kay yi loto kullum yake juyawa,

Kai ne ka raya Allahu kai ka matarwa,

Ka halicci fajir sannan kayo Mumnawa,

Zan so ku ji ni ya al'umarmu mutane.

 

Kafin na fara na yo salati farko,

Wurinsa Manzo Shalele da aka aiko,

Duk Annabawa shi ne ya zam cikamakko,

Sannan iyalai sahabihi nai anko,

Ban ƙin na sanya nagargaru a mutane.

 

Yau firgici ne ya mamaye yankinmu,

Tsoro a kullum daɗo yake jama'armu,

An sace mata an sace har yaranmu,

Masu kuɗinmu an sace sarakanmu,

Abin takaicin wai gwamnatin jama'a ne.

 

Cikin gidanka a zo a ɗau maka mata,

Koko ɗiyanka a bi su har makaranta,

Waninmu fasinja yana kan mota,

Yau al'umarmu muna cikin firgitta,

Halin ƙasarmu na garkuwa da mutane.

 

Sam baabu imani wurin kidifawa,

In sunka sata wasu waya suka yowa,

Kuɗi miliyya su ce abin fansowa,

Allah tsare mu kaidinsu mun roƙawa,

Su al'umar da ke garkuwa da mutane.

 

Wasu cikinmu in sun yi garkuwa das su,

Nau'i da nau'i azaba suke gunsu,

Duka da yunwa su gaggalabaita su,

Har izgilanci kidifawa ke yi gunsu,

Sharri gare su 'yan garkuwa da mutane.

 

 

Daji su ɗaure ruwa ya ƙare kansu,

Sanyi na hunturu a kai na wasunsu,

Can daga baya za su kira ikhwansu,

Kuɗi a kawo koko su hallaka su,

Wayyo ni wayyo wai gwamnatin jama'a ne!

 

Kare suke ci ba babbaka yankinmu,

Abin takaici wai shugaba kuma ɗanmu,

Mun raina himmar da ake wurin kare mu,

Wai sulhu za ai da masu kakkashe mu!

Anya hukuma aikinta kare mutane?

 

Abin takaici ne ƙwarai kui duba,

Wai a hakan ne ake faɗin ci gaba,

Ƙalubale ne gare mu wannan babba,

Dukkan musifa yaye mana Wahhaba,

Duk kar ka ware har garkuwa da mutane.

 

Ni sha'írin nan 'yar shawarata ga ta,

Wurin hukuma ni ma gudummuwata,

Tsayin daka ku yi don kare al'ummata,

Jami'an tsaronmu ciki da maha'inta,

Ku sanya lura cikinsu kun gaggane.

 

Bora da mowa kul kar ku wawware su,

In kun ka gano tabbas ku hukunta su,

Wurin hukuncin kul kar ku bambanta su,

'Yar shawarata ƙin garkuwa da mutane.

 

 

A sa idanu sosai ga infomansu,

Jami'an tsaro na sirri a alkinta su,

Dama cikakka a ba su sui aikinsu,

'Yan sanda soji a ba su duk ƙarfinsu,

Don daƙilewar 'yan garkuwa da mutane.

 

Mu 'yan ƙasa kau gare mu shawarata,

Aikin alkhairi mu yi mu nuna a yi ta,

Har addu'o'i mu rinƙa yi gun bauta,

Kamun ƙafa na duk matsalar Allah kyauta,

Babbar musifa ta garkuwa da mutane.

 

Ko ƙyas bayani in mun ji kar mu rufe ta,

Mu kai rahoto ga jami'ai su bahasta,

In mun yi wannan Allahu za ya tsayatta,

Allahu amsa duk matsalar ga ta kwanta,

Babbar musifa da ta damu dukka mutane.

 

Ashirin da biyu "Two thousand eighteen" yin ta,

A shekarar da "Musabbabi" ma nai ta,

Wata na Maris don ba ni son in manta,

A tsakkiyar da muke cikin firgitta,

Birni da ƙauye yin garkuwa da mutane.

 

Ni wanda nai ta Abdulhamid Malumma,

Abba ga Hafsat ni ne Uban Fatimma,

Jihar Katsina birninmu mai alfarma,

Garin Matazu a nan kuma nake zamma,

Allah taƙaita a daina kama Mutane.

 

A


LHAMDULILLAH

 [1] Allah wadaran mai tado ta,

 Da waɗanda suke daɗa jawota,

 Allah ka hane mu da tashin ta...

 (Abubakar Ladan Zariya, Waƙar Haɗin Kan Afirka)

[2] Wannan ba ya nuna cea ba za a samu wasu ƙabilu na daban bayan Hausawa ba. Abin da kawai ake nufi shi ne, mafi rinjayen alumma da aladu da cikar tarihi na garin duk na Hausa da Hausawa ne.

[3] Waɗannan sun haɗa da wayoyin salula da kwamfutoci da ababen hawa da makamai da makamantansu.

[4] Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na da wannan ra’ayi. Ya kafa hujja da cewa, duk yankin da mawaƙa da sauran masu zalaƙar harshe suka yawaita, to zai iya kasancewa tushen wannan harshe a tarihance. Ya bayyana haka a hirar da aka yi da shi a gidan rediyon FM Zamfara, a watan Oktoba, shekarar 2019.

[5] Wato ana ƙara tabbatar da bayanan da aka samu daga wani mutum ko wasu mutane ta hanyar tambayar wasu mutane na daban.

[6] A shekarar 2019, kafar intanet ɗin nan mai suna Sitatista da ke adana bayanai dangane da kafafen intanet ya fitar da ƙididdigar maaikatan Facebook. Ya bayyana cewa, a shekarar 2018, maaikatan sun kai dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya da biyar (25,105).

 

[7] Wasu daga cikin rubuce-rubucen sun haɗa da na Baruah, (2012) da Korkmaz, Celebe & Yucel, (2014) da OwusuAcheaw & Larson, (2015) da Siddiqui & Singh, (2016).

[8] Makarantun da suka fara amfani da kafar sun haɗa da Columbia da Yale da Stanford (Clement, 2019: 2).

[9] Kamfani ne da ya shahara wajen ayyukan fassara da tafintanci da bincike (da makamantansu) cikin harsuna da al’adun Afirka. Don ƙarin bayani, a duba https://www.amsoshidigitalservices.com/

[10] Shi ne ke da kamfanin Dayn’s Collection.

[11] Toh gaskiya yanzu kusan za a iya cewa kafar sadarwa ta zamo wani sashi na rayuwa. Kamar yadda muka sani cewa rayuwa yanzu ba za ta yiwu babu ita ba.” (Zulyadain, 2019)

[12] A lokacin babu tashe-tashen hankula da suka shafi garkuwa da mutane da salwantar rayuwa da dukiyoyi.

[13] An kira su ƙanana ne kasancewar ba sa cikin nau’ukan miyagun ayyuka da ke ta da hankalin al’umma da jan hankalin duniya (musamman idan ba su yawaita ba).

[14] Ya faɗi haka a hirar da aka yi da shi ranar Alhamis, 23 ga watan Fabarairu, shekara ta 2020 a ƙofar gidansa.

[15] A hirarraki da aka yi da su, duk sun tabbatar da wannan batu.

[16] Burtali na nufi hanyar da ake bi da dabbobi musamman zuwa kiwo. Takan kasance marar ciyawa saboda tattakawa da dabbobi ke yi yau da gobe.

[17][17] Ɗaya ɓangaren tushen tattalin arzikin nasu shi ne noma.

[18] Akwai albarkatun zinari a yankunan ƙananan hukumomin Maru da Zurmi da Maradun. An fi samun sa ƙaramar hukumar Maru, musamman yankin Ɗansadau.

[19] Daga kimanin shekarar 2017 zuwa 2019 an tsinci Alƙur’anai da aka jefa a masai kimanin kashi huɗu ko sama da haka.

[20] Daga cikin amfanin kafafen na sada zumunta da ya lissafo akwai: (i) Samar da bayanai da (ii) Neman addu’a daga al’umma da (iii) Neman agaji daga al’umma da kuma (iv) Sanar da duniya abin da ake ciki wanda hakan ke sanya gwamnati ƙara mayar da hankali kan lamarin. Ya kuma bayyana rashin alfanunsu da suka haɗa da: (i) Yaɗa labaran ƙarya da (ii) Ta da hankalin alumma,

[21] Za a iya samun ƙarin bayani dangane da maanar faɗakarwa cikin ayyukan Gusau, (2008) da Usman, (2008).

[22] Gobir, (2019) ya labarta yadda wata ‘yar uwarsa ta so kawo ziyara tare da halartar buki daga Adamawa zuwa Sakkwato. Yayin wannan tafiya, dole sai an wuce ta cikin jahar Zamfara. Kasancewar ta samu bayanai game da tashe-tashen hankulan, cikin sauƙi suka yanke shawarar rashin zuwanta shi ya fi kwanciyar hankali.

[23] An gina wannan salon magana daga ƙoƙon bara na ainihi wanda shi ne mai bara ke miƙawa domin karɓar abin sadaka.

[24] Sarkin Gulbi, (2007: 23) ya bayyana ma’anar bara da cewa: “... wata hanya ce ta roƙon jamaa da wasu mutane kan bi bisa waɗansu dalilai don neman abin da suka ci ko suka sha ko suka yi sutura ko ma suka ajiye don biyan wasu buƙatu na rayuwa.

[25] A wancan lokaci, babban abin da ya ba ni ƙarfin guiwa tare da karkata zuciyata wajen mayar da hankali kan wannan taimako shi ne labaran waɗannan tashe-tashen hankula da nake karantawa a waya. Duk da a cikin mamun akwai dattawa da suke ta’ammuli da rediyo, matasa irina na da yawa, waɗanda kuma wayoyin hannunmu su ke matsayin rediyonmu. A intanet muke samun labaran yau da kullum.

[26] Misali, Government Girls Secondary School Kotorkoshi da Government Day Secondary School Mada da sauransu.

[27] Misali, Sakateriyar ƙaramar hukumar Tsafe

[28] Karin maganar zamani shi ne nau’in karin maganar da ake ƙirƙira a zamanin yau. Mafiya yawancin ire-iren karuruwan maganar suna da tsoffin karuruwan magana makamantansu.

[29] A wasu baitukan waƙar, shairin ya ba da shawara ga hukuma da sauran alumma baki ɗaya dangane da yadda za a shawo matsalar waɗannan tashe-tashen hankula. Yana cewa:

Ni sha'írin nan 'yar shawarata ga ta,

Wurin hukuma ni ma gudummuwata,

Tsayin daka ku yi don kare al'ummata,

Jami'an tsaronmu ciki da maha'inta,

Ku sanya lura cikinsu kun gaggane.

 

Bora da mowa kul kar ku wawware su,

In kun ka gano tabbas ku hukunta su,

Wurin hukuncin kul kar ku bambanta su,

'Yar shawarata ƙin garkuwa da mutane.

 

A sa idanu sosai ga infomansu,

Jami'an tsaro na sirri a alkinta su,

Dama cikakka a ba su sui aikinsu,

'Yan sanda soji a ba su duk ƙarfinsu,

Don daƙilewar 'yan garkuwa da mutane.

 

Mu 'yan ƙasa kau gare mu shawarata,

Aikin alkhairi mu yi mu nuna a yi ta,

Har addu'o'i mu rinƙa yi gun bauta,

Kamun ƙafa na duk matsalar Allah kyauta,

Babbar musifa ta garkuwa da mutane.

 

Ko ƙyas bayani in mun ji kar mu rufe ta,

Mu kai rahoto ga jami'ai su bahasta,

In mun yi wannan Allahu za ya tsayatta,

Allahu amsa duk matsalar ga ta kwanta,

Babbar musifa da ta damu dukka mutane.

[30] A nan ana nufin waƙar da aka rera a situdiyo.

[31] An samu waɗannan bayanai sakamakon hirarraki da aka yi da Aminu, (2019), Almustapha, (2019) da Hassan, (2019).

[32] Babban misali a nan shi ne, ko da ayyukan ta’addanci kafefen watsa labarai za su nuna, sukan tabbatar da cewa sun kauce nuna wasu ɓangarororin. A kafafen sada zumunta kuwa, akan sanya kowane irin labari ko odiyo ko bidiyo. Sau da dama akan ci kawo da bidiyo na yadda ake yanka mutane ƙarara, ko kuma ake sassara su gunduwa-gunduwa. Akan samu lokuta da kamfanin Fesbuk ke bayyana wasu daga cikin bidiyoyi ko hotuna da ake ɗorawa a matsayin masu ta da hankali (violent). Wani lokaci har takan cire su. Misali, akwai bidiyon da aka ɗora ɗauke da bayani a sama (wanda wannan bincike ba zai kawo bayani ko bidiyon ba saboda dalilai na tsaro) inda wanda ya ɗora bidiyon da kansa yake nuna ba kowa zai iya kallo ba “Amma fa sai mai ƙarfin zuciya.

[34]An ɗauko shi ranar 29 ga watan 12, shekarar 2019. 

DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.011

Post a Comment

0 Comments