Ticker

6/recent/ticker-posts

Noma

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Mu tashi mu farka Arewa

Mu kare mutuncin Arewa

 

Allah mabuwayi ka ƙarfafa yanki namu,

Mun san baiwa duka ka yi ta a yanki namu,

Ga ni’imomi bila adadin yankinmu,

Ga al’umma da ka yi a lardi namu,

Ƙarfafi zuciyarmu kar a katse mana karmu Arewa.

 

Mu tashi mu farka mutumgumi noma ƙasarmu,

Arewa da arziki na ƙasar noma cinikinmu,

Mui noman auduga mu noma gyaɗa dalarmu,

Mu samu abin kaɗi mu raya dukkan sana’unmu,

Mu tashi mu aikatu da dukka masaƙu namu Arewa.

 

Akwai mu da yanayi na noman kifayenmu,

Akwai mu da yanayi na noman kaji namu,

Mu yi noman Salwa mu warke dukan cutarmu,

Mu yi noman dawa hatsi wake masararmu,

Mu samu abinci da aikin kare ƙasarmu Arewa.

 

Mu kare mutumci da al’adu na garinmu,

Mu ɗaukaka martabar saraku dake mulkar mu,

Mu girmama shugaba dake mulkin yankinmu,

Da sun adalci mu bi su sawu da ƙafarmu,

Allahu ka kare Arewa da mai kishin mu Arewa.

 

Allah da ya yi mu ya yi mu daban a kalarmu,

Ya yi mu da ban-ban idan ka ji harshe namu,

Ya yi mu aji-aji kama-kama har addinanmu,

Ya ƙaddara mu zama guda a ƙasar haifarmu,

Mu zaune garinmu mu tashi mu kare ƙasarmu Arewa.

 

 

 

Idan Rabaran ka ke ka tashi a yanki namu,

In ko Alaramma ka zam a Arewa garinmu,

Mu ƙaunaci Allah mu bar haɗa kan mabiyanmu,

Mu tabbata fa Allah shi ya haɗe jinsinmu,

Ya yi mu ƙasa ɗaya mu zam kishin lardinmu Arewa.

 

Mu zam haɗa kanmu mu tattala arzuƙanmu,

Mu zam haɗa kanmu mu ɗabbaka ilimi namu,

Mu zam haɗa kanmu mu kau da bara a cikinmu,

Mu kare mutuncin ƙasarmu da yanki namu,

Mu girmama kanmu da shugabanni namu Arewa.

 

Sarki na Musulmi yana goyon bayanmu,

Ya ce haɗa kanmu ya ƙarfafi yanki namu,

Sarki na Kanawa yana nuni a garemu,

Ya ce da Kudawa Arewa dukansu ƙasarmu,

Sarkin Katsinawa ya ce mu kiyayi kanmu,

Mu sada zumunci tsakanin ƙabilu namu,

Sarkinmu da Daura ya ce mu tsare hakkinmu,

Haƙi na maƙwabta abokan harƙoƙinmu,

Sarkinmu na Zazzau ya ce mu tallafi kanmu,

Mu sam aikin yi tsaye a diga-diganmu,

Sarkinmu na Barno yana addu’a a garemu,

Neman sauƙi Arewa garin kakanmu,

Neman sauƙi Arewa gari da ƙasar mu,

Sarkinmu na Bauchi yana ta tuni a garemu,

Ranar tsayuwa mu san da su’al a garemu,

Sarkinmu na Gombe yana ALA kare garinmu,

Ya kare ƙasarmu ya kare Arewa garinmu,

Sarkinmu na Yola na iske yana yin saumu,

Yana ta Wahabu ka kare zubi na ɗiyanmu,

Sarkinmu na Naija da Keffi cikin zikirinmu,

Suna aza karu cikinsu ji daɗa ta ƙimu,

Sarkin Kebbi da Zuru Arewa garinmu,

Ƙiyamul laili suke dan kare garinmu,

Sarkinmu na Zamfara da Dutse suna tausam mu,

Mu kai kukanmu gurin mai ceto namu,

Malaman addini suna sujada da siyamu,

Suna ta du’a’i Allahu ya kare garinmu,

Ka kare garinmu Allahu ka kare ƙasarmu,

Mu tashi mu farka Arewa mu kare mutuncin Arewa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments