Cite this article as: Gummi, M.F. (2023). Lafiya Jari: Tsakuren Gudunmuwar Sarkawa Ga Ayyukan Kiwon Lafiya Na Gargajiya. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)1, 113-121. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i01.014.
Daga
Dr. Musa Fadama Gummi
Department of Languages and Cultures, Federal
University Gusau, Nigeria
Email: gfmusa24@gmail.com, mfadamagummi@ fugusau.edu.ng
GSM NO.: +2347065635983
Tsakure
A Æ™asar Hausa, masu aiwatar da sana’o’in gargajiya suna da muhimmanci matuÆ™a. Baya ga samar da kayayyakinsu ga
masu saya, suna kuma taimakawa sosai ga sha’anin bayar da magungunan gargajiya.
Kowane mai sana’ar gargajiya yana da fannin da ya Æ™ware a sha’anin magani. Manoma, ga misali, su suke
bayar da maganin ciwon baya da na zafin rana. Sarkawa, waÉ—anda sana’arsu ita ce kamun kifi, na da muhimmanci matuÆ™a wajen samar da kifi, wanda ke É—auke da sinadarai masu gina jiki da Æ™ara lafiya. Baya ga wannan suna gudanar
da muhimmin aiki dangane da abin da ya shafi bayar da magungunan gargajiya. WaÉ—annan ayyuka nasu na bayar da maganin gargajiya ne wannan
muƙala ta ƙuduri warware zare da abawarsa.
Binciken an aiwatar da shi ne ta hanyar bibiyar Sarkawa tare da yin hira da su
domin zaƙulo ire-iren gudumawar
da suke bayarwa a fagen kiwon lafiya.. Muƙalar, ta gano cewa suna bayar da
magunguna na waraka daga cutar sanyi da ma sauran cututukan da ake iya ɗauka a cikin ruwa kamar tsagiya da cutar ƙaiƙayin jiki da cutar sanyi. Haka kuma
suna bayar da magungunan riga-kafi, da magungunan biyan buƙatun zuciya, har ma da na siddabaru, da
na sharri. Muƙalar ta karkata ga
magungunan cututukan jiki, waÉ—anda Sarkawa suke taimaka wa al’umma da
su. Yana da kyau masana ilimin haɗa magunguna na zamani su yi ƙoƙarin gano sinadaran da ke ƙunshe cikin magungunan da sarkawa suke
bayarwa da nufin ƙara inganta su da
kuma zamanantar da su.Yin haka zai taimaka wajen samar da kiwon lafiya mai
rahusa ga al’umma.
Fitattun Kalmomi: Tsakure, Gudunmuwa, Sarkawa, Kiwon lafiya, Gargajiya
1.0 Gabatarwa
Cuta da magani da
lafiya, wasu muhimman abubuwa ne, masu buÆ™atar kulawar gaske, a kowace al’ada
ta kowace al’umma ta duniya. Cuta wata damuwa ce da take shiga jikin
É—an’adam domin raunana garkuwar jikinsa;
tana iya shafar zuciyarsa ta fuskokin buƙatocinsa na jin daɗi ko ɗaukaka darajarsa da sauransu.[1] Magani abu ne da ake amfani da shi domin gusar da ko
kwantar da ko kare jiki daga kamuwa da cutar da ka iya takura wa lafiyar
halitta walau ta mutum ko dabba da dai sauran halittu.[2] Al’ummar Hausawa wayayyiyar al’umma ce da take da tsarin
kiwon lafiya da ya dace da muradun ahalinta tun gabanin shaÆ™uwarta da kowace irin baÆ™uwar al’umma daga Æ™etare, walau daga gabas, balantana
yammacin duniya. Kowane rukunin al’umma da ke aiwatar
da sana’o’in gargajiya, na da rawar da yake
takawa, wajen wanzar da kiwon lafiya na gargajiya a cikin al’umma ta Hausawa[3]. A misalce, wanzamai likitoci ne na gargajiya da har fiÉ—a suna yi domin cire cuta a jikin marar lafiya. Cutar
ciwon ƙugu da na zafin rana sai an koma wajen
manoma. Maganin wuta kuwa, maƙera ba kanwar lasa ba ne. Haka dai
kowane rukuni na masu sana’o’in gargajiya na da nasa Æ™warewa dangane da irin nau’in taimako da yake bayarwa a sha’anin kiwon lafiya na gargajiya.
Ƙudurin wannan muƙala shi ne nazartar irin ayyukan da
Sarkawa suke yi domin bayar da tasu gudunmuwa ga sha’anin kiwon lafiya, irin na
gargajiya. MuÆ™alar za ta waiwayi waÉ—annan ayyuka ta la’akari da rukuni na farko daga
rabe-raben magungunan gargajiya da masana (Bunza, 1995) da (Sarkin Gulbi, 2014)
suka samar. Rukunin na farko kuwa shi ne magungunan cututkan jiki. Muƙalar za ta waiwaye a kan waɗansu cututuka, ta yi nutso da nufin ƙyallaro yadda Sarkawa suke agazawa wa
al’umma a wajen bayar
maganin cutar, domin inganta kiwon lafiya a tsakanin al’umma.
2.0 Ma’anonin tubulan take
Gabanin shiga cikin ayyukan sarkawa dangane da bayar da
magani, ya dace mu dubi fitattun kalmomi, waÉ—anda tubula ne da aka yi amfani da su domin gina taken
wannan bincike. Kalmomin su ne, tsakure da gudunmuwa da Sarkawa da kiwon lafiya
da kuma gargajiya.
2.1 Tsakure
Kalmar tsakure kalmar Hausa ce ta asali. An samo ta ne
daga kalmar tsakura. Kalmar tana nufin É—ibar abu Æ™anÆ™ani daga cikin maiyawa.[4] Ayyukan da Sarkawa suke gudanarwa, waÉ—anda suka jiÉ“inci sha’anin kiwon lafiya a cikin
al’ummar Hausawa suna da yawa ainun. Wannan muÆ™ala taÆ™aitacciya ce don haka ba za ta wadatar
ba a ce an kawo dukkan gudunmuwar da suke bayarwa dangane da kiwon lafiya irin
na gargajiya, a cikin al’umma ta Hausawa.
Kasancewar ayyukan nasu da yawa, an É—an gutsuro wasu daga ciki ne, ba wai
duka ba. Abin nufi, muƙalar ta taɓo ƙalilan ne daga cikin magunguna da Sarkawa
suke bayarwa.
2.2 Gudunmuwa
Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, ya faÉ—a cewa, kalmar gudunmuwa tana É—aukar ma’anar taimako na aiki ko kuÉ—i ko abinci ko sutura ko wani abu CNHN (2006 p. 171). Bargery
(1934 p. 402) kuwa cewa ya yi gudunmuwa na nufin taimako ko ƙarfafawa. A wannan muƙala, gudunmuwar da ake son a bayyanawa
ita ce nau’in taimako da É—auki wanda Sarkawa suke bayarwa a fagen
kiwon lafiya. Wannan kuwa ya shafi taimakon da suke yi wa al’umma ta hanyar samar
da abinci (kifi) mai gina jiki da ƙara masa karsashi da ƙoshin lafiya, haɗe da aikin da suke yi na bayar da magungunan gargajiya
domin hana wanzuwa tare da kawar da damuwa a jikin É—an’adam, musamman abin da ya jiÉ“inci cututuka da ake kamuwa da su sakamakon tu’ammali da
ruwa.
2.3 Sarkawa
Bisa asali, kalmar Sarkanci an samo ta ne daga kalmar
‘Sorko’, wata al’umma a daular Sanwai. Wannan al’umma ta shahara matuÆ™a a sha’anin fito na jirgin ruwa da kuma kafin
kifi a kogin Kwara da fadamun da suka raÉ“i kogin. Bakin masana kamar AlÆ™ali, (1969) da Wara, (2019) ya zo É—aya dangane da cewa tun farkon Æ™arni na 19 ne Sarkawa suka riÆ™a gwamutsowa yankin Kabi da nufin faÉ—aÉ—a sana’arsu ta kamun kifi. Sannu a
hankali suka sami gindin zama a wannan yanki kuma sakamakon auratayya, cikin
sauÆ™i, al’ummar ta Sorko sai ta saje da
al’ummar Hausawa da suka tarar. Dalilin Æ™warewarsu a fagen kamun kifi da ingancin makamansu na
kamun kifi ya sa suka yi tasiri sosai a sha’anin sana’ar, ba wai Kabi kaÉ—ai ba, har da sauran yankuna, inda sana’ar take
gudana. A yanzu, Æ™warewa a sana’ar su ko kamun kifi, ita aka sani da
suna sarkanci. Ƙwararren mai aiwatar da sana’ar kuwa, ana kiransa Basarke; jam’insa
kuwa Sarkawa.
2.4 Kiwon lafiya
Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, CNHN,
(2006 p. 247) ya faÉ—a cewa kiwon lafiya shi ne tsabta. A
tunanin wannan muÆ™ala, ma’anar da Ƙamusun ya kawo ba ta wadatar ba. Dalili
kuwa shi ne kiwon lafiya ya zarce tsabta kawai. Abubakar, (2015 p. 264) cewa ya
yi, kiwon lafiya shi ne nazari da ayyukan tabbatar da lafiyar jama’a. Shafin
matambayi ba ya É“ata na wikipedia cewa ya yi kiwon
lafiya shi ne
Inganta lafiya ta hanyar yi wa jiki kandagarki daga cuta
da binciken gano ko tabbatar da cutar
da nufin kwantar da ita ko magance ta, haka ma duk wata damuwa kamar rauni ko
duk wata kasala ta jiki ko ta ƙwaƙwalwa da ka iya shafuwar mutane.[5]
A taƙaice kiwon lafiya shi ne duk wani yunƙuri da ake yi domin kula ko kiyaye
lafiyar jiki da ta zukata, ta hanyar yi wa jiki garkuwa ko magancewa ko kwantar
da duk wata damuwa da ka iya illata ko yi wa É—an’adam barazana ga lafiyarsa da walwalarsa.
2.5 Gargajiya
Kalmar gargajiya Bahushiyar kalma ce. Abubakar, (2015 p. 156)
ya ce kalmar tana iya É—aukar waÉ—annan ma’anoninu: Gado daga tsohon zamani, hali ko al’ada
mai asali tun daga da. Abin da ba a wannan zamani aka Æ™irÆ™ire shi ba. Abin da al’umma ta gada daga zamanin da ya shuÉ—e. Bunza, (2006 p. xxvii) ya ce daga kalmar gado ne aka
sami gadajje da gargajiya. A nan duk wani abu aka ce na gargajiya ne, to ana nufin abin da Bahaushe yake
jin shi ke da shi tun fil azal kuma babu nason wata al’ada a ciki gaba É—aya.
Kiwon lafiya na gargajiya a nan yana nufin hanyoyin kula
da kiyaye lafiyar al’umma, waÉ—anda Bahaushe gadon su ya yi daga kaka
da kakanni, ba su da wani É—osane ko surki da wasu hanyoyi ko
dabaru na kiwon lafiya na wasu al’ummu na daban, saÉ“anin Hausawa.
3.0 Ayyukan sarkawa na kiwon lafiya
Ayyukan Sarkawa na kiwon lafiya suna da yawa matuÆ™a kuma wannan muÆ™ala kaÉ—ai ba za ta iya Æ™unsar duk bayanan ayyukansu ta É“angaren kiwon lafiya ba. Duk da haka, za a É—auki wasu muhimmai a bayyana su, ta la’akari da wasu
muhimman sassa na kiwon lafiya na gargajiya na Hausawa. Misali, za a É—auki riga-kafi da agajin farko a matsayin wani rukuni, ayyukan
da suka jiɓinci waraka su kasance wani rukuni na
daban.
Bunza, (1989 p. 134) ya kawo bakandamiyar ma’ana dangane
da magani. Masanin cewa ya yi:
Magani wata hanya ce ta warkarwa ko kwantar da, ko rage
wata cuta ta ciki ko ta waje ko
wadda aka samu daga haÉ—ari ko kuma neman kariya ga cutar
abokan hamayya ko cutar da
su ko neman É—aukaka ta daraja ko buwaya, ta hanyar
siddabaru da sihiri na ban al’ajabi
3.1 Riga-kafi
Bahaushe yana cewa ‘riga-kafi ya fi magani’. Abubakar,
(2015 p. 410) ya ce riga-kafi shi ne abin da ake yi ko ake ci, ko ake sha don
neman hana shigar cuta. Wato irin wananan magani ana yin sa domin yin kariya ga
jiki, yadda cuta ba za ta shiga cikinsa ba. Sarkawa suna da iri wannan magani
da suke bayarwa. Daga ciki, babban riga-kafi da suke yi shi ne É—aurin ruwa.
3.1.1 ÆŠaurin ruwa
Wannan wata al’ada ce da ta shafi yin maganin duk wani
mugu da zai iya cuta wa mutane yayin da suka shiga ruwa. ÆŠaurin ruwa shi ne magani ko laÆ™ani ko addu’ar da ake yi domin samun kariya da hana
kowane irin kifi ko dabba motsawa. Haka kuma don a hana mugun iska cutarwa a lokacinlokacin
da aka shiga ruwa domin ƙetarewa (tsallakewa) ko domin aiwatar
da kamun kifi. Yin haza zai sa a shiga ruwan lafiya a kuma fito lafiya, ba tare
da wani haÉ—ari ya faru ba. (Fadama, 2015 p. 168).
Idan fashin ruwa za a yi, Mairuwa ko Sarkin ruwa ne ke da
alhakin É—aure ruwa gabanin a shiga. A É—aiÉ—aiku ma, kowane masunci yana da tasa
dabara da yake yi ta É—aure ruwa. Galibi É—aurin ruwa kan Æ™unshi addu’a ta surkulle,
inda ake haÉ—a harshen Larabci da na Hausa da na Dandanci[6]. Ire-ren waÉ—annan addu’o’i na surkulle, ba su faye
wata cikakkiyar ma’ana ba. Bisa misali akwai wata addu’a da ake karantawa Æ™afa bakwai. Daga nan za a É—ebi ruwan tafki ko gulbin da ake son a É—aure, a moÉ—a ta Æ™warya. Guntsar ruwan za a yi a baki,
sannan a furza shi cikin ruwan da za a É—aure. Daga nan sai a sami tsumangiya ta
itacen tumfafiya, a doki ruwan da ita har sau uku. Ana yin haka, sai bai wa
masunta dama su bazama cikin ruwan domin neman abinci. Ga yadda addu’ar take:
Bismillahi! Ai salam dabiga. Annabi
salam makwaiga.
A yi nutan badago, baki gunÉ—e.
Mai dogon baki bai cizon mu.[7]
Idan aka kalli kalmomin Hausa da suke cikin addu’ar, ana
iya fahimtar cewa addu’ar ta fi dacewa da É—auri ne ga kada, domin yana É—aya daga cikin halittun ruwa masu dogon baki, da sukan
kasance barazana ga masunta, musamman waÉ—anda ba su shahara ba.
3.1.2 Riga-Kafin shafar iska
Bahaushe yana da cikakkiyar fahimtar cewa ruwa mazauni ne
na Iska. Ruwan ka iya kasancewa na kogi ko tafki ko kududdufi. Daga cikin nau’o’inau’o’in
Iskoki da suke da mazauni a cikin ruwa akwai Harakwai da Hajaruwa da Jittakuku
da Tamashaya da dai sauran su. WaÉ—annan Iskoki mazauna ruwa kan cutar da mutane, musamman masu shiga ruwa ko dai domin kama kifi ko wanka ko kurme. Sarkawa su ne
malaman ruwa, su suka san ciki da bai na ruwa da abin da ya ƙunsa. A kan haka ne sukan ba da taimako
na magani domin riga-kafi ga cutar shafar Iskar ruwa. Misali
na maganin riga-kafin Iska da suke bayarwa shi ne a sami ɗanyen ƙayar itaciyar aduwa guda ɗari ba ɗaya (99). A sanya shi cikin turmi za a yi
sai a saɓa shi, daga nan a shanya ya bushe.
Bayan ya bushe, sai a dake shi ya zama gari. Wannan garin ne za a riƙa ɗiba a duk lokacin da za a yi wanka, sai
a zuba cikin ruwan, a yi wanka
da shi.[8] Falsafar amfani da ƙayar aduwa wajen yin riga-kafi shi ne cewa ana amfani da
ita wajen yin shinge domin yin kariya da keɓance wani wuri da ba a son a ratsa ko a shiga. Yadda ƙayar aduwar take hana a ratsa wuri,
haka za ta hana Iska, ta katange shi daga shafa ko shiga jikin wanda ya yi
wanka da maganin.
3.1.3 Riga-Kafin ƙaya da dafinta
Ƙaya[9] na nufin ƙashin da ake samu a jikin kifi. Daga
cikin nau’o’in kifi da ake samu a ruwa na Ƙasar Hausa, karfasa ko gargaza kusan ta fi kowane kifi
yawan ƙaya. Sau da dama, tsautsayitsautsayi na
iya kamawa, ƙaya ta maƙale wa mutum a maƙogwaro yayin da yake cin kifi. Sarkawa
suna yin riga-kafi na addu’a domin samun kariya daga haÉ—arin maÆ™alewar Æ™ayar kifi. Gabanin cin kifi, musamman
gargaza ko karfasa, ana karanta wannan addu’a domin yin kandagarki. Addu’ar ita
ce:
Bismillahi! Tallakum
Bi hadimakum, danhwatsobiru.[10]
3.2 Ceto da agajin farko ga wanda ya faÉ—a ruwa
Duk lokacin da wani ya faÉ—a ruwa, Sarkawa ake nema su nemo shi kuma su ba shi
agajin farko. Idan haÉ—arin bai daÉ—e da aukuwa ba kuma ya kasance ba a yi kuka ba yayin da
aka fahinci mutum ya nutse a ruwa, Sarkawa kan yi masa tawada tare da hayaƙin magani. Cikin yardar Allah, ana yi
ana matsa cikinsa sannu a hankali, sai a tarar ya farfaÉ—o. Ba wannan kaÉ—ai ba, idan aka sami haÉ—ari na kifewar kwalekwale ko jirgin fito, Sarkawa ne suke
bazama cikin ruwa domin kuɓutar da mutane. Waɗanda suka mutu kuwa,Sarkawan ne dai ke nemo gawarwakinsu
domin yi masu sutura da jana’iza. Wannan zai hana su ruÉ“ewa a cikin ruwan, wanda hakan zai kare shi daga gurÉ“ata. Wani lokaci, idan aka sami kifewar kwalekwale a
tsakiyar gulbi mai zurfin gaske, Sarkawa na da wata waibuwa ta rage zurfin
ruwa. Sukan iya bai wa mutane umurni su tashi tsaye ko da a
wuri mai zurfin gaske ne. A irin haka, ruwan ba zai wuce iya cibiyar mutane ba.
Suna yin irin wannan waibuwa ne domin kuɓutar da rayukan mutane yayin da aka
sami mummunan hatsari lokacin sufuri ko fito tsakanin wannan mashaya zuwa
waccan ko kuma daga wannan gaɓar kogi zuwa wancan.
3.2 Magungunan waraka
Akwai cututuka da dama waÉ—anda Sarkawa suke taimakawa wajen bayar da magungunan da
za a yi amfani da su domin samun waraka. Galibi, cututukan da suka jiɓinci ruwa, wato waɗanda ake kamuwa da su sakamakon yawaita
shiga ruwa, Sarkawa kan bayar da taimako domin warkar da su. Dalili kuwa shi
ne, a koyaushe, a ruwa wajen neman abincinsu yake. Su ne masana ruwa ko malaman
ruwa. Cututukan da suke bayar da maganinsu sun haɗa da cutar sanyi da ciwon ciki da ciwon ƙaiƙayin jiki da ake ɗauka sakamakon shiga gurɓataccen ruwa da maganin Iska da maganin cutar maroƙi da maganin cizon kifi da dai sauran
su.
3.2.1 Maganin cutar sanyi
Ciwon sanyi wata damuwa ce da take raunana lafiyar mutum
sakamakon ciwon da ake É—auka ko kamuwa da shi sakamakon yawaitar
shiga ruwa, ko yin sammako a jeji lokacin damina, musamman lokacin da ake samun
raÉ“a sosai. Ana kuma É—aukar cutar sanyi sakamakon yin lalata ko jima’i da mace
ko namijin da ya harbu da ciwon. (Fadama, 2015 p. 456) Ta la’akari da wannan
bayani, ana iya cewa cutar sanyi ta kasu nau’i biyu. Akwai cutar sanyin fadama
da kuma cutar sanyin mata. Kowane daga cikinsu, Sarkawa na bayar da taimako. Magungunan
sanyi da suke bayarwa domin samun waraka daga cutar sanyi suna da matuƙar yawa. A wannan muƙala, za a kawo misali ɗaya na maganin. Misali na wani taimako na cutar sanyi da
suke bayarawa shi ne:
A nemi sayyun bishiyar gawasa, sai a wanke shi sosai
domin a cire ƙasa da ke tare da shi. Haka ma za a ɗebi sayyun magarya, a wanke shi domin cire ƙasar da ke jikinsa. Za a ɗora ruwa a tukunya sai a haɗa maganin tare da jar kanwa. Idan aka sauke maganin ya
huce, sai sha moÉ—a É—aya, bayan an ci abinci da safe. Da
yamma ma, sai a sha moÉ—a É—aya bayan cin abinci.[11]
3.2.2 Maganin fitar baya/dubura
Wani lokaci, idan cutar sanyi ta yi yawa a jikin mutum,
takan haddasa fitar baya, yayin da aka ziyarci ban ɗaki domin yin bayan gari. Dalili kuwa shi ne akan ɗauka cewa cutar ta sanyi tana sa bushewar ciki, a riƙa shan wahala wajen yin bayan gari. A
riƙa yin sa kamar ɗiɗɗira, wato atini. Sakamakon yawan yunƙuri, baya sai ta riƙa fitowa. Wasu Sarkawa suna bayar da
taimako na irin wannan lalurar. Abin da ake yi shi ne a sami tsiron duman kada.
Za a saka shi a tukunya a dafa shi sosai sai ya gisÉ—u. Za a sauke tukunya, a juye tafasasshen ruwan a wani
baho. Akan bar shi ya ɗan huce kaɗan. Lokacin da zafinsa ya ragu ta yadda ba zai ƙona jiki ba, sai mai fama da wannan
rashin lafiya ya zauna a cikin bahon. Zafin maganin yana kai ga duburarsa. Haka
za a yi riƙa yi safe da yamma har sai an sami sauƙi.[12] Idan an yi maganin na ɗan lokaci abin bai ja da baya ba, ana iya ƙara ganyen iccen kalgo a cikin haɗin. Za a tafasa kamar yadda aka tafasa duman kadan. Idan
ya rage zafi, sai a zauna cikin ruwan har ya huce. Za a yi hakan safe da yamma
har sai an sami biyan buƙata.
3.2.3 Ciwon ciki
Sarkawa sun yarda da cewa akwai nau’i na ciwon ciki da
cutar sanyi take haddasa shi. Irin wannan ciwon cikin, ko an sha maganin ciwon
ciki da aka saba da shi yau da kullum, ba za a sami waraka ba, har sai an
magance musabbabinsa, wato ciwon sanyi. A irin wannan, ana samun saƙe-saƙin zogale, sai a jiƙa shi a cikin ruwan tsagwaro ko tsari.
Idan ya jiƙa, mai fama da cutar zai riƙa sha safe da yamma har tsawon kwana
bakwai. Wannan zai sa duk sai an fitsare cutar sanyi da take a marar mai fama
da cutar. Wannan kuma zai sa a sami waraka daga ciwon cikin.[13]
3.2.4 Cutar sanyin ƙashi
Cuta ce da take kama ƙashi, a riƙa fuskantar zogi da raɗaɗi a daidai inda cutar ta kama. Wani
lokaci idan a ƙafa ne, sai tarar a mai fama da ciwon
yana É—ingishi a yayin da yake tafiya.
Magungunan da Sarkawa suke bayarwa domin magance cutar suna da yawa. Misali É—aya shi ne za a sami ganyen itacen malga, sai a tafasa
shi sosai a tukunya. Idan ya gisÉ—u, sai a sauke, a kuma yi surace da
maganin. Ana son a yi lulluɓi yayin da ake yin surace da maganin.
Haka za a riƙa yi safe da yamma, har zuwa yaushe?.[14]
3.3.5 Cutar ƙaiƙayin jiki
Mutane masu yawan shiga ruwa kan kamu da cututukan fatar
jiki. Daga ciki, akwai ƙaiƙayin jiki wanda akan kamu da shi sakamakon shiga ruwan da
ya gurɓata da datti kamar na ruɓaɓɓun ganyaye, da hakukuwa da gawarwakin
dabbobi da ake jefarwa a ciki. Galibi an fi samun wannan matsala a ruwan da ba
ya gudu, kamar na tafki da kududdufai. Idan yara suka shiga wannan ruwa domin
yin kurme, suna iya kamuwa da cutar ƙaiƙayin jiki. Masu kama kifi a irin wannan
ruwa ma suna iya fuskantar matsalar ta ƙaiƙayin jiki. Sarkawa suna bayar da
taimako domin magance wannan damuwa. Daga cikin magungunan da Sarkawa suke
bayarwa, akwai ganyen sabara. Za a saka a turmi a kirɓa shi sannan a shanya, Idan ya bushe, sai a sake daka shi
sosai har ya zama gari. Garin nan za a riƙa ɗiba ana zubuwa a moɗa tare da kunu ko koko ko fura. Sau biyu za a sha
maganin, safe da yamma. Garin maganin ba ƙaiƙayin jiki kaɗai yake magancewa ba, ana amfani da shi wajen maganin
samiha.[15]
3.3.6 Maganin ciwon maɗiga da haƙarƙari na ƙananan yara
Wasu yara sukan fuskanci ciwon maɗiga inda za su riƙa yin rama da masifar kuka koyaushe. Akan sami ƙwallon kansu ya yi wani layi, maɗigar kuwa sai ta ɗan lutsa ciki kaɗan.Waɗaansu na kiran irin wannan damuwa da
suna ‘kai’. Ciwon haÆ™arÆ™ari ma abu ne da kan addabi Æ™ananan yara. Masu fama da ciwon za a ga
suna nunfashi da wahala sosai kuma haƙarƙarinsu su riƙa motsawa da sauri yayin da suke
numfashin. Wasu Sarkawa suna da fahimtar cewa sanyi ne yakan haddasa ciwon haƙarƙarin. Akwai taimako na magani da suke bayarwa domin samun
waraka daga damuwar. Ana samun É—anyen tafarnuwa tare da kan ramboshi.[16] Za a daka waÉ—annan abubuwa biyu a turni. Yayin da
aka dake su, za a ga kamar an kwaɓa su saboda sanyin da ke ga tafarnuwar.
Haɗin ne za a riƙa shafa wa mai fama da ciwon a daidai
wurin maɗigarsa. Mai ciwon haƙarƙari kuwa, za a riƙa shafa masa a daidai haƙarharin, safe da yamma, musamman
lokacin da za a shiga barci.[17]
3.3.7 Maganin cizon kifi ko kada
A halittar kifi da yake rayuwa a ruwa, ana samun wasu nau’o’i
da suke cuta wa mutane ta hanyar cizo. Kifayen nan da ake kira yauni, da zawai
da kuma boÉ—ami ko gawo, wani babban misali ne. Irin
waÉ—annan kifaye masu cizo, galibi za a
tarar cewa jikinsu ba ya da wata ƙaya mai ƙwari, wadda za su riƙa amfani da ita domin kare kansu daga
abokan gaba. Don haka a madadin ƙaya, suna amfani da haƙoran da ke cikin bakinsu domin su kai
farmaki. Tare da su, akwai kuma dabbobi na ruwa, kamar kada, da ka iya yin cizo.
Cizon irin waÉ—annan kifaye, musamman yauni, yakan yi
illa matuƙa. Tana iya katse wa mutum yatsa ko ma
al’aura, idan tsautsayi
ya zo da haka. Wani lokaci, cizon nata ka iya sa mutum ya sandare, ya zamana gaɓoɓi ba sa lanƙwasawa balantana wani dogon motsi.
Idan haka ta faru, Sarkawa na bayar da taimako na magani
ta hanyar yin tawada da kuma yin turare ko hayaƙi na magani, wanda galibi sayyu da
ganyaye na itatuwa.[18]
3.3.8 Maganin sukar ƙayar kifi
Kifi halittar ruwa ce da take amfani da ƙayoyin da ke jikinsa domin yawatawa a
cikin ruwa da nufin neman abinci. Baya ga amfani da ƙayar wajen yawatawa, ƙayar kan ba shi kariya daga farmakin
abokan gaba. Da ƙayar ne yake kai farmaki ga abin da
yake yi masa barazana. Waɗansu kifayen, suna da ƙaya mai ƙwari a gefen kumatunsu. Da wannan ƙayar ne suke sukar wanda ya farmake su.
Misalin kifaye masu wannan ya haɗa da tarwaɗa da hana noma da harya[19]. Akwai kuma waɗanda ko baya ga ƙayar ta kumatu, suna da wata ƙayar mai ƙarfi a sashen gaba na doron bayansu.
Misali a nan shi ne ƙaraya ko ƙurungu. Sukar da kifayen kan yi, takan
yi tsanani matuÆ™a. Akwai waÉ—anda idan suka soki mutum, sukan sakar masa zazzaÉ“i sosai. Nau’in tarwaÉ—an nan da ake kira hana noma, sukar sa na illa matuÆ™a. Sarkawa sun tabbatar da cewa idan
mutum ba yana da magani ba, sukar wannan kifin ka iya hana mutum yin noma a
wannan shekarar, saboda tsananin wahalar da zai sha fama da ita, sakamakon
cizon.
Sarkawa kan ba da taimako na magani ga wanda wannan
lalura ta shafa. Galibi addu’o’i na surkulle ake yi ana tofawa inda raunin
yake. Wani lokaci Æ™asa ta ruwan da kifin ya yi suka ake É—iba, a yi addu’a, sannan a shafa wurin da rauni yake.
Idan abin ya yi tsanani, akan haÉ—a da sayyu da ganyayen da za a dafa a
sha ko a yi farsa a inda rauni yake. Misali na wata addu’a da wasu Sarkanwa kan
yi wa wanda kifi ya soka ita ce:
Bismillahi! Sama ba ta ƙaba, ƙasa ba ta ƙaba.
Hakin kifi ba ya sa ƙaba da ikon Allah.[20]
3.3.9 Cire ƙayar kifi kai tsaye
Wani lokaci, tsautsayi kan sa ƙayar kifi ta laƙe a dasashi ko a maƙogwaraon mutum, yayin da yake cin kifi.
Idan irin wannan ya faru, mutum kan shiga wani hali, ya rasa sukuni, yawu yana
zuba daga bakinsa, ba tare da yana so ba. Idan haka ta faru kuwa, Sarkawa suna
cire Æ™ayar kai tsaye. Wani lokaci, addu’a suke yi a tofa ga ruwa ko wani abinci
da ake iya haÉ—iyewa, sai a ba wa mai matsalar ya haÉ—iye. Akan kuma yi addu’ar a tofa ga hannu, sannan Basarke
ya shafa inda ake jin nan ne Æ™ayar take. Addu’o’in dai na surkulle ake yi, inda ake haÉ—a kalmomin Larabci da suka jiÉ“inci AlÆ™ur’ani mai tsarki, da kuma kalmomin Hausa ko Dandanci.
Misalin wata addu’a da suke yi ita ce:
Bismillahi! Mawu kam sakin.
Ma sakin, sarirun masat.[21]
3.3.10 Maganin gyambo
Gyambo ciwo ne mai fitar da mugunya, musamman a Æ™afar mutum, wanda ya daÉ—e bai warke ba.[22] Wato ma’ana, miki a jikin Æ™afar mutum da aka samu sakamakon rauni
da aka yi bisa tsautsayi na wani haɗari ko wani ƙurji da ya fito a ƙafar mutum, ya kasance ya daɗe bai warke ba. Irin wannan ciwon yana da wuyar warkewa
matuƙa. Wasu daga cikin Sarkwa suna
bayar da taimako na magani domin warkar da ciwon. Domin yin maganin, ana haÉ—a abubuwa kamar haka:
a.
Ana karkaro ƙasa ta inda almajiran makarantar allo
suke wanke allunansu
b.
A sami matsattseku a shanya ta bushe
c.
A sami zuciyar kifaye, mulgi da ramboshi a shanya su
bushe
Bayan sun bushe, sai a dake su, sai sun zama gari.
Koyaushe, sai a sami ruwa mai kyau, a riƙa wanke mikin da shi. Bayan an wanke, sai barbaɗa garin maganin a jikin gyambon. Haka za a riƙa yi kullum da safe, har sai an sami
biyan buƙata.[23]
3.3.11 Maganin fuka
Fuka wata damuwa ce ko cuta da take kama huhun mutum ta
yadda zai riƙa yawan yin haki da numfashi a
wahalce. Galibi Sarkawa sukan É—auka cewa sanyi idan ya tsananta yakan
shafi huhun mutum ta yadda za a riƙa yin haki. Sukan bayar da taimako na
magani domin samun waraka daga cutar. Maganin kuwa shi ne ana samun wani kifi
da suke kira ƙazagge[24]sai a shanya shi ya bushe. Duk lokacin da mai fama da
cutar ya ji alamar ta, sai ya ɗauko kifin nan ya jiƙa a moɗa. Idan ta jiƙa, sai ya cire shi ya sake shanyawa. Ruwan kuwa sai ya riƙa kurɓa shi sannu- sannu, yana haɗiyewa. Haka zai riƙa yi har ya sami sauƙi.[25] Idan kuwa aka ga ciwon ya tsananta, sai a sami huhun
kada. Shanya shi za a yi ya bushe. Duk lokacin da aka ji mai wannan rashin
lafiya, ana jiƙa huhun kada. Idan ya jiƙa sai a cire shi daga ruwa, a sake
shanya shi. Ruwan kuwa, mai fama da cutar zai riƙa shan sa a kai- a kai, sai an sami
waraka.[26]
4.0 Sakamakon bincike
Sarkawa suna bayar
da gagarumar gudunmuwa a sha’anin kiwon lafiya na gargajiya a Æ™asar Hausa, tun gabanin Æ™asar ta Hausa ta sami haÉ—uwa da kowace irin al’ada daga Æ™etare. Tattaro wasu daga cikin
magungunan gargajiya da Sarkawa suke bayarwa domin kwantar da ko samun waraka
daga cututka da suke takurawa al’umma, a tunanin wannan muÆ™ala, wani babban alheri ne. Wasu daga
cikin magungunan nan, saiwoyi ne ga ganyaye da saƙe-saƙin itatuwa haɗe da wasu ganyaye. Tattaro su da aka yi aƙalla tamkar taskace su ne aka yi. Hakan
ba ƙaramin taimakawa zai ba yi wajen adana
wannan muhimmiyar al’ada. Salwantarsu kuwa, ba Æ™aramar hasara ba ce ga al’ada ta
Hausawa.
Wannan muƙala ta daɗa fito da magungunan gargajiya a sarari, da yake abin da
ya shafi magani a al’ada ta Bahaushe, abu ne na sirri. Akan yaÉ—a shi daga iyaye zuwa ‘ya’ya da jikoki. Ko a hakan ma,
sai É—a ko ‘ya’yan da suka yi biyayya, suke
rabauta a sanar da su wannan ilimi. A halin yanzu kuwa, wannan ilimi na
magungunan gargajiya yana fuskantar barazana ta salwanta, musamman idan aka yi
la’akari da cewa waÉ—anda suke da ilimin tsofaffi ne. Wanda
duk Allah ya karɓi rayuwarsa, shi ke nan ya tafi da iliminsa.
WaÉ—anda suke raye kuwa, sun yi hasara.
Wannan muÆ™ala ke nan ta zama ma’adani na wannan al’ada.
5.0 Kammalawa
Sha’anin kiwon lafiya na gargajiya aba ne da masu aiwatar
da sana’o’in gargajiya suke da ruwa da tsaki wajen aiwatar da shi a tsakanin
al’ummar Hausawa. Kamar yadda wannan muÆ™ala ta fito da shi a fili, an ga irin gagrumar gudunmuwar
da Sarkawa suke bayarwa ta wannan haujin. Idan lura da kyau, za a fahimci cewa
magungunan da suke bayarwa sun ƙunshi abubuwa uku a jimlace. Na farko akwai
amfani da saiwoyi da ganyaye da kuma saƙe-saƙin itatuwa daban-daban. Na biyu akwai
addu’o’i da suke yi domin neman sauÆ™i ko waraka daga cuta ko damuwa. Na uku
kuwa akwai sassan kifaye da wasu halittu na ruwa da ake sarrafawa domin magance
matsalar cuta. WaÉ—annan duka, an ga yadda suke sarrafa su
domin biyan buƙata.
Ra’ayin wannan muÆ™ala shi ne a ce, masana ilimin zamani da kan haÉ—a magunguna, su zurfafa bincike na kimiyya domin gano
sinadaran da saiwoyi da ganyaye da aka kawo suka ƙunsa. Hakan zai sa a haƙiƙance alfanunsu wajen warkar da cututukan da aka ce suna
yi. A kuma gano ƙima da adadin maganin da ya dace a sha
domin a sami biyan buƙata. Yin haka zai ƙara sauƙaƙa kiwon lafiya, da kawo shi kuwa ga masu buƙata.
Manazarta
Abubakar, A.T. (2015). Ƙamusun
Harshen Hausa.
Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Ltd
Alkali, M.B. (1969) “A Hausa Community in Crisis: Kebbi in the
Nineteenth Century.” M.A. Thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Bargery, G.P. (1993). A Hausa-English Dictionary and English- Hausa Vocabulary (2nd
Ed.) Zaria: Ahmad Bello University Press.
Bunza, A.M. (1995). “Magani A Rubuce: Nazarin
Ayyukan Malaman Tsibbo.” Kundin Digirin Ph.D Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A.M. (2006). Gadon FeÉ—e Al’ada Lagos: Tiwal Nigeria Ltd.
Bunza, A.M. (2008). Hausa Medicine:
Its Relevance and Development in Hausa Studies. The Second
Inaugural Lecture. Usmanu ÆŠanfodiyo University, Sokoto. Lagos: Ibrash Islamic
Publications Centre Ltd.
CNHN, (2006).
Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.
ÆŠandume, M. (1995). Magani
da Itatuwa da Addu’o’i. Funtua: Himma Press.
Fadama, M.G. (2015) “Sarkanci A
Gundumar Sakkwato” Ph.D Thesis, Sokoto: Usmanu ÆŠanfodiyo University.
Sarkin Gulbi, A. 2014: "Magani a Ma'aunin Karin
Magana" Kundin Digiri na uku, Sakkwato, jami'ar
Usmanu Danfodiyo.
Sa’id, B. (1997).
“Kwatanci-FaÉ—i: Tasirin Harshe A Tsibbun Bahaushe.” cikin Harsunan
Nijeriya Vol.xviii CNHN, Kano: Bayero University.
Shehu, M. (2013).
“Dabbobon Ruwa A MahaÉ—in Magungunan Gargajiya” MuÆ™alar
Da Aka Gabatar Sashen Harsunan Nijeriya, Sokoto:Usmanu ÆŠanfidiyo
University, Alhamis, 28/02/13.
Wara, M.A. (2019). “The Sorko Expansion in the
Waters of the Niger to the End of the 20th Century” in Annals of Global Vol. 1, Issue 1, PP
1-6.
[1]
Farfesa Bunza, A.M. 1995). “Magani A
Rubuce: Nazarin Ayyukan Malaman Tsibbo.” Kundin Digirin Ph.D. Kano: Jami’ar
Bayero. Shafi na 48.
[2]
Daidai da tushen bayani na 1
[3]
Duba Bunza, A.M. (2009) HAUSA MEDICINE: Its Relevance and Development in Hausa Studies. The Second Inaugural Lecture, Usmanu ÆŠanfodiyo
University Sokoto. Lagos:Ibrash Islamic
Publication Centre Ltd shafi
na 77
[4] CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Shafi na 450.
[5]
Health care-Wikipedia
en.m.wikipedia.org
[6]
Dandanci wani karin harshe na
Zabarmanci. A ruwaitowar Fadama, (2015:169) daga Alkali, (1969:31) cewa
ya yi Dandawa mutane ne da suka shahara a wajen tsafi da kuma bautar
Iskoki kamar Godakasa da Barkasa da Gwaragwa. A wurin dandawa, bori abu ne da
aka bai wa muhimmin matsayi
don kuwa kusan duk abin da za a yi, sai an tuntuɓi Iskoki
kafin a fara shi. Dandawa sun
shahara a sha’anin Sarkanci
[7]
Hira da Sarkin Ruwan Gyalange, Ƙaramar hukumar
mulkin Gummi, jihar Zamfara. Talata, 28 ga Fabrairu, 2023.
[8]
An sami wannan bayani ne daga Mairuwa
Bala Barga na garin Barga, ƙaramar hukumar mulkin Tambawal, jihar Sakkwato.
[9]
Sarkawa bias ala’ada ba sa kiran Æ™ayar kifi da sunan
ƙaya. Hakin kifi
suke kiranta domin al’adar nan ta tada da suke da ita. A wurinsu Æ™aya tamkar haki
take domin yadda haki ba ya da ƙwari da ƙarfi, haka ƙaya take a wurinsu.
[10]
Hira da Basarke Umaru Manu Gayari, ƙaramar hukumar
mulkin Gummi, Jihar Zamfara. An haÉ—u da shi a Yauri,
a wasu shekarun baya, 2012.
[11]
An sami sami wannan bayani na tushen
magani daga Fadaman Ƙurfa, Fadama Auwal. Ƙurfa tana cikin yankin Gayari na ƙaramar hukumar
mulki ta Gummi, jihar Zamfara. An yi hira da shi a gidansa da ke Gayari, ranar
23 ga Disamba, 2022.
[12]
Hira da Fadama Sa’idu, Fadaman Gummi, Æ™aramar hukumar
mulki ta Gummi, jihar Zamfara, ranar 12/9/2022.
[13] Hira da Alhaji Maibirgi Falam Birni, Ƙasar Gayari, ƙaramar hukumar
mulki ta Gummi, jihar Zamfara, An yi hira da shi a ƙofar hakimin Falam Birni, Jano, ranar
Asabar, 17 ga Disamba, 2022.
[14] An sami wannan bayani a wajen Sahabi Ƙardaji, yankin
Falale, ƙaramar mulki ta
Gummi. Ni ma na tarar da ana ba da wannan taimako a gidanmu, yayin da mahaifina
yake raye.
[15] An sami bayanin wajen Sahabi Ƙardaji na yankin Falale, ƙaramar hukumar
mulkin Gummi, jihar Zamfara.
[16] Ramboshi wani nau’i ne na kifi da ya yi kama da tarwaÉ—a amma ya fi tarwaÉ—ababban kai kuma jelarsa tana da launi jajaja. Yana da
wata heta a gadon bayansa mai kama da tozo. Gashin bakinsa ya É—ara na tarwaÉ—a tsayi
[17] Hira da mairuwa Bala Romo, ƙasar Tambawal, jihar Sakkwato.
[18] Hira da Danbuga Mairuwa Kebbe, jihar Sakkwato. Ya shahara
matuƙa wajen bayar da
irin wannan taimakon.
[19] Wannan kifi har kirari Sarkawa kan yi masa da “ÆŠan harya alhajin ‘yan suka.”
[20] Hira Sarkin ruwan Gyalange, Alhaji Hamidu Gyalange, ƙaramar hukumar
mulkin Gummi, jihar Zamfara.
[21] Hira da Sarkin Ruwan Gyalange, Alhaji Hamidu.
[22] CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero Shafi na 185.
[23]
An sami wannan bayani ne wajen Mairuwa
Bala Romo, Romon Sarki, ƙaramar hukumar mulkin Tambawal, jihar Sakkwato.
[24] Ƙazagge wata gargaza ce da ta faye girma
ba. Komai daÉ—ewarta, ba ta
girma sosai.
[25] Hira da Homan Argungu, Alhaji Muhammadu Bashar Argungu.
[26] Hira da Basarke Muhammadu Ɗanmaiyaƙi Ndalada, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.