𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Yaya matsayin mutumin da yake azumi kuma sai yasha ruwa kafin a kira sallah Amma kuma lokacin shan ruwan ya yi magariba tayi, Sannan idan na yi kurkurar baki na yi shakar hanci sai in dinga ji kamar ruwan ya shigemin ta maƙoƙaro sannan idan ban yi da yawaba sai in dinga ji kamar be yiwuba malam dan Allah ya zan yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To bayin Allah daman Allah maɗaukakin sarki cewa
ya yi mu cika azumi izuwa dare kamar yadda aya ta 187 ta cikin suratul Baƙara ta yi bayani. Shikuma dare yana farawa daga lokacinda
rana ta faďi wannan ita ce fahimtar dukkan malamai ahalussunnah. Sabida haka
lokacin shan ruwa ga me azumi yana farawa daga sadda rana ta faďi, ke nan
matukar dai rana ta faďi mutum yasha ruwan to azuminsa ya yi in Shã Allahu koda
kuwa masallacinda yake kusa da su basu kira sallah ba.
Ba sharadi bane koda rana ta faďi kuma a ce dole sai an kira sallah sannan
mutum zaiyi buďa baki, a'a sharaďin kawai shi ne faďuwar ranar, domin idan ance
dole sai an kira sallah sannan mutum zaisha ruwa koda kuma ranar ta faďi to
mutuminda yake cikin jeji ba zai sha ruwa ba ke nan hakanan wanda baya kusa da
masallaci shi ma ba zai sha ruwan ba ke nan, kunga kuwa hakan akwai cutuwa
domin wani a inda yake idan za a kwana ba lallai yaji kiran Sallah ba. Sabida
haka da faďuwar rana ake la'akari wajen shan ruwa ga mai azumi matukar dai ya
tabbata cewa ranar ta faďi to idan yasha ruwa azuminsa ya yi koda ba akira
sallah ba.
Dangane da kurkurar baki da sha'ka ruwa Annabi ﷺ
ya umarcemu da yin alwala yadda ya kamata sai dai ya hanamu kaiwa makura wajen
shakar hanci da kurkurar baki yayinda muke azumi kamar yadda Tirmizi da Abu
Dawud suka rawaito. Sabida haka idan mutum yana azumi ba ason yakai makura
wajen kurkurar baki da sha'ka ruwan sabida gujewa zarcewar ruwan zuwa makogaro
ga mai azumin, Sabida haka sai a nisanci kaiwa makura a yayinda ake azumin Amma
wanda ya yi hakan abisa rashin sani bada ganganciba to azuminsa ya inganta in
Shã Allahu matukar ya kiyaye aukuwar zarcewar ruwan gwargwadon ikon sa. Sannan
kuma idan mutum ba azumi yake ba ana son ya sanya ruwa a cikin hancinsa sosai
gwargwadon yadda ba zai cutu ba
WALLAHU A'ALAM
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GlolWn2ocAj0vaFZxHKhbL
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.