Ticker

6/recent/ticker-posts

Raba Gardama

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Mai raba gardama ɗan Sani jikan Abubakar ɗan Gwanki,

Alan al’umma me waƙa kishin al’umma kukanka,

Bambancin mutum fa da dabba,

Shi ne ilimi al’umma.

 

Allah Shi yac e mu yi bauta yas sa ilimi jigonta,

Ya yanke uzurin bayi dan nuni da hanyar bauta,

Ya aiko Muhammadu Manzo dan nunin matakan bauta,

Sarki masanin adalci mai jin tausayin al’umma.

 

Duk wani mai izo a bi doka sai ya bari a san iliminta,

Tsari na ƙasar haifa ta kundin tsaruwar mahukunta,

Rashin ilimi kan doka ba hujja ba ne a ƙasata,

Sannan ilimi a ƙasata ya zama biddiri al’umma.

 

In da duk ka je a ƙasashe fannin ilimin al’umma,

Kyauta ne ake ba kowa dan yanke uzurin al’umma,

Amma mu ƙasarmu ta gado ba a so mu san komai ma,

Dan mulki na kama karya mun yi kama da kifin koma.

 

Kun ji a nan ƙasar babata an kasa illimi rukunoni,

Iri na ɗiyan masarauta ko boko fa ko addini,

Iri na ɗiyan mahukun ta ko addini ko zamani,

Za sui ne ƙasar Turawa kun ji irin ƙasar alfarma.

 

Sannan a ƙasar babata an yi kala-kalar makarantu,

Kayan aiki ko malamai babu cikin su nagartattu,

Yajin aiki ay yi watanni har dai ɗalibai su shagaltu,

Ko sun kamala in ba aiki sai dai su zamo ‘yan kama.

 

A ƙasar iyayena na ne defot na barace-barace,

Domin rashin alkunya kan sanadin salon a yi fauce,

Dan neman karfar yin sata an yi gini da sunan ‘yance,

An gina makarantun boge dan almajirai al’umma.

 

Shi almajiri al’umma ba ɗan Adam ya zamo ba,

Dan shelanta ba shi da gata ba za a haɗa shi da mu ba,

An ware masa makaranta saura gwamnati ba wai ba,

Idan ya gama ina zai aiki wacce ma’aikata al’umma.

 

Idan an lura duk talakawa ko sun digiri fa a banza,

Ba gurbin da za kai aiki sai dai kay yi aikin banza,

Majalisar zaman kashe wando masu zama da sunan banza,

Ba aiki ɗiyan talakawa kun ji irin ƙasar alfarma.

 

Na tuna san da an ka yi shela a kan aiki na furzin taiga,

Na ga dubu-dubun talakawa na dako a filin daga,

Kowa ya fito sikirinin dan burin ya zamto taiga,

Adaddin waɗan da suka mutu an rasa rayuka al’umma.

 

Na tuno da aikin kwastom da ‘yan shekaru can baya,

Lokacin ina Kaduna an ka kira bakansi baya,

‘Yan digiri na hanga burjik na kwana gidan mai hanya,

An rasa rayukansu da dama kun ji irin ƙasar alfarma.

 

Wannan shekara ta dubu biyu da goma sha huɗu al’umma,

Shi a cikin uku Maris Imagireshin sun kai koma,

Komar tsakurar ‘yan aiki sai lamarin ya zam ba dama,

Wannan ya isar mu ji kunya kunyar duniya al’umma.

 

Mamaki da al’ummar nan da ba ta san kimar ilimi ba,

Mamaki da al’ummar nan da ba ta san kimar ra’ayi ba,

Kullum rayuwar talakawa fansa ce ga burin babba,

Sakirifayis ake yi da jininmu dan mulkin da bai ɗore ba.

 

Sun juyar da mai yin waƙa ya zamoto karan mafarauta,

A iza ka kac ci mutunci dan yunwa ka magance ta,

Yau ka zagi wannan sashe gobe ka je ka na ragaita,

Hanyar arziki ka bar ta hanya na rahama ka bar ta.

 

 

 

Ba a da tanadin iliminmu balle ma mu san ‘yancinmu,

Babu tanadin rayuwarmu babu asibiti na a kai mu,

Babu tanadin ‘yancinmu ay yi abin da ya shafe mu,

Kai mana magani Sarkinmu maji ƙai rayuwar al’umma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments