Ticker

6/recent/ticker-posts

Macen Da Al'adarta Ta Zo Mata A Goman Qarshe Ya Za Ta Yi Ta Rabauta Da Lailatul Qadari?

Duk wacce ALLAH yasa Al'adarta ta zo mata a wannan goman ƙarshe, haƙika an haramta mata shiga masallaci don yin sallah, kuma ko da ita kaɗaice sallah da Azumi ba za ta yisu ba.

 Amma saboda tanason ta ribaci kwana goman da wata ibadah, domin haɗuwa da wannan daren, to sai ta farka a dare, sai ta ɗauki Alƙur'ani ta karanta abin da ya sauwaƙa, suratul fatiha ce ko wata surar, idan taso ta yi ta maimaita sura ɗaya, idan taso kuma ta karanta wasu.

 Bayan ta gama sai ta yi istigfar gwargwadon iko, ta yi salati ga Annabi {s.a.w},

 Sannan ta ɗaga hannun ta sama ta roƙi ALLAH dukkan buƙatarta, in sha ALLAH za ta rabauta da wannan dare, indai ta raya dararen ko da ta hanyar karanta Alkur'ani ne.

ALLAH ka azurtamu da wannan dare mai albarka.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments