Ticker

6/recent/ticker-posts

7.30 Nuhu Uba Kura - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 381)

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Na karkato garin Kura – Garin Kura,

In gaida Nuhu Uba Kura.

 

Uba – Uba – Uba – Uba,

In gaida Nuhu Uba Kura.

 

Na karkato garin Kura in gaida Nuhu Uba Kura.

 

Na karkato garin Kura,

In gaida Nuhu Uba Kura.

 

Na waiwayo garin Kura,

In gaida Nuhu Uba Kura.

 

Na karkato garin Kura,

In gaida Nuhu Uba Kura.

 

Allah wanda yai Kura a Kano,

Ka ƙara ba ni fikkira,

Kar na zama rago.

Ƙasaita tana garin Kura,

Albarka tana garin Kura,

Jarumta tana garin Kura,

Noma je ka garin Kura,

Aure je ka garin Kura,

Nai sha’awar zama garin Kura,

Ni dai ina fa son Kura,

Mai motar ga ya ƙure Kura,

Kayana su tadda ni Kura,

Nai zango a can garin Kura,

Albarkar Nuhu Uba Kura.

 

Basarake kake adala,

Kai yi irin salon Nuhu Uba.

 

Mai mulki ka tsaida mulki,

Da hali irin Nuhu Uba.

 

Ɗan siyasa ka yi siyasa,

Da ɗabi’ar Nuhu Uba.

 

Malami kake sai ka koyar,

Tausayi irin Nuhu Uba.

 

Ɗalibi kake kai yi ƙasa-ƙasa,

Haƙuri irin Nuhu Uba.

 

Alkhairinsa ba da an mai ba,

Kyauta bad a nuna ramko ba,

Zumunci fa ba da an mai ba,

Soyayyarsa ba da an mai ba.

 

Jagora Nuhu Uba Kura,

Haƙuri gun Nuhu Uba Kura,

Kyautayi gun Nuhu Uba Kura,

Tausayi ga Nuhu Uba Kura,

Yakana ga Nuhu Uba Kura,

Kai ƙana a garai Uba Kura.

 

Mun karkato garin Kura,

Mu gaida Nuhu Uba Kura.

 

Gamzaki Nuhu Uba,

Hamshaƙi Nuhu Uba,

Gogarma Nuhu Uba,

Ganjarma Nuhu Uba,

Jinjimi ka fice gaban bara.

 

Tafiya sannu-sannu sai Giwa,

Bajintar Kada tana a ruwa,

Gafara ga Giye mijin Giwa,

Mai kiwo ba fargaba a dawa,

Hanya babu ƙaya da gantsarwa,

Malam Nuhu Uba Kura.

 

Mun karkato garin Kura,

Mu gaida Nuhu Uba Kura.

 

Na gode Nuhu Uba Kura,

Ta gode Nuhu Uba Kura,

Mun gode Nuhu Uba Kura,

Sun gode Nuhu Uba Kura,

DPM Nuhu Uba Kura,

Gogarma naɗin garin Kura.

 

Garin Kura – Garin Kura – Garin Kura.

Na karkato garin Kura,

In gaida Nuhu uba Kura.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments