Ticker

6/recent/ticker-posts

8.1 Momi Ummina - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 389)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:  Ummi yee, ummi momina,

Ummi yee, ummi momina.

 

Share hawaye ki dena kuka uwa ma ba ‘ya mama,

Share hawaye ki dena kuka momi ummina.

 

Rayuwa a duniya abar tsoro ce ummina,

Kyakkyawar assali hawaiwai sa tso ummina,

Labarin hankali sai a dubi kamala ummina,

Labarin nittsuwa a dubi natiya ummina,

Halayyar ɗan Adam naƙaltar hali ummina,

Labarin soyayya tana ga iyaye ummina.

 

Ummi yee, ummi momina,

Ummi yee, ummi momina.

Share hawaye ki daina kuka ummi momina,

Labarin duniya a je ga fatake dangina,

Labarin zuciya sai a tambayi fuska dangina,

Labarin kududdufi a je ga agwagwa dangina,

Ai hulɗar arziki da tunanin kirki dangina,

Labarin ƙuruciya a je gun yara dangina.

 

Farin ciki mai sa a yi kuka da hawaye,

Farar uwa alfarmar renon ‘ya’yaye,

Nishaɗuwa mai sa a ji kukan tsuntsaye,

Adon gani ai ado da tagullar hannaye,

Farin dare mai sanya zumuɗin angwaye.

 

Baƙin hali mai sa a yi bore tawaye,

Baƙin ciki sa ‘ya’ya mata su yi maye,

Baƙar uwa mai sanya takaici da hawaye,

Baƙin dare alfarma ce gun kuraye,

Baƙin naɗi mai ɓoye kamannin Buzaye.

 

Maza share hawaye ki daina kuka momi ummina,

Cuta yau gobe cuta ba mutuwa ba ummina,

Cuta mai warraka ta zamo kaffara ummina,

Cuta mara magani ac cika da sa’ada momina,

Kyakkyawan tanadi ke ƙarkon ƙarshe momina,

Allah ya sa a cika da imani da salama momina.

 

Burina addu’a gami da biyayya mai haiwa,

Haƙuri da ki kai da ni ni Aminu ba zan manta ba,

Rainon da ki kai mana ba zai yo ac ce mun rama ba,

Addu’ar da kike mani ba za fa ta faɗi a ƙasa ba,

Allah ya biya maki da ƙarkon ƙarshe da na raiwa,

Share hawaye ki daina kuka ba farau ne ba.

 

Tsakar dare rigar sanyawar mugaye,

Wutar ciki mai sanya nadama da tsumaye,

Azarɓaɓi mai sa katsalandan kai waye,

Dirin cida mai sanya kurame waiwaye,

Hassada mai kore nagartar kowaye.

 

Ragon amo waƙa da ɗabi’ar ɓeraye,

Ragon salo waƙe da salon ‘yan nanaye,

Ragon maza goga mai dukan mataye,

Abin gudu malam da ɗabi’un bokaye,

Ruwan dare guɗa a gidajen angwaye.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments