Ticker

6/recent/ticker-posts

Kalmar So

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Ba Kalmar so ke da wuyar faɗi ba,

Haƙiƙar so ke da wuyar rabewa.

 

Kalmar so na da wuyar rabewa Ala,

Nazarin so mai ruɗar da ƙwaƙwalwa Ala.

 

Harƙar so taka sannu a sannu Ala,

Fuji’ar so cira-cirye ta figa Ala.

 

Allahu ka zammana gani da jina,

Allahu ka zamma ni zaɓi a guna,

Zaɓin da kammun fa Ubangijina,

Duk yanda ka so ba ni da zaɓi sona.

 

Barcina makaho ba ka iya rabewa,

Mace da ciki Allah ne ke iya rabewa,

Saƙar zuci Allah ne ke saniwa,

Halaiyar ɗan Adam ba a iyawa.

 

 Harshen baki da shi ake tsarawa,

Da laɓɓan nan da su ake harbawa,

Su haɗu su ba da sautukan isarwa,

Da sigar nan gobe suke sauyawa.

 

Hannun karɓa da shi ake ƙwacewa,

Idan duba da shi ake ritsewa,

Kunnen nan dai da shi ake jiyowa,

Kazalika dai da shi ake bonewa.

 

Haƙoran nan da su ake darawa,

Haƙoran nan da su ake cizawa,

Zukatan da su ke farantatawa,

Zukatan yanzu sai fa ƙuntatawa.

 

 

Da kare da are gwanda kare fa baba,

Don ka ga kare bai rasa fa’ida ba,

Shi ka ga are bai rasa za’ida ba,

Da are da aradu ni ba zan rabewa.

 

Masonin lammari a nai da so ne,

A ƙarshensa ya birkice da ƙi ne,

Ka so mai son ka saise-saise gane,

Watan wataran a dawa za ku gane.

 

Duk wata cuta da shimfiɗar ta so ne,

Makidar ta ta zarce masu aune,

Dukkan zamba da shimfiɗar ta so ne,

Jalalarta ya zarce kalga ne ɗan uwa.

 

Mafi girman kaba’ira da zamba,

Mafi tsananin balahira ku duba,

Ku nutsu da kyau da so a kai turba,

Jalalar so ta zarce masu duba.

 

Komai ka nufa za ka iya shi baba,

Komai tsauri da gagararsa baba,

Dabba aljan an mallake su baba,

Amma ba dai halina ɗan Adam ba.

 

Ɗan Adam ne a zizziga shi,

Ka iske gobe-gobe ya tire shi,

Ana ga shi a yanzu-yanzu yashi,

Ya rikiɗe ya rasa inda za shi.

 

Gangar-gangar a ziga ka ga shi,

Tiryan-tiryan a gobe ba ka ba shi,

Lami-lami harka kuke a da shi,

Hannun riga kuke a gobe da shi.

 

Allah kenan mai sanya so da ƙauna,

Da kun juya ya zama so da ɓarna,

Kalaman so a da ku nai wa juna,

Su koma ƙi da muzgunawa juna.

 

Allah ga ka a yanzu ga ni ga su,

Allah ka san abin dake a ransu,

Allahu ka mai da sharrukaina mai su,

Raba mu da su irin na kalbisu.

 

Iska da ruwa mai sha’awar kaɗawa,

Curin hadari mai sha’awar ganowa,

Da taurari adon gani ga kowa,

Koren ganye abin ɗebe kewa.

 

Da kare da are gwanda kare fa baba,

Don ka ga kare bai wuce fa’ida ba,

Shi ka ga are bai wuce za’ida ba,

Da are da aradu ni bazan rabewa.

 

Dalilan so akwai yawan sabubbai,

Gurbin so akwai yawa ya dubbai,

Ku bi ni a sannu kar ku zo a bai-bai,

Zan zo da su in fasale su ɗai-bai.

 

Abin ɗoki ya zam abin soyewa,

Abin nema ya zam abin gujewa,

Abin marari ya zo da gundurarwa,

Da son kwaɗayi haka take zamowa.

 

Abin fahari ya zam abin kawarwa,

Abin ƙauna ya zam abu na yarwa,

Abu na lale ya zam abin kawarwa,

Da son sha’awa haka take zamowa.

 

Mu saurara ku bi ni ba gazawa,

In zo da batuna so abin rabewa,

Lura baya da tsakuwa rabewa,

Makkhon so ya kau ya zam dishewa.

 

Alan al’umma ɗan jahar Kanawa,

Ke saƙona hikima ga kowa,

Ba dan kushe da ɓata rai ga kowa,

Domin faɗaka da so hallakarwa.

 

Da kare da are gwanda kare fa baba,

Don ka ga kare bai wuce fa’ida ba,

Shi ka ga are bai wuce za’ida ba,

Da are da aradu ni bazan rabewa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments