Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamaye

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Ado mai Kano mai martaba,

Ado ɗan Bayero mai martaba,

Na taya murna mai martaba,

Ka yi naɗin sardauna kamai.

 

Sarki Allah ƙara martaba

Mai Kano Allah kau da ja’iba,

Ɗan Abdu karimi shugaba,

San kano Sarki mai martaba,

Ado madubin Shugaba,

Sadauki marar fargaba,

Jimrau sa gabanka kai gaba,

Masallata limamu na gaba,

Mamu a shige sahun gaba,

Mai mota direba na gaba,

Fasinja ba a jira ka ba,

Ado in da duk ka sa gaba,

Masoyi ba zai ƙi bin ka ba,

Na taya murna mai martaba

Yayi naɗin Sardauna kamai

Mallam Sardauna kamai.

 

Allah Shi ka aram ma bawa mulki san da ya so Ubangiji,

San da ya so wanda ya so ga wanda ya so ba wani agaji,

Kullu Amrullahi Ƙadirun Maƙadurin kun ji ingiji,

Don haka wannan babu hassada wanda ya ja to zai karairaya.

 

Ka ƙara salati da amintaka ga Annabi bawan ka Balarabe,

Mahe Mahmudu Mahe wanda ya sa ƙarya mukarrabe,

Arabiyyun Ajamiyyun da Inyamuraru da Bayerabe,

Wanda da zakkowarsa duniya katangun kisra suka rairaye.

 

 

 

 

Taka sannu da kyau lafiya,

Ya Ɗan Bayero mai martaba.

 

Duƙa sannu da kyau da lafiya,

Ya ɗan mai asali da martaba.

 

Zauna sannu dakyau da lafiya,

Ya ɗan mai haƙuri da martaba.

 

Juya dama da kyau da lafiya,

Juya haunu ba sa tararka ba.

 

Ka zama sanɓargon sarakuna,

In dai ga ka ba za a gan su ba.

 

Kogi ka cinye kududdufa,

Ka wuce shinge mai datsar gaba.

 

Mallam in ka ji doka tambura,

Ko ka ji kakaki matso gaba.

 

Taso ga giwar sarakuna,

 Ado Bayero mai martaba.

 

Sarki na juyo da dundufa taya ka bikin murna na zo in yi,

Ka yi naɗin Sardauna kamai ne bisa tsari da kyauta yi,

An yi naɗin Sardauna Iro ne a kan cancanta da kyauta yi,

Ado Allah ƙara lafiya babbar giwa ko in ce gini.

 

Alan waƙa ke ta tambari domin ƙauna ba tanguwa,

Sarki cancantar ka ta isa in yi yabo ba sai da ilwa,

In yi kirari har da salsala jikan Dabo ba za na iji ba,

Ado Ɗan Bayero San Kano in har ga ka fa babu waiwaye.

 

Ka yi naɗin Sardauna a Kano Allah riƙa Mallam da martaba,

Sarki kai sara a kan gaɓa ka naɗa mai kishi na ci gaba,

Ka naɗa Gwarzo mai karisma mai haƙuri ƙauna ta ci gaba,

Mallam mai halin a kwaikwaya don haka ne na ƙira shi kamai.

 

 

Sai na tuno Sardauna Ahmadu mai kishin da ba ai kamarsa ba,

Sa Ahmadu gwani firimiya mulkin Arewa can shugaba,

Sa Ahmadu abin da kai mana har a naɗe ba a mantaka ba,

Roƙo na Allah Ubangiji halaiyarsa ka baiwa kamai.

 

Mai haƙuri mai son ci gaba mai kishi na Arewa can ƙasa,

Jajirtacce jarimin uba su suka samo ‘yancin ƙasa,

Sun mutu don kishin ƙasarmu ne an kakkashe mana jarimin ƙasa,

Fatana Allahu Rabbana Sardaunanmu ka sa shi yammai.

Mallam limamun San Kano Sardauna mun sallama maka,

Allah riƙa ma wagga daraja mu ba mu ja mun yaba maka,

Allah taya ka riƙo da ɗaukaka halayyarka ta sa a kai maka,

Tafi dai ɗoɗar a gwaddabe babu tsayawa babu waiwaye.

 

Sakayyar ƙauna akai maka ƙara nutsawa babu jirwaye,

Tarbiyarka face ta ja maka ƙara nutsawa babu kewaye,

Gogayyarka face ta ja maka ƙara izawa babu tirji,

Kamewarka da shi ya ja maka ƙara gaba ka dena waiwaye.

 

Manaɗa sarki suna maka bai’a sun ce eh Allah ƙara martaba,

Kingimeka suni nake nufi sun maka bai’a mai martaba,

‘Yan majalisar sarkin Kano sun yi mubai’a babu ja’iba,

Hakimai cikin jahar Kano sun yi mubai’a mai martaba,

Hakimai na kewayen Kano sun yi mubai’a mai martaba,

Bayin sarki na cikin gida miƙa wuya dai babu fargaba,

Fadawa na sarkin Kano sun yi mubai’a mai martaba,

Sarakunan Arewacin ƙasa sun yaba kyautar mai martaba,

Don haka ALA ya taƙarƙare yake baitin murnar da ci gaba,

Kowa ya bi a yankin Kano an naɗa Sardaunanmu kamai.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments