Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Gane Daren Lailatul Qadari

Ranar da daren zai sauka, Rana ba za ta yi zafi ba, gari zaiyi ni'ima a wanann ranar.

Kuma daren wannan ranar zai kasance babu hayaniya, babu ko da haushin kare ko kukan jaki, zai zama gari ya yi tsit babu motsi sosai.

Sannan wata ni'ima za ta sauka, za'aji ko ina ya yi tsit sai ni'ima mai daɗi, yanayin iskar garin ma za'ajita mai daɗin gaske.

Don haka duk wanda ya lura da irin wannan yanayi saiya dage da addu'a sosai a wannan rana.

ALLAH TA'ALAH ya azurtamu da wannan dare.

ALLAH ka biya mana buƙatunmu baki ɗayanmu.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu tare da iyayenmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments