Ticker

6/recent/ticker-posts

Auren Dole

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Auren so mai sa a yi soyayya,

Auren so mai sa a yi soyayya.


Tushen waƙar ne auren dole,

Don da yawa an sa mata lalle,

Auren tilas an kai mu su dole,

Wannan ya sa sun faɗɗare hanyoyi.


Kai Baba mai yin auren dole,

Koko Uwa mai son auren dole,

Kar kuc ce zan yo zuƙi ta malle,

Ku ne tushen rushe soyayya.


Na rantse Allah yai mana ‘yanci,

Yin aure shi ne babban ‘yanci,

Auren so mai sada zumunci,

Mai sawa a nuna karamci,

Tsantsar so so sai da aminci,

Allah kar ka sha mu da soyayya.


Shi ne tushen yawon ragaita,

Ga zawara sun fi a lasafta,

Wagga masifa ku kun ka biɗo ta,

Da son rai mai sawa a ji kunya.


Auren tilas aikin banza ne,

Ko an ɗaura tarkon ɓarna ne,

Allah ma bai ce ay yi ba dole,

Sanadin komai shi ne soyayya.
Ala silken duk mai soyayya,

Ala tirken mai yin soyayya,

Sannan gatan mai yin soyayya,

Mai kyauta domin ai soyayya,

Mai alfarma domin soyayya,

Komai ALA zai yi da soyayya.


Auren tilas tushen tarbiyya,

Sanadin lalacewar ‘yan baya,

Turbar warware tufkar baya,

Mai yi ya ci amanar soyayya.


Ala ba ya son auren dole,

Mu ma ba ma son auren dole,

Wai waye ke son auren dole?

Wa ke fatan ay yi masa dole?

Allah kai ka tare gunmu da dole,

Tilas mai sassaƙaya soyayya.


Tabbas ba na son auren dole,

Ba na son mai son auren dole,

Ni limamin ƙin auren dole,

Tilas sai dai ay yi da soyayya.


Allah ba ya son auren dole,

Annabi ba ya son auren dole,

Ni ma ba na son auren dole,

Komai za ai ay yi da soyayya.


Mu ne kotun ƙolin soyayya,

Alƙalan alƙalan soyayya,

Majilisar ɗinke soyayya,

Hujjarmu ƙarfinmu da soyayya,

Ba ma son komai sai soyayya,

Allahna bayanmu da soyayya.


‘Yanmata wanda a ka wa dole,

Mu ne kotun ƙin auren dole,

Yi haƙuri kar kit tafi shargalle,

Allahna bayanmu da soyayya.

Auren Dole- Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)


Post a Comment

0 Comments