Ma’anar zakkah a shari’ah ita ce:
Fitar da hakkin daya wajaba daga dukiya yayin da takai nisabi ga waÉ—anda
suka cancanta.
Zakkah rukuni ce daga cikin rukunan Addinin Musulunci kamar yadda ya zo a
Hadisi:
Zakka ta kasu gida biyu:
1• Zakkah ta jiki (Wato zakkar fidda kai), bayaninta zai zo a nan gaba
2• Zakkar Dukiya.
DALILAN WAJABCINTA
Zakka wajibi ce da nassin AlÆ™ur’ani, kamar yadda AlLLAH (S.W.T.) Yace: Ku bayar da Zakkah.
[Al Bakara Ayata: 110].
Manzon ALLAH {s.a.w} Yace: Da Mu’azu sanda ya tura shi Yemen:
Ka sanar da su cewa ALLAH {S.W.T} Ya wajabta Zakka a kansu, wadda za a karɓa
daga mawadatansu, a bayar da ita ga matalautansu.
[Bukari da Muslim]
WAÆŠANDA TA WAJABA A KAN SU
Malamai sun haÉ—u a kan cewa zakka tana wajaba a kan
Musulmi baligi mai hankali.
Kuma wanda ya mallaki nisabi, tare
da cika sauran sharuɗa, amma sun yi saɓani
a kan yaro da mahaukaci.
Wasu sunce bata wajaba a kansu ba, wasu kuma sukace tana wajaba.
Amma magana ta biyu ita tafi ƙarfi,
saboda hadisai ingantattu da aiwatarwar sahabbai a kan haka.
Anas (R.A) yace:
Manzon ALLAH {s.a.w} yace:
Kuyi ciniki da dukiyar marayu, domin kada Zakka ta cinye ta.
[ÆŠabarani ya
rawaito].
[Duba FiKhuz Zakkat juz’i na 1, shafi:95 – 112].
Wannan ya nuna cewa za a fitar da Zakka daga dukiyar yaro data mahaukaci.
LOKACIN FITAR DA ZAKKA
Lokacin fitar da zakka ya danganta ne da nau’in dukiyar.
Idan zakkar kuÉ—i da dabbobi, da kayan sayarwace, to
sai dukiyar ta shekara, bayan ta kai nisabi.
Amma idan zakkar amfanin gonace, to ana fitar da itane a lokacin da aka
girbe ta ko aka tsinke ta.
Zakkar ma’adanai data zuma kuwa, a
wajen mahzahar Hanafiyya, ita ma ana fitar da ita a yayin da aka fito dasu.
(Duba FiKhul Islami Wa Adillatahu,
juz’i na 3, shafi: 1814 – 15)
SHARADAN WAJIBCIN TA
Dangane da abin da ya gabata, zamu fahimci cewa, tsabar kuÉ—i
da kayan sayarwa suna buƙatar
sharuÉ—a biyar kafin a fitar musu da Zakka.
1• Musulunci.
2• 'Ƴanci.
3• Mallaka.
4• Cikar Nisabi.
5• Cikar shekara.
Idan kuwa Zakkar dabbobi ce, to, sai a ƙara sharaɗi daya, shi ne:
kasancewa suna fita kiwo.
Ba aÉ—aure suke ana nemo musu abinci ba,
wato waÉ—anda ba atirkesu ba.
Haka kuma idan amfanin gonane, to shi ma sai a ƙara sharaɗi ɗaya,
wato ya kasance abinci ne ga É—an Adam, amma a
fitar dashi ne da sharaÉ—in cikar shekara.
[Duba Al-FiKhul Muyassar na Ahmad Isa, juz’i, 1, sh;220-222]
HUKUNCIN WANDA YAƘI
BAYAR DA ITA
Mai ƙin fitar da zakka
iri biyu ne:
1• Kodai yaÆ™i
bayarwa ne saboda bai yarda wajibi ce ba.
2• Ko kuma yaÆ™i
bayarwa ne saboda tsananin rowa da son abin duniya.
Idan yaƙi bayarwa ne
saboda bai yarda da wajibcinta ba, to ya kafirta.
Idan kuwa don rowa ne, ko sakaci to fasiƙi ne, kuma hukuma za ta iya karɓa
ta ƙarfi daga
garesshi.
Kamar yadda Khalifan Manzon ALLAH {s.a.w} Abubakar (RA) ya yaƙi waɗanda sukaƙi bayarwa a zamaninsa.
[Duba za katul Ma’adni na Almukhtar bin Umar bin Al-Hussain As-Shankidi
Sh:18-19].
Kuma ya kamata mu sani cewa, ƙin
bayarda zakka yana jawo azaba mai muni ga mutum a lahira.
Abu Huraira (RA) yace:
Manzon ALLAH {s.a.w} yace:
Babu wani mai k'dukiya wanda baya bayar da zakkarsa, face sai an ƙona kuɗin a wutar
Jahannama ya yi faɗi sannan a rinƙa manna masa a geffansa da fuskarsa, har lokacin da ALLAH
zaiyi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawon shekara
dubu hamsin.
Sannan a nuna masa hanyarsa, ko dai zuwa aljannah ko kuma zuwa wuta.
Babu wani mai raƙuma
wanda baya bayar da Zakkarsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai
faɗi cike dasu, sannan su rinƙa bi ta kansa,
Idan suka kai ƙarshe,
sai a dawo da na farkon, H'haka za a rinƙa
yi masa, har ALLAH ya yi hukunci a tsakanin bayinsa.
A yinin da yake kwatankwacinsa tsawon shekara dubu hamsin.
Sannan sai a nuna masa hanyarsa izuwa Aljanna ko zuwa wuta.
Babu wani mai tumaki ko awaki wanda baya bayar da zakkarsu, face sai an
jefashi a cikinsu, a wani kwari mai faÉ—i, cike da su sannan
su rinƙa takashi da
kofatansu, suna sukansa da ƙahonsu.
Babu mai tanƙwararren
ƙaho a cikinsu,
balle marar ƙaho, idan suka kai
ƙarshe, sai a dawo
dana farkon.
Haka za a rinƙa
yi musu, har ALLAH ya yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake
kwatankwacin tsawonsa shekara dubu hamsin.
Sannan sai a nuna masa hanyarsa zuwa Aljanna ko zuwa Wuta.
(Duba Nailul Audar na Shaukani, juz’i 2, shafi na:172-173).
ALLAH kabamu ikon aiki da abin da muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki É—ayanmu Ameen.
**************************
Wannan É—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waÉ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta Æ™arin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.