Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Idan Mijina Bai Neme Ni Ba, Ni Kuma Na Ƙi Neman Sa Na Yi Laifi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam don Allah ina neman karin haske saboda ina gudun fadawa fushin Allah, Idan mijina ya neme ni zuwa shimfidarsa ina zuwa, to ina so in sani idan bai neme ni ba! Ni kuma ban je ba ina da laifi, kasancewar mutum ne me wuyan sha'ani ko da na yi niyyar faranta masa rai, da zaran ya dawo gidan sai neman fitina, in na cika matsansa sai fada sai wulakaci, sai in gwammace ban je, ba.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, idan miji bai nemi matarsa zuwa shimfiɗa ba, ita kuma ta ƙi nemansa, to ba za a ce ta yi wani laifi ba, sai dai inda laifin yake shi ne; idan ya neme ta ta ƙi ba shi haɗin kai, kuma ba tare da wani uzuri da shari'a ta yarda da shi ba, to tabbas Malá'iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari, saboda hadisin Annabi da yake cewa: "Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfiɗarsa sai ta ƙi, kuma ya kwana yana fushi da ita, Malá'iku za su yi ta tsine mata har sai ta wayi gari". Bukhariy 3237.

Saboda haka babu laifi a kan mace saboda ba ta nemi mijinta ba, har sai idan shi ɗin ya neme ta ita kuma ta ƙi amsa masa, kamar yadda wannan hadisin ya nuna.

Sai dai yana daga cikin kammaluwar mace a wurin namiji, ta zama tana nemansa ko da shi bai neme ta ba.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments