Ticker

6/recent/ticker-posts

Aure Ibada

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Allah masanin abin da ba ma san shi ba,

Na cikin sarrari da gaibi duk bai ɓoyu ba,

Bashar Ɗan Dago da babu a kogunku ba,

Ya ɗau bahharin da ALA bai san shi ba,

Matsalolin ma’aurata yak ke ƙwazza ba,

Matsalolin da ba yi wa karan tsaye ba,

Sai mai hankali da lura zai rarraba,

Sarƙaƙƙen halin da Ɗan Dago zai rarraba,

Manazarta ku ɗauki alƙaluma kuz zuba,

Baban Rumasa’u zai kore ja’iba,

Da amonkarsa shi da siga marar fargaba,

Ga Maryama ki wakilcin mata gaba.

 

Aure ibada zaman sa ɗan haƙuri ne,

In ka daka ta zuciya zaman ba zai samu ba.

 

To bisimillahi Jallah Rabbi abin dogaro,

Sarkin da yai rayuka ya bai al’umma aro,

Rufa mana asiri Ilahu raba ni da tallen ƙaro,

Haɗa ni da masoya mai iko ba zan san shi ba.

Ni ba zan san shi ba.

 

Kay yi salati ga Annabi Ɗaha Uban Faɗima,

Wannan da a kullum da arzikinsa nake taƙama,

Da ƙaunarsa nake ado gidansa nake hidima,

Masoyin Allah wannan da bai taɓa saɓon sa ba.

 

Bashirun kuna Ɗan Dago a yau zai wani nazari,

A kan halayen ma’auratana rashin haƙuri,

Mai gida girman kai Uwar gida ko tana yunƙuri,

Da an ɗan ɓata ta ce gidan ga ba zai zaunu ba.

Sam-sam ba zai zaunu ba.

 

 

 

Ta kafa kai tai waje ta je ta gida tai amai,

Abin da akai har da wanda ba ai ba ta buɗe sarai,

Iyaye su ga sirkinsu ya ɓata musu rai,

Ko da an yi sulhu ba sa mayar ma sa ƙimarsa ba.

 

Idan ɓera da sata ina lamarin daddawa?

Ni Maryama na fahimta da bazarmu kuke rawa,

Fagen neman aure za a ga kanku yana yin rawa,

Idan kun sa mu soyayyar da ba za ku tuna ta ba.

 

Ki ɗau namiji Uba ki mutu marainiya ‘yar uwa,

Da daɗin murya ya tarar da ke har soron Uwa,

Da kin tari za ya ce miki me yake faruwa,

Haba mai dalin ban yarda sauro ya taɓa ki ba.

 

Da kin ba shi zanin anko a gurguje za yai miki,

Idan ya aure ki sai fa komai ya canza miki,

Hatta a kuɗin cefane yana zargi a ciki,

Batun sabon ɗinki kya shekare ba ki same shi ba.

 

Bar kukan daɗi Maryama halin ku akwai wuya,

To ki koyi da matan Ɗaha hairul ambiya,

Koko ki duba ga Faɗima ‘ya ga ambiya,

Duk sun biyayya ba su yad da aure su kashe shi ba.

 

To matan yanzu ko so suke sui gasar zani,

Ko sarƙoƙin daham da takalman zamani,

Da sun ga ƙawa ta yi shiga su zo gida da guna-guni,

Su takura mazansu wai su ba za su wulaƙanta ba.

 

Ƙarshe in aure yam mutu su za su fi cutuwa,

Ko da a makwanci gidansu sai dai sui raɓuwa,

A ba ta tabarma ta je cikin yara kwantawa,

Girma ya watse ƙannen ba za su ga girmanta ba.

 

 

 

Da safe guɗararsu duk ta wanke ba wata gardama,

Ta ɗebo kayansu duk ta wanke sannan ba zama,

Abin mamaki ƙannen ta da gunta suke nema,

Da sun ga ta dawo ba za su yarda ta aike su ba.

 

Na Ɗan Dagona gane batunka ko san kai ne gaba ɗaya,

Laifi tudu ne ka take naka kawai ga baya,

Idan gida ya ɓaci mai gida fa ake tambaya,

Adadin matansa adadin batun sa ba zai kimtsu ba.

 

Cikin abokansa ka gan shi na ƙyalƙyala dariya,

Amma a gidansa ya ɓata rai rana da safiya,

Da safe a hau sa-in-sa da shi kan kayan miya,

Kyautarsa ga matan waje ba za fa ta kintatu ba.

 

Da ya matso gida ya gyara murya ka ji yai um um,

Kurin gida ne yara su kama sui kakam,

Harƙa ta ƙare da walwala an daina su sam,

Shi manufarsa a gida ba zai yu a raina shi ba.

 

Ko da kun ɓata addini ya ce ki zauna gida,

Kar ku je ga iyaye yin haka zai kawo gargada,

Ki caɓa ado tsaf-tsaf da safe kina rangwaɗa,

Da wuya ai sati laifin da ki kai bai yafe shi ba.

 

Bincike ya nuna mutum uku ba su da sa’ar aure,

Mutum ɗaya ne jal yafi kowa dace gun aure,

Ku bi ni a sannu in baku su ba wani ƙetare,

A nan za ku gane mata ba su san mai ƙaunar su ba.

 

Farko basarake dacensa da aure bai samu ba,

Ya ba da umarni amma a gida ba zai bayu ba,

Hatta a gidansa so ake yam mutu ba dai bi ba,

Ba a taransa burinsa bai wuce a gaje shi ba.

 

 

 

Na biyyu mai kuɗi ma azirci mai tarin dukiya,

Matarsa ba ta biyar sa sau da ƙafa sai dan dukiya,

Auren jari take da shi a cikin duniya,

Giwa ta faɗi su sharɓe nama ba su damu ba.

 

Na ukku Malami masanin Allah sarki ɗaya,

Komai yake yi matarsa ba tai masa godiya,

Ya gaya mata Allah ta ja da baya tai wani dubiya,

Ko ‘yan banki wa’azi ba zai shiga kunnenmu ba.

 

To waye ya dace da aure Ɗan Dagonai tambaya?

Fagen dacewa da aure ka ware mutum ɗaya,

To wane ne faɗe shi kunnenmu ya ji jiya,

Ka ce akwai shi faɗe shi ba tare da ƙwange ba.

 

Haƙiƙa ɗan giya ya fi dacewa da macen zama,

Ya sha in ya faɗi ita za ta ɗauko shi tana tsuma,

Ta kinkintsa shi da ya nutsu sai ya doke ta ma,

Amma dan biyayya ba za ta taffi ta ƙyale shi ba.

 

Mazanmu da mata mu ɗau haƙuri a wannan zama,

Mu ɗaukar ibada kar mu ba sheɗanu gurin zama,

Duk baitukannan da mu kai mun yo su da hikima,

Mun yo wa’azi ne ba dan mu ɓata wa waninku ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments