𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Dr. shin ana iya bada kuɗi a zakkatul fitr
maimakon kayan abinci ?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam, Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya wajabta zakkar fidda-Kai da sa'i na dabino ko Sha'ir
kamar yadda ya zo a hadisin Ibnu Umar wanda Muslim ya rawaito a lamba ta:
(2287).
Abin da Malamai suka fahimta
a hadisin da ya gabata shi ne ana fitar da zakkar fidda-Kai ne daga abin da
mutanen garinku suka fi ci kamar Shinkafa Dawa Masara a wajan 'yan Nigeria,
Fukaha'u sun yi saɓani game bada kuɗi a maimakon abincin da ya zo a hadisi :
1. Umar Ɗan Abdulaziz da Abu-hanifa da
Ibnu-taimiyya da Albani da wasu magabata sun tafi a kan halaccin bada kuɗi a maimakon zakkar fidda-Kai saboda abin da yasa aka
shar'anta zakkar fidda-Kai shi ne: wadatar da talakawa daga barin roƙo a ranar idi hakan kuma yana tabbata ta hanyar bada kuɗi ko Ƙimar abincin.
2. Ya wajaba a fitar da abincin da mafi rinjaye suke ci,
saboda tun da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faɗi sunayen abinci,
hakan sai ya nuna su yake so a fitar ba Kimarsu ba, kamar yadda yake a hadisin
Ibnu Umar wanda ya gabata.
Zance na biyu ya fi inganci saboda bin sunnar Manzon
Allah ﷺ shi ne daidai,
tare da cewa in an samu lalura ta Karancin abinci ko kuma talakawa suka nuna
sun fi bukatar kuɗi ya halatta a fitar da kuɗin ko Kimar
abincin a maimakonsa, saboda akwai hadisai da suke nuna halaccin amsar Kima a
babin zakkar dabbobi in SA'I bai samu dabbar da ya kamata ya amsa ba.
Don neman Karin bayani duba: Al-mabsud 2/156 da kuma
Al'istizkaar 9/346 da kuma Al'iktiyarat Alfiƙhiyya
lil'Albani na Abu-shady shafi na 209-210.
Allah ne mafi sani
✍🏼Dr Jamilu Zarewa
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta
Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.