Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Zazzau Shehu Idirisu

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:

Allah ya riƙa ma ja ragama,

Farar aniya farar atamfa,

Shehu Idirisu mai Zazzau mai sonka ba za ya jikkata ba.

 

Mafarin lammuran ALA Allahu abin riƙo a tsaro,

Tsani na hawa tsanin ALA Allahu abin riƙo alaro,

Mai ba ni tsumi da dabaru sam ba ni tsumi da ‘yan dabaro,

Allahu madogaran ALA don haka ba za ni jikkata.

 

 

Sannan na ƙwaƙume shugaba jakadan Rabba ja mu gaba,

Al abdu balaraben asali mai bin sa ba za ya kuskura ba,

Na gai da sahabu har ahali da tabi’u tabi’una gaba,

In nai haka baitukan ALA ko kaɗan ba za su taskata ba.

 

Zan zana fagen sanin ilimi ba zan tauye ɗigo ɗaya ba,

Ku ji shi tarai-tarai ilimi don shehu ba ai iri nasa ba,

Ya san ilimi na addini baƙu da faru duka ku zuba,

Zan zayyana illimin boko fagen da ba a ɗaran masa ba.

 

A Zariya City Ƙur’anic School ya fara farawa,

Sannan ya yi firamare a birnin Zariya komawa,

Zariya Model School sakandari ya ɗorawa,

Sannan ya wuce Training School a Katsina ban daɗa muku ba.

 

ABU Zariya daga nan ya zarce ba nawa da ƙwafa,

Institute of Administration ya yi kuma ya zurfafa,

A nan ya yi diggirin farko da na biyu babu ɗaga ƙafa,

State Deɓelopment Center Kaduna Training  ya ci gaba.

 


 

 

A ƙarshe ya shige Osteralia don ci gaba shugaba,

A can yai Public Admin sanin haƙƙin shugaba,

Can ya zamo gangara da a yau nake yi wa tambura na yaba,

Wajen eɗperience malam da ka ji ka ce masa shugaba.

 

Ya koyar a firamare har ya kai hedimasta uba,

Sai Zariya Natiɓe Authoritiɓe  yai ma’aji na gaba,

Sannan kuma ya yi sakatare na sarkin Zariyanmu uba,

Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu abin bugu na gaba.

 

Sai dai kawai fa na zahirta a kan eɗperience ɗin gaba,

Yai Ɗanmadami nan zazzau hakimin Zariya a gaba,

Sannan ya sarauci duk Zazzau ya zam sarki uwa da uba.

Alif da ɗari tara saba’in da biyar ban da ɗa mai kuba.

 

Am mar digiri na girmamawa a Jos da Mina uban tafiya,

Amirul hajji dukka ƙasa an ba shi a baya Nijeriya,

An ba shi award na CFR a gwamnattance don ku jiya,

Kai ba shi faɗu award ɗinsa a waƙen nan da na tattara.

 

Dundu mai ta da zaunanne gun masu takaffuri da isa,

Mari mai zauna ɗa na tsaye gun masu gwaji da sanya a sa,

Kai ga fage na sarakoki zaki na saraki ba wasa.

 

Da an buga jiniya malam gwamna ko uba na ƙasa,

Da an buga bigilan malam sojoji za su basasa,

Da an buga tambura ku tafi sarki ne babu sa-in-sa,

Yau na buga tamburan Zazzau ALA ne ba wani nasa ba.

 

Da an buga bigilan malam sojoji za su basasa,

Da an buga jiniya malam gwamna ne ko uba na ƙasa,

Da an buga tambura mu tafi sarki ne babu sa-in-sa,

Yau na buga tamburan Zazzau ALA ne ba wani nasa ba.

 

 

 

Kai mai tallar maɗi kauce ga mai tallar zuma a gaba,

Idan wani ya kasa a saya idan wani ya yi ba haka ba,

Tsuntsu sunansu ne fa guda kukansu daban ku dudduba,

Ku lura da baitukan ALA kar ku yi tsuru ina ta zuba.

 

Ku lura da baitukan ALA kar ku yi tsuru ina ta zuba,

Tsuntsu sunansu ne fa guda kukansu daban ku dudduba,

Idan wani ya kasa a saya idan wani ya yi ba haka ba,

Kai mai tallen maɗi kauce ga mai tallar zuma a gaba.

 

Allah ka are ni numfashi na yi alkawari na ida shi,

Zubin waƙa kamar dashi arewa kakaf na ida shi,

Dukansu saraki ba ƙyashi kowansu in tsara gaida shi,

Yau na nufi nahiyar Zazzau sarkin da ba ai iri nasa ba.

 

Du wanda ya sa Ilahu gaba aikinsa ba za ya munana ba,

Na ambaci mai isa da nufi kun san ba zan ƙasar guiwa ba,

Yau zan yi yabon uban tafiya ka ja mu ka kai mu ba fargaba,

Bangon lasa a gun bayi mai bin ka ba za ya cim maka ba.

 

Jifa mai tarwatse taro taron maƙiya da mai gaba,

Girgije alamun zuba na ruwa mai kakaki da alkabba,

Cida saka waiwayen kurma mai sa gurgu gudu da gaba,

Jirgin sama wanda kau wa watsari ya san ka ko ba zai furta ba.

 

Jirgin sama wanda kau wa watsari ya san ka ko ba zai furta ba,

Cida saka waiwayen kurma mai sa gurgu gudu da gaba,

Jifa mai tarwatse taro taron maƙiya da mai gaba,

Girgije alamun zuba na ruwa mai kakaki da alkabba.

 

Ga rana mai rabon aiki gurin na gari da mai zamba,

Horon aiki na jaki ne horon tafiya amale uba,

Horo na gudu barewa ce mai bin ta ba za ya cim mata ba,

Dutse a dira ka ba daɗi a faɗa ba a kuɓɓuta ba.

 

 

 

Dutse a dira ka ba daɗi a faɗa ba a kuɓɓuta ba,

Horo na gudu barewa ce mai bin ta ba za ya cim mata ba,

Horon aiki na jaki ne horon tafiya amale uba,

Ga rana mai rabon aiki gurin na gari da mai zamba.

 

Ka ji waƙa hannun riƙa ta bara daban ta banna daban,

Baitoji babu harigu don ka san za ka ji su daban,

Don babu kwata a harshena kalmomina ka ji su daban,

Allah alhamdu na gode ba alfahari nake masu ba.

 

Ala na Kano garin Dabo da Zariya can garin dagaci,

Kano can ne mahaifata matata ko garin dagaci,

Domin haka Zariya da Kano garina ne ku bai ƙunci,

Allah nai godiya gun ka albarka ba ka ƙire mini ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments