Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi:
Kibiya ta mai baka ta soken a zuciyata wayyo,
Sai dawurwura nake,
Na rasa inda za ni in saka kaina.
Allah Ƙadiran ALA manni tasha’u Rabbana Jallallah,
Mai ikon tasarrufin ruhina da jukunana Allah,
Yarda ya so a lammura kunfa yakunu za ya cewa Allah,
Allah na yi durÆ™uso lamura sun ta’azzara fa a kaina.
Na yi riƙo da Annabi tsantsar sonsa ta zamo tsanina,
Tsanina na É—aukaka kai har ma da warrakar ruhina,
Ƙauna ce da bibiyar ya Annabi ɗan Amina baban Nana,
Don tsantsar isarsa gagara koyo ka karɓi lamurana.
Cuta ta ci zuciya ta koma zuwa ga gaɓɓai ɗina,
Ciwo na nuƙurƙusa ta a cikin jiki har raina,
Ga cuta cikin jiki ba ikon kusurkusur da jikina,
Ba halin wutsirniya don susa na samu sassaucina.
Basir ya zigan jikina ya sanya zazzaɓi a jikina,
Ga mura ta saka idona ya zama kama da markar rana,
Shessheƙa nake ta yi babu dare maraice balle rana,
Ga ciwo a zuciya mai hana É—anÉ—ano a kan harshena.
Sannan ga ni na zamo matafiyi musafihi dangina,
Yanzu ina jahar Kano gobe Kaduna zan wuce dangina,
Jibi ina jaha ta Jos Bauchi nake nufin zuwa ba kwana,
Daga nan za na dawaya Adamawa da Gombe don burina.
Citta ina haƙon zuwa Lagos don na tallata hajata,
Daga nan sai na ya da zango a Abuja inda tarayyata,
Inna kwan biyu a nan sai kuma Sokoto garin babata,
Daga nan in yi Katsina birnin Dikko inda masoyana.
Barci ya fa ƙauracewa idanun Aminu Alan waƙa,
Ga auren tuna-tuni da ya sassarƙafe zukata saƙa,
Sai saƙa da warwara ba hutu cikin ƙwaƙwalwa haƙƙa,
Na yi gamo gamon rabo fuji’a anka manna har mai sona.
Duka in yai yawa na saman ka kawai ake karewa,
Na rasa É—anÉ—ano a kan harshena bare in zam mai sha’awa,
In ka gan ni sai ka ce yaro ƙarami dake shayarwa,
Lallashi na ake in ci abinci karna hallaka kaina.
Babu laka cikin jiki na yi kama da mai cikin shayarwa,
Koko ma in ce da kai na yi kama da mai layi donkwawa,
Na yi kama da guzuma da ta haifa ta kasa ma miƙewa,
Sai dawurwura nake na rasa inda za ni in saka kaina.
Adam Kirfi ne yace ALA ɗauki haƙurin dacewa,
Ala fauwala wa Allah Sarkin dake da ikon kowa,
Komai na duniya fararre kuma mai ƙarewa,
Ɗau haƙuri da dangana bar wa Rabbi lamura alhina.
Adam ca I ce da ni wai sulusin dare fa ba na barci,
Kai komo ya ce nake kakaci nake ta yi ba barci,
Ya ce sintiri nake kai ka ce mayuwancin kyarkeci,
Wai har inkiya nake sautina da hannuwa gyaÉ—a kaina.
Adam yai É—awainiya ALA babu sautukan godewa,
Adam Kirfi ke ta jewar tuƙa mu ba shi ba ƙosawa,
Kiwona kawai yake ba shi bari in durƙusa dankwawa,
Sannan addu’a yake da roÆ™o Ubangijin ruhina.
In na je ni jami’a jama’a nata zakwgwaÉ—i da ganina,
Har wani sowa suke har zanbarwa suke da zuwana,
Ni ko inata dariya har É—aga hannuwa nake dan kaina,
Amma can a zuciyata dawurwura take dangina.
Ko a fage gurin biki ko taro na mawaƙa dangina,
Kowa yai acan-acan mata nata kai da komo guna,
Indan ni fa dafa sai mateku su daina wankan rana,
Dan ni ba fa ji nake bakuma ma gani nake da idona.
Wai daÉ—i da arziki ka yi gida sannan da mota ta hawa,
Ka yi ado na kece reni ga sutura kalolin sawa,
Sannan ka zamo fa mai sawa a yi ko gida koko dawa,
Ala bai rashan guda da gajeren giyar abinda na zana.
DaÉ—i kwanciya ta hankula samuwar abin saraina,
Burin zuciya ta kai ga buƙatar abinda ta zayyana,
Mai ban so na zuciya zai yi dumu-dumu watan wata rana,
Zai kwana ya tashi tafkin danasani watan wata rana.
Na gode Ubangiji mai aiki da cutuka gun bayi,
Allah mai tajarribi na gode da jarrabawar da na yi,
Allah ta zama ni kaffara ta zunuban da na yi,
Komai ka yi Rabbana ba mai ce da kai muhim sarkina.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.