Irin gijin sakarkari,
Jami’a gidan wuya,
Rayuwa a duniya,
Ala sai kai a hankali.
Rayuwa a duniya,
Jami’a gidan wuya,
Irin gijin sakarkari,
Aminu sai kai a hankali.
Aminu in yau anai da kai,
Aminu gobe a yar da kai,
wataran a yi babu kai,
Ka bar jiji da kai,
A duniya sai a hankali,
Ka zamo mai hankali,
Mai aiki da hankali,
Ka zamto aƙili,
Aminu ko kuma adali.
Allah kula da ni ka san da ni a arziki,
Kar nai ƙarkon kifin ruwa,
Kar nai sakkon bukukuwa,
Kar na jewar unguluwa,
Kula da ni ka san da ni.
Allah mai zamani Aminu ALA bawan ka ne,
Allah ke da magani,
Allahu kuɓutar da ni,
Allah ka hayar da ni,
Makiɗar zamani,
Allah ka san da ni,
Azimul zamani yarda na zamo aƙili.
Yanzu ga shi ina waƙa bisa izza da kwarjini,
Yanzu ga shi ina waƙe isahe ba da kwarjini,
Gobe sai da wanina ni na shuɗewa zamani,
Mutuwa ko tsufa Alan waƙa ya riski zamani,
Yau da gobe karyar Allah Sarki mai cim ma mumini,
Allah ka san da ni ka sa ni a taska ta adali,
Tasku na adali.
Allah tsare ni da sharrin sheɗan kar yai ƙawa da ni,
Allah tsare ni dan harshena zai hallakar da ni,
Harshenka assadinka in ka sake shi a zamani,
Shi za ya hallaka ka a ƙarshe ka goce zamani,
Ka zama daƙili gwaliƙi ga goce zamani,
Muddabbirul zamani,
Ya alimul zamani,
Ya sirril zamani,
Allah ne mai zamani,
Kai ni zamani,
Tsare mu da zamani,
Zai sure mana hankali.
Alan zamani,
Taka tsantsan da zamani,
Cutar zuciya Allah shi ke da magani,
Ka ƙanƙame Rabbana da bauta ba ji ba gani,
Akun hakuru ne mai kyauta ba wani bambini,
Muna roƙon Ilahu ya ƙarfafi dukkan mumini,
Ya sa mu ciki na ceton Manzo Sarki adali,
Sarki adali Manzo Sarki adali.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.