Kushewa- Daga Diwanin Wakokin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 92)

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

     

    Ranar da ba tsumi da dubara,

    Ranar da za ni kwanta kushewa.

     

    Duniya budurwar wawa,

    Matar mahaukaci ko wawa.

     

    Gidan maras gida mai ƙawa,

    Gidan maras rabo ran tsaiwa.

     

    Wa ke biÉ—ar ganin ruÉ—ewa,

    Yana ga mai sahun miƙewa.

     

    Mai tara dukiya don ƙawa,

    Zato yake ana É—orewa.

     

    RuÉ—i na dukiyar tarawa,

    Ta sa shi ya zamanto bawa.

     

    Bawan ciki da bai ƙosawa,

    Kullum a ba shi bai turewa.

     

    Kainuwa dashen mai kowa,

    Saman ruwa take tohowa.

     

    Gamji sassaƙa da sarewa,

    Ba ta hana ka kai tohowa.

     

     

    Rashin jini rashin tsagawa,

    A na zuwa a ke iskewa.

     

    Sarrari wuyar a ƙurewa,

    Mai sa mataffiya sarewa.

     

    A kwan a tashi mai gillewa,

    A kwana wattaran ba kowa.

     

    Ayau da ni ake damawa,

    Ina ta jan zaren saƙawa.

     

    A kwan a tashi na zama gawa,

    Koko zaren ya zam tsinkewa.

     

    Duniya fa ba É—orewa,

    Babu wanda zai É—orewa.

     

    Aminu É—an Kano ta Kanawa,

    Saƙo na zo nake idawa.

     

    Talla nake fa ba hargowa,

    Mai hankali kaÉ—ai ka tayawa.

     

    Ga magani a gonar kowa,

    Mai izgile ka yi hargowa.

     

    Allah wadan ido gululu,

    Idon da babu tsinkayowa.

     

    Da kunnuwan da ke jin sowa,

    Fage na gargaÉ—i É—oÉ—ewa.

     

    Da sau da ke zuwa ga fasadi,

    Ba sa zuwa ga amfanarwa.

     

     

    Da sautuka da kan furtawa,

    Ba furrucin da zai shiryarwa.

     

    Da baituka da kan tsarawa,

    Bisa hululu don sheƙewa.

     

    FiÉ“e sencery organs dubawa,

    Gani da ji da saurarawa.

     

    Shaƙa da ɗanɗanon ganewa,

    Da ji na zahirin ganewa.

     

    Dukkansu mai halittar kowa,

    Ya yi su don mu zam ganewa.

     

    Mu zam rabe kaloli tsanwa,

    Mu bautace shi ba ƙosawa.

     

    Abin bugun gaba gun bawa,

    Tsoron Mamallaki mai kowa.

     

    Dukkan abin da yai farawa,

    Tabbas gare shi kwai ƙarewa.

     

    Da ka ji alhudusu ta zuwwa,

    Sai ka ji alfana'u ƙirewa.

     

    Wannan kaÉ—ai fa ya ishi bawa,

    Taku da waiwayen dubawa.

     

    Mai izgili shira shiryawa,

    Ba ya zuwa gaba dubawa.

     

    Ina uba a gun duk wawa,

    Abu Lahabi ya ƙarewa.

     

     

    Uban maƙaryata mai kwarwa,

    Abdu Salulu ya sheƙewa.

     

    Uba ga jahilai mai tsiwa,

    Abu Jahala ya taɓewa.

     

    Ga mutakabbirin Misrawa,

    Fir'auna ya yi ya kwantawa.

     

    Ƙaryar Ubangiji mai kowa,

    Komai gudu tana iskewa.

     

    Gata kake da shi koko wa?

    Nabiyu mursalai ba kowa.

     

    Tun daga Adamu na Hauwa,

    Uba na talikai har kowa.

     

    Cikamakon nabi É—an baiwa,

    Wannan da kansa an ƙarewa.

     

    Malla nabiyu ba'adahu kowa,

    Mai izzini na ceton kowa.

     

    Wa yar rage abin dubawa,

    Wa ke da mattsayi zartarwa.

     

    Allah ka sa mu zam dacewa,

    Mu yo gamon katar ran tsaiwa.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.