Ticker

6/recent/ticker-posts

Makomar Arewa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Taro mukai na sanin makama,

Alƙibla makomar Arewa.

 

Allah muƙaddari bai hanawa,

Almuƙutaddiru mai sakawa,

Shi ne ya ƙagi kudu Arewa,

Ƙasa guda kudawa Arewa,

Na karkato bayanin Arewa.

 

Ɗan Abdu mai halin ambatawa,

Alih ta asahabu na sawa,

Haɗa da tabi’ai masu baiwa,

Kamun ƙafa nake da riƙewa,

Riƙo na shari’a ba ɓacewa.

 

Sanadi na yi waƙar Arewa,

Da ni aka yi taron Arewa,

ATE ai a ɗakin Arewa,

A Kaduna a zauren Arewa,

Tu o tuwelb idan na tunowa.

 

Taro a kai na manyan Arewa,

Sarakuna ma mulkan Arewa,

Da mai faɗi a ji a Arewa,

Da mai riƙon miƙami Arewa,

Da masu so da kishin Arewa.

 

 ATE ai ta tsara shiryawa,

Arewa transformation ta kowa,

Fomin initiatiɓe kowa,

A ƙarƙashinta ne muka zowa,

Don kau da mishkilolin Arewa.

 

 

 

Duk wanda ka sani ɗan Arewa,

Abin nufi wakilin Arewa,

Na duba hai tebul Arewa,

Ko zanga mai muƙamin Arewa,

Na dai ga Ɗan Masanin Kanawa.

 

Sai muttaƙa rabon Katsinawa,

Ciyaman na okeshin Arewa,

Sai kuma malaman jami’awa,

Kirista da Musulman Arewa,

Sai ɗalibai matasan Arewa.

 

An karanto muƙalun Arewa,

An karanta takardun jiyarwa,

Ni da Haruna Ningin Arewa,

Da Abubakar Sadiƙ Kanawa,

Da Abdu Boda ɗan Katsinawa.

 

Wani ya ce larurar Arewa,

A ƙara ƙarfafar ilimin ruwa,

Wani ya ce sana’un Arewa,

 A ƙarfafe su don haɓakowa,

Zai kau da matsalolin Arewa.

 

Wani ya ce bara a Arewa,

Almajirai na yankin Arewa,

Miliyan tara har da ɗarawa,

Shi ne barazanar ‘yan Arewa,

Rashin tsaro a yankin Arewa.

 

Sai Maitama Sule ko ya cewa,

Ɗan Masanin Kano na Kanawa,

Dastistalok shi ya killacewa,

Ya riƙa tufka har warwarewa,

Ga hikima ya gamsar da kowa.

 

 

A nan aka musaya ta baiwa,

A kai rabon takardu na kowa,

Musharakar tunanin Arewa,

Abin da ni ya juyan ƙwaƙwalwa,

Ya za a sada saƙo na kowa.

 

Batun da mun ka yo kan Arewa,

A aikace ake son isarwa,

An ce sani da ba aikatawa,

Kama da jakuna an azawa,

Kaya na littafan ilimarwa.

 

Sai ra’ayi na Alan Kanawa,

A kai na matsalolin Arewa,

Mu ne muka fi kowa da kowa,

Mafi yawa cikin talakawa,

Na ƙirƙira a lardin Arewa.

 

Mu ne muka fi kowa da kowa,

Rashin kulawa da ilimi Arewa,

Ga haihuwa da aure Arewa,

Ba ma kula da haƙƙin tarbiyarwa,

Sai lataƙirƙirar talakawa.

 

Mu ne muke da ƙasar haƙawa,

A shuka ɗan iri ya fitowa,

Mutum guda a yankin Arewa,

Ya mamaye ƙasa ya sayewa,

Ya saye gonakin talakawa.

 

Bai ba da hurumin aikatawa,

Bai noma ko haki ba kowa,

Ya zagaye katangar mayewa,

Irinsa sun fi irgar tusawa,

A nahiya ta lardin Arewa.

 

 

Mutum guda a sashen Arewa,

Yana da hurumin mallakewa,

Idan ya so fa zai mulki kowa,

Da hidima da tanyun Arewa,

Da ilimi da aikin taɓawa.

 

Yana matsalolin Arewa,

Rashi na so da kishin Arewa,

Waɗanda ke da halin Arewa,

Idan su kai kuɗi ‘yan Arewa,

Waje suke zuwa don ajewa.

 

Da ka aje a bankin Arewa,

Da sufa za a juya Arewa,

Ko kai gini na estet Arewa,

Koko ginin masaƙar Arewa,

Da ya zamo faragar Arewa.

 

Masu kuɗi na yankin Arewa,

Ku kaɗai fa kun ma yi yawa,

A gyara matsalolin Arewa,

Bare sarakuna na Arewa,

Su haɗa kai a gyaran Arewa.

 

Da Mallamai jumlar Arewa,

Da rabaran na yankin Arewa,

Da masu waƙe-waƙen Arewa,

Kowa ya ɗau gabarin sanarwa,

Kafin fa gobe mun zarce kowa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments