Ticker

6/recent/ticker-posts

Malam to wanda bai samu talakawan da zai ba wa zakkar fidda kai ba yaya zai yi?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu alaikum, malam to wanda bai samu talakawan da zai ba wa zakkar fidda kai ba yaya zai yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Zakkar fidda kai Allah maɗaukakin sarki ya wajabtata ta harshen manzansa sallallahu Alaihi wasallam, a kan maza da mata, yara da manya, bawa da ɗa, kuma Annabi sallallahu Alaihi wasall ya yi umarni a bayar da ita kafin afita sallar idi, wanda bai samu talakawan dazai bawa akewayansa ba, wajibi ne yanemesu agaruruwan da suke kusa dashi, ya yi gaggawar bayar da ita kafin fita sallar idi, bai halatta yajinkirta zuwa bayan sallar idi, saboda wannan saɓanin Abunda manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya yi umarni dashi ne.

Hakika Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya yi umarni afitar da ita kafin afita sallar idi ya ce: (Duk wanda ya bayar da ita kafin fita sallar idi hakika zakkah ce karbabbiya wanda ya bayar da ita bayan sallar idi sadakace cikin sadakoki).

Abunda yake wajibi shi ne mutum yakula sosai yafitar da ita, ko da kafin idi ne da kwana biyu ko ɗaya ko uku.

Abdullahi dan Umar Allah yakara yarda da su ya kasance yana fitar da ita kafin ranar idi dakwana ɗaya ko biyu, wani lokacin kafin ranar idi da kwana uku hakama sahabbai Allah yakara yarda dasu.

Manufa dai shi ne mutum yafitar da ita daka ranar ashirin da takwas har zuwa ranar idi, Amma kada yakuskura yajinkirtata harzuwa bayan sallar idi, idan a inda kake babu talakawa to ka nemesu a wani wajan ko da zakayi tafiyane wajan neman talakawan dazaka bawa.

Abdul'aziz bin baaz fatawa Nurun Alar darbi (2/1209).

WALLAHU A'ALAM

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments