Ticker

6/recent/ticker-posts

Dan Jarida

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Ku gafara ya share rawatai,

Wai baza ya zamo ɗanjarida.

 

Da fari Rabbana na yo kamun ƙafa da yabon Mahmudu,

Da so da bibiyar Manzo Almustafa ka sa kanai sa’a.

 

Ubangijina roƙo kai lamuni in rubuto ƙasida,

Ku gurguso akwai babban al’amari daga bakin Jakada.

 

Da wa’azi waɗansu suke horo na so ko ta hanyar ƙasida,

Ɓangarenmu ni ko ina horon maza da rubutun jarida,

 

Da kurkuku waɗansu su ke horo na so ko su ke bada oda da bindiga,

Waɗansu su ke horo hani koko su watsa hoda.

 

Ku ɗan kula fa ko kafui a ka sa gari ban da mu ‘yanjarida,

Da ka taɓa mu sai mu bari duniya ta ji ka taɓo ‘yanjarida.

 

Ko shugaba ka zauto ko kuma mallami koko mai bada oda,

Muna sani da tarihin kowa aje tanadi don jarida.

 

Kuna sane da kaifi na alƙalami ya fi gafi na hoda,

Da na ga dama sai in rubuto atikil ko in zano ajenda.

 

Ku gafara in doki magauta kai tsaye na riƙe al’amuda,

A duniya wanda na so shi zana yi na zamo ɗanjarida,

 

Ku ban guri in tauna tsakuwa kai tsaye mai aya sai ta kauda,

Ina cikin nishaɗi ga alfahari na zamo ɗan jarida.

 

A yanzu ni fa ko fa hamayya ba a min in ka min sai rejoinder,

Idan na nemi mata in ka sake ka je ka ji yo a jarida.

 

 

Idan na so a ji ka ɗan loto kaɗan ko ina sai a sada,

Idan na so in rusa ma alƙadari sai in harbo jarida.

 

Ina ga ni tsirarar kowa ni tuƙui ban da dangi jarida,

Ina ganin saman kan kowa a seɗe ƙwal kwabo babu hoda.

 

Da ɗamara kake tunƙaho ko kuwa ko da doka da oda?

Ina da ƙalmin sauƙe mai rawani ko in ɗora jarida.

 

Kuna sane fa ko a fagen yaƙi da mu ne a ke ‘yanjarida,

Mu raurayo bayanai mui maku tanadi dan karatun jarida.

 

Anan fa ka ga mun zamto maku fitilu masu saƙon sa’ada,

Wani jiƙon mu zam fitilar sharrin gari masu hasko jim raɗa.

 

Manufa ta aikinna wayar da kai anka samo jarida,

Manufa ta aiki don a warware ƙusuƙun da jimurɗa.

 

Manufa ta aikinnan a ji ra’ayi nasu ‘yan ba da oda,

Manufa ta aikinnan a ji ra’ayina ƙasa don a ida.

 

Ni sai na juya aikin nan kan ra’ayina na shashshafa hoda,

Da na ji ba ni ƙauna ko kuwa ra’ayi sai in sa al’amuda.

 

Bare a ce kana tunƙaho ka yi suna kana ba da oda,

Kana ganin a yau kai ke yin sharaɗi sai in yi ma rejoinder.

 

Ina da masu ɗauko min dukkan rahoto da hoton jarida,

Ina ta bi ta bi-ta-da-ƙulle da tanadi dan kawai nai jarida.

 

Idan na zo ni ɗaukar labari naka sai fa ka ba ni lada,

Da ka ƙiya in juya ma alƙalami ka ga aikin jarida.

 

Da lafiya ake dukkan al’amari a zaman shaya daga,

A yanzu ga ni zaune cikin ɗaki bugui ba ni aikin jarida.

 

 

Hayaniyana ɗorawa kaina dukka ta zame min jim raɗa,

Yau ina cikin cutar ɓarin jiki ba ni ba yin jarida.

 

Da laifuka na ɓatanci dukka na yiyo jama’a sun kai shaida,

A yau ina cikin hali na tausayi mai biɗar yin shahada.

 

Na yi sharri sannan na yo ƙazzafi ba ƙidaya da ƙa’ida,

A yanzu babu halin neman gafara dukka sun shaida.

 

Allah Ubangiji Sarki mai gafara rahma mai sa’ida mai afuwa,

Ga laifi ko ya kai sama zai maye ma da lada.

 

Idan zama laifinnan kuma Shi kawa kai tuba a oda,

Ubangiji cikin rahama ta sa za ya sa ka zamo mai sa’ada,

 

A yanzu ni ko laifina dukka sharri ne da ƙazabba babu shaida,

Na taho ina neman ku da fattawa don in risko shada.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments