Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Dhul Hijja

🔸Babu wasu kwanaki a duniya da suka kai falalar  kwanaki goma na farkon watan Dhul Hijja, in ban da dararen goman karshe na watan Ramadhan, kamar yadda wasu malamai suka ce.

🔸Aikin alheri a cikin su ya fi soyuwa, falala da girman lada a wurin Allah سبحانه وتعالى. Saboda haka su ne kwanakin da suka fi dukkanin kwanakin shekara falala

🔸 Annabi صلى الله عليه وسلم ya yi umarni a yawaita yin kabbara (Allahu Akbar) da Hailala (Là'ilàha illallah) da Hamdala (Alhamdulillah) a cikin wadannan kwanaki masu albarka.

🔸 Ana so a fara yin kabbara tun daga ranar farko na watan Dhul Hijja. Ana so a dinga yi a masallatai, a cikin gida, a kasuwanni, a kan hanya, a kitchen da sauran su. Ana so a yi shi a ko da yaushe. Ana so kuma a yi shi a bayyane.

🔸 Wadannan kwanaki goma masu albarka suna da girma a wajen Allah سبحانه وتعالى ya kamata mu yi farin ciki da zuwan su, mu ribaci alkhairan da suke cikin su, mu rayasu da nau'ikan ibada, mu tuba, mu koma ga Allah سبحانه وتعالى.

🔸 Aikin alheri ya ƙunshi duk abin da Allah سبحانه وتعالى yake so kuma ya yarda da shi. Saboda haka mu fuskanci wadannan kwanaki da yawaita yin nafilfili, azumi, karatun Alqur'ani, zikiri da sauran su.

🔸 Kada mu manta cewa shigar da farin ciki a zuciyar musulmi yana cikin mafi soyuwar aiki a wurin Allah سبحانه وتعالى balle a cikin wadannan kwanaki masu alfarma.

Allah سبحانه وتعالى ya nufe mu da aikata abin da yake so, kuma ya yarda da shi. Allah سبحانه وتعالى ya sa kuma ya zama karbabbe a wajensa cikin rahmarsa.


Copied.

Post a Comment

0 Comments