Ticker

6/recent/ticker-posts

Za A Iya Fitarwa Da Kirista Zakkar Fidda-Kai?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ina yiwa mlm fatan alkhairi, Allah ya kara budi. Wasu ne suke neman fatawan a kan wannan mas'alar "musulmine yake auren Christian, to wai idan zai fidda zakkar fidda-kai itama zai fitar mata?"

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam

Hadisi ya tabbata daga Ibnu Umar cewa: "Annabi (SAW) ya farlanta zakkar fidda-kai a kan kowanne musulmi Ɗa ne ko bawa" kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

Hadisin da ya gabata yana nuna musulmi ake fitarwa zakkar fidda-kai, amma kafiri ba'a fitar masa, kuma ba'a ba shi in an fitar.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments