Ticker

6/recent/ticker-posts

Lu’u-Lu’u

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

Lu’u-lu’u a cikin juji,

An zubar da dukan juji,

Yaƙutu a kan juji,

Tagulla a kan juji,

Allah ke isa da bayarwa.

 

Amshi 

Lu’u-lu’u a cikin juji,

Sun tadda ni a kala,

Allah ne me isa da bayarwa,

Mai isa da karɓewa.

 

Allahu mai abin mamaki al'ajabi ibadallah,

Dubi haihuwar Annabi Isa ba uba ibadallah,

Dubi rayuwar Annabi Musa a gidan aduwullah,

Dubi rayuwar Annabi Yusuf rijiya ta zam daula,

Dubi rayuwar Ibrahimu sai wuta ta zam daula,

Waiwaya ka je ga Sulaimanu mulki cikin daula,

Karkata ga Annabi Yunusa da kifi ka yo ƙwalla.

 

Ku tuno da Annabi Nuhu da ɗufana ibadallah,

Dubi rayuwar Asahabul Kafi ta sa ka kai ƙwalla,

Ka tuno da Naƙatus Saluhu ka sake yin ƙwalla,

Kar ku manta ƙissar yaro Rabbu Gulam ibadallah,

Dubi rayuwar Muhammadu Sayyadina Rasulallah,

Ikonka ta wuce komai, Ilahu ganiyu jallallah,

Mai tasarrufin komai da isa da buwayiwa Allah.

 

Abin dogaran Ala, Allah madogarar Ala,

Waƙa noman Ala, tabarma ta kwanciyar Ala,

Kafar sanin Ala,

Suttura adon Ala,

Gani da jin Ala, hanya ta martabar Ala,

Silar ilim Ala, siga ta yaɗuwar Ala,

Allah ubangiji na gode da ni'imarka jallallah,

Sila ta samuwar komai tana a gurin ka jallallah.

 

Sara da sassaƙa ba kashe gamji yake yi ba,

Kainuwa dashen Alalh Buwayi ba ga mutum ne ba,

Tsiran tsiro a tsandauri sai Allah ba mutun ne ba,

Hassada ga bawa rabo-rabon riba, rabo babba.

 

Haƙuri isa ga muradi ba jinkiri asara ba,

Juriya da jajircewa dace ba kasala ba,

Aiki da hankali nutsuwa ga abin biɗa babba,

Aiki da tunnani ke rabba tsatson mutum, dabba.

 

Ɗan uwa fa harshenka zakinka da za ya cinye ka,

In ka iya bakinka ka tsira da rayuwa taka,

Ɗan’uwa tunaninka shi ne fa awon kamanninka,

Ɗan’uwa tunaninka shi ke sadar da furucinka.

 

In ka furta furucinka da shi za a gane nauyinka,

Ɗan’uwa bayaninka mizani a gane ilminka,

Shi ake fa aunawa a gane duhun jahalarka,

Shi ake fa aunawa a gane gaba na ƙilbarka.

 

Hankali abin awon Ala,

Tunani maribacin Ala,

Hikkima makewayin Ala,

Fasaha fa dandalin Ala,

Zalaƙa abin riƙon Ala,

Yaƙini madogarar Ala,

Allah mataimakin Ala,

Allah Ubangiji na gode damar da kai a gun Ala,

Ka tsarkake ji da gani da mu'amalar Ala.

 

Allahu kai ka tara sani na abin da yake samaninka,

Allahu kai ka tara sani na abin ƙarƙashin ƙasa taka,

Allahu kai ka ɓoye sani na abin da ke gudu a kan iska,

Allahu mai dubun sannai na abin da ke ƙasan ruwa dukka,

Allah mai tsirar da tsiran tsandauri faƙo fa ba shakka,

Ga tsiro a kamfa ya tsiru tsaf tsara suna shakka,

Ikonka ya wuce komai ina daɗa riƙo da tsoranka.

 

Ni Aminu ba ɗan sarki, ba basarake ba,

Ni Aminu ba ɗan gwamna ba, ba mai muƙami ba,

Ni Aminu ba ɗan masu kuɗi ba, ba mai kuɗi ne ba,

Ni Aminu ba ba ɗan malam ba, ba fa mu'allim ba

Ni Aminu ba fa ma'aikacin rediyo da tibi ba,

Rabbana ka yalwata harshena ba da baɗala ba,

Gashi na zamanto lu'u lu'un juji ku yo duba.

 

Allahu mai dubun komai

Mai tasarrafin komai,

Shi yake rabon komai,

Sai ya ba ka yai maimai,

Babu mai yi ma komai,

Sa ni na zamo jarmai,

Sha gwagwarmaya gwarmai,

Rabbi kai ka san komai, Illahu maƙaddarin komai.

 

Lu'ulu'ueey… Lu'u lu'uuu!

Lu'ulu’u a ciki juji,

Tsintar dami a kala Allah ne mai isa da bayarwa,

Mai isa da karɓewa

 

Lu'ulu'u a cikin juji, tsintar dami a kala,

Allah ne mai isa da bayarwa, mai isa da karɓewa.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments