Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Yahalatta Haɗa Kalar Abunci Guda Biyu A Bayar Da Zakkar Fidda-Kai?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Yahalatta Haɗa Kalar Abunci Guda Biyu A Bayar Da Zakkar Fidda-Kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai sun yi saɓani a kan halaccin hada nau'in abunci guda biyu ko sama dahaka a bayar da zakkar fidda-kai dashi, abisa zantuka guda biyu.

1. Magana tafarko: Bai halatta ba kuma ba ta yi ba, shafi'iyyah da ibnu hazam azzahiry, sun dogarane dazahirin nassoshin da sukazo cewa ana bayar da zakkar fidda-Kai sa,i ɗaya ne a cikin nau'ikan abunci sanannu, saboda haka idan mutum yafitar da rabin sa'i daka nau'in abunci darabin sa'i daka wani Nau'in babu wani nassi ɗaya kawo misalin hakan.

Annawawi a cikin Almajmu'u (6/98-99) ya ce: " Shafi'i ya ce: bai halatta bayar da sa'i ɗaya na nau'in abunci kala biyu ba azakkar fidda-kai, kamar yanda akaffarar rantsuwa bai halatta yaciyar da mutum biyar ba ya tufatar da mutum biyar ba, domin an umarce shi ne ya bayar da sa'i na dabino ko acca, dasauransu, kuma bai fitar da sa'in daka daya daka cikinsu ba, kamar yanda aka umarceshi yaciyar da miskinai guda goma ko tufatar dasu, bai ciyar da mutum goma asiffar da'aka ambata ba kuma bai tufatar da su ba.

Tuhfatul Muhtaaj (3/323).

Ibnu hazam a cikin Almuhallah(4/259) ya ce: " bai halatta yafitar da wani sashi na sa'i alkama wani sashin kuma dabino, haka bai halatta kimantata dawani abunba a'asali, domin wannan bashi ne abunda Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya wajabta ba.

2. Zance na Biyu: Ta inganta kuma ta yi, shi ne maganar Hanafiyyah da hanabila, su suntafi zuwa ma'ana ba zahiri ba, domin sa'i ɗaya na nau'ikan abunci hade da juna zai tabbatar da dauke bukatar talaka, da tsarkake rai, da fitar da sadaka.

Ibnu rajab Alhambali a cikin ƙawa'idul fiƙhiyyah ƙa'ida ta (101, shafi na 229) ya ce: "Wanda aka baiwa zabi tsakanin abubuwa guda biyu, kuma zai iya kawo rabin kowanne shin hakan ya isar masa ko a'a?

Akwai saɓani wanda wasu mas'alolin zasu bijiro karkashi daka cikinsu akwai.

@ - Da mutum zai yi kaffarar rantsuwa tahanyar ciyar da mutum biyar ya tufatar da biyar, hakan ya isar masa abisa zance mafi shahara.

@- Da mutum zai fitar da sa'i daya na jinsin abunci guda biyu azakkar fidda-kai, mazhaba shi ne ta yi, dakuma rashin ingantuwar zakkar.

Al insaaf (3/183) Da Hashiyatul Ibnul Ãbideen (2/365).

Amma mazhabar datafi karfin hujjah afahimtar mu a kan wannan mas'ala ita ce mazhabar shafi'iyyah da kuma ta ibnu hazam Allah yajikansu.

Domin shi ne zahirin abunda sunnar Annabi sallallahu Alaihi wasallam yanuna, Sa'i daya na alkama ko accah ko dabino dasauran dangin kayan abunci.

Kuma haka sabbbai suka kasance suna fitar da ita, duk wanda yafitar da ita sa'i na kalar abunci biyu bai fitar da ita yanda Annabi sallallahu Alaihi wasallam yai umarni ba.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta wannan Links...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments