Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Na godewa Allah,
Dan baiwa Jallallah.
Kyauta gun Allah fa ba ya zobe,
Kyauta gun Allah fa ba ya zobe.
Al amarin Allah a kan ƙadara ne,
Shi fa ya so Allah yai min zane,
Yai baiwar hikima in waƙe mutane,
Faɗakarwa don a ɗan gaggane.
Wanda ya san ALA silar waƙa ne,
Ga matsayin daraja silar waƙa ne,
Gado uban jama’a silar waƙar ne,
Ko ilimin Alan silar waƙa ne.
Waƙa ba gado na yo ba a ga ne,
Ni asalina ɗan gidan ilimi ne,
Yarena Hausa Bagobiri ne,
Ruwa biyu Hausa Fulani in an gane.
Idan aka ce ALA mawaƙi ni ne,
In a ka ce alkatibi ma ni ne,
Manazarci anka ce muku ni ne,
Fulani ki san wannan kufar illa ne.
In kuma laifina na waƙa ne,
Waƙa baiwa ce nufin Allah ne,
Sannan kyauta ce ga keɓaɓɓu ne,
Ba ni barin waƙa gare ku mutane.
Idan kuma laifina na halayya ne,
Ba na shan taba da wiwi gane,
Ba na alfasha ku ɗan gaggane,
Ba na masha’a idan an aune.
Idan kuma laifina a kan sana’a ne,
Ba na yin sata fa ba na sane,
Ba na jagora kan su mutane,
Balle in hau cin haƙi na mutane.
Fulani meye laifi da na yi a zane?
Tsai da biyar sallahna tsai da biyar ne,
Ga kalmar shaida ta imani,
Ga Musulunci ya haɗa mu a juni.
Idan ka zamo talaka a ce Allah ne,
A baki ana ta faɗin hakan bisa aune,
A zuci da aikace kuwa an bobbone,
Halin ɗan Adam abin dubi ne.
Dukkannin komai nufin Allah ne,
Har samu da rashi nufin Allah ne,
Tallauci da wadatuwa Allah ne,
In ka zamo Sarki a ce Allah ne.
Ba na ja shakka nufin Allah ne,
Kowa komai ya zama Allah ne,
Harƙar soyayya nufin Allah ne,
To haka ma auren nufin Allah ne.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.