Ticker

6/recent/ticker-posts

Waɗanne nau'in mutanen ne da za a ba wa zakkar fidda kai?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu alaikum malam. Waɗanne nau'in mutanen ne da za a ba wa zakkar fidda kai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wannan mas'ala akwai saɓanin malamai a kanta, shafi'iyyah suntafi a kan waɗanda ake bawa zakkar fidda kai su ne jinsin mutane takwas da Allah yalissafa waɗanda za a bawa zakkar kuɗi ko dukiya.

Malikiyya suntafi a kan waɗanda za a bawa zakkar fidda-kai su ne talakawa da miskinai, kuma shi ne ra'ayin da shaikul islam ibnu taimiyyaj da dalibinsa ibnul ƙayyeem suka zaɓa, cikin malaman wannan zamanin kuma shaik bin baaz ya zabi wannan maganar.

ya zo a cikin hashiyatul dasuƙi (1/508) " Ana bayar da zakkar fidda kai ga ɗa musulmi talaka wanda ba dangin Annabi ba, ban da mai aikin zakkar ko wanda akesan ya musulunta ko wanda yake matafiya ko bako, kawai ana bawa talaka ne.

Ibnu taimiyyah ya ce: " wannan zancen shi ne ya fi karfi wajan dalili, majmu'u fatawa (25/71).

Ibnul ƙayyeem a cikin zadul ma'ad (2/23) ya ce: yana daka cikin shiriyar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam keɓance talakawa da ita, bai kasance yana rabata ga jinsi takwas danki danki ba, kuma bai umarni da hakaba, babu wani cikin sahabbai daya aikata hakan, ko waɗanda suka biyo bayansu, daya daka cikin zantukan awajanmu, shi ne ta keɓanta ne kaɗai ga miskinai datalakawa, bai halatta rabata tsakanin jinsi takwas ba.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta wannan Links...

MUTUM ZAI IYA BA WA ƊAN UWANSA ZAKKAR FIDDA-KAI?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam tambayata ita ce mutum zai iya ba wa ɗan'uwansa zakkar fidda-kai wadda suke uwa ɗaya uba ɗaya, sannan kuma don Allah a taimake mu a duba mana in mutum zai ba da Zakka fidda-kai na kuɗi nawa ne kowane mutum ɗaya zai bayar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, dama ita zakkar fidda-kai an shar'anta a ba wa talakawa ne, saboda haka matuqar wanda kuke uwa ɗaya uba ɗaya da shi ɗin nan yana daga cikin faqirai ko miskinai, to ya halasta ki ba shi zakkar fidda-kai, kawai sharaɗin dai ya zamana wanda za a ba zakkar yana daga cikin faqirai ko miskinai, kamar yadda malamai suka tabbatar ta la’akari da ayar Alqur’ani.

Shi ko hukuncin yin zakkar fidd-akai da kuɗi, malaman Musulunci suna da fahimta guda biyu: na farko suna ganin ya halasta mutum ya yi zakkar fidda-kai da kuɗi, saboda su a fahimtarsu daga cikin manufar shar'anta zakkar fidda-kai shi ne don a faranta wa talakawa rai a ranar Eidi, saboda haka suke da fahimtar za a iya ba da kuɗin da zai yi daidai da qimar sa'i ɗaya na abinci, masu wannan fahimtar sun haɗa da: Imam Abu Haneefa, da Hasanul Basriy, da Umar ɗan Abdul'aziz, da Thauriy.

Sai dai Is'haq da Abu Thaur sun ce qimar zakkar fidda-kai ba ya isarwa a yi da kuɗi har sai in akwai lallura. Amma fahimtar mafi yawan malaman Musulunci ita ce: Qimar Zakkar fidda-kai da kuɗi ba ya isarwa kamar yadda Imam Malik, da Imam Ahmad, da Ibn Munzhir suka faɗa. Duba ALMAJMU'U 6/144 na Imamun Nawawiy.

Saboda haka, abin da ya fi cancanta shi ne a fitar da zakkar fidda-kai da nau'in abincin da aka fi ci a garin da mutum yake, sai idan akwai lallura ne sannan a ba da kuɗin da ya yi daidai da qimar sá'i ɗaya na abinci.

Sai dai fa ni ban san ko nawane qimar kuɗin zakkar fidda-kai a kuɗin qasarmu ba, saboda ni da abinci nake yi ba da qima na kuɗi ba, abin dai da ya wajaba a kiyaye shi ne: Asali dai kowane mutum ɗaya da zai yi fidda-kai zai ba da abinci ne SÁ'I ɗaya, sá'i ɗaya kuma shi ne Muddun Nabiyyi huɗu.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments